in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara wa kasar Angola girma a kasashen duniya sabo da nasarar da ta samu wajen shirya gasar cin kofin Afirka
2010-02-02 16:29:14 cri
A ran 31 ga watan Janairu an rufe gasar cin kofin Afirka ta wasan kwallon kafa wadda aka shafe makonni 3 ana yin ta a birnin Luanda, kungiyar kasar Masar ta lashe ta kasar Ghana kuma ta zama zakara. Kasar Angola wadda ke karbar bakuncin gasar ta nuna wa duniya cewa ita ce kasar Afirka dake samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma ta samu yabo sosai daga wajen kasashe masu halartar gasar na Afirka da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasashen duniya wato FIFA sabo da kwarewar da ta nuna wajen shirya gasar.

Wannan gasar cin kofin Afirka ta zama gasar wasannin motsa jiki mafi girma da kasar Angola ta shirya, an shafe shekaru fiye da 50 ana ta yin ba ta kashi a kasar wanda bai kare ba sai shekarar 2002, yake-yaken da aka yi sun jawo babbar hasara ga zaman al'umma da tattalin arzikin kasar Angola, kuma an haifar da rikice-rikice da gurbataccen hali wajen harkokin samar da ruwan sha, da hanyoyin tafiye-tafiye da zirga-zirga da manyan gine-gine domin wasannin motsa jiki da harkokin zaman al'umma, kashi 2 bisa 3 na jama'ar kasar suna zama cikin talauci kwarai, sabo da haka ba yawancin kasashen Afirka kawai ba har ma da akasarin mutanen kasar Angola wadanda suka yi shakku cewa, ko kasar Angola za ta iya daukar nauyin shirya irin wannan babbar gasar wasannin motsa jiki? Yau kimanin shekaru 3, shugaba Jose Eduardo Dos Santos na Angola ya nuna hazaka sosai wajen siyasa, ya lashi tabobin neman hakkin shirya gasar cin kofin Afirka, kuma za ta kara karfin gwiwar al'ummar kasar, ta yadda wannan gasar za ta zama wata damar nuna nasarar da ta samu wajen bunkasa tattalin arziki bayan kammala yakin basasa da aka yi a kasar.

Gwamnatin kasar Angola ta dogara bisa taimakon da kamfanin yin gine-gine na kasar Sin ya bayar, cikin shekaru 2 kawai ta gina filaye da dakunan wasannin motsa jiki irin na zamnani da sauran manyan gine-gine ciki har da hanyoyi da zirga-zirga, da harkokin samar da ruwan sha da wutar lantarki, da hotel-hotel da ayyukan sadarwa da yawon shakatawa, har ta kammala dukkan ayyukan share fage domin wannan gasar cin kofin Afirka, wannan abu ne mai ban ta'ajjabi. Ban da wannan kuma gwamnatin Angola ta haye walalhalun da aka kawo mata sabo da matsalar hada-hadar kudi da faduwar farashin man fetur na duniya, ta ba da tabbaci ga ayyukan gina wadannan manyan filaye da dakunan wasannin motsa jiki guda 4 da sauran manyan gine-gine cikin gajeren lokaci. Mutanen Angola suna mai da wadannan manyan filaye da dakunan wasannin motsa jiki guda 4 a matsayin ayyukan siffofin kasar Angola.

Bisa lokacin da aka tsayar, an bude gasar cin kofin Afirka a ran 10 ga watan da ya wuce a filin wasan motsa jiki na "Ran 11 ga Nuwamba", shugabanni da dama na kasashen Afirka sun halarci bikin bude gasar domin more wannan babban bikin wasannin motsa jiki na nahiyar Afirka, sa'an nan kuma sun tattauna tsakanin bangarori 2 ko kuma bangarori da dama kan batutuwan da suka jawo hankalinsu dukka, sabo da haka ana iya cewa gasar cin kofin Afirka kuma ta zama wani babban taron harkokin waje da aka yi tsakanin shugabannin kasashen Afirka, haka kuma ta bai wa kasar Angola wata damar sake hawa kan dakalin siyasa na Afirka bayan yakin basasa da aka yi a kasar, da daga matsayinta a nahiyar, da kuma kara samun ikon fadin albarkacin bakinta a kasashen duniya. (Umaru)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China