in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan motocin da za a kera da kuma sayarwa zai samu karuwa a bana
2010-01-31 20:40:46 cri
A shekarar 2009, yawan motocin da aka kera da kuma sayar a kasar Sin ya kai fiye da miliyan 13 da dubu dari 5. Hakan ya sa a karo na farko kasar Sin ta yi wa kasar Amurka zarra, inda ta zama kasa mafi girma wajen kera da kuma sayar da motoci. Kuma an yi hasashen cewa, yawan motocin da za a kera da kuma sayar a shekarar 2010 a kasar Sin zai kai fiye da miliyan 15. Mr. Jia Xinguang, wanda yake nazarin sana'ar motoci ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai fiye da kashi 8 cikin kashi dari a shekarar 2009. Hakan ya sa kasuwar motoci ta samu ci gaba. A waje daya, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta dauki matakai 3 domin sa kaimi ga kokarin sayar da motoci, wato rage yawan harajin da ake bugawa kan motocin da aka saya, kuma ta sa kaimi ga kokarin sayar da motoci a kauyuka, sannan ta samar da nau'o'in tallafin kudi ga wadanda suke son sayar da tsoffin motocinsu domin sayen sabbin motoci."

Ko da yake wadannan matakai sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kasuwar motoci ta kasar Sin cikin sauri a shekarar 2009, amma wasu kafofiin yada labaru da manazarta sun nuna cewa, kasuwar motoci ta samu ci gaba cikin sauri fiye da kima a shekarar 2009. Sakamakon haka, wasu mutane sun sayi motocinsu kafin lokacin da suka tabbatar a cikin shirin da suka tsara a da, hakan mai yiyuwa ne zai kawo mummunan tasiri ga kokarin ci gaban kasuwar motoci a bana.

Game da irin wannan ra'ayi, wani kamfanin binciken ra'ayoyin jama'a na kasar Sin ya nuna cewa, bukatun da ake da su a kasuwa za su goyi bayan kasuwar motoci ta kasar Sin da ta dinga samun ci gaba cikin sauri. Mr. Yuan Yue, shugaban wannan kamfani ya ce, yanzu matsakaiciyar jimillar kudin harkokin kawo arziki na kasar Sin, wato GDP ta kowane mutum ta riga ta kai dalar Amurka dubu 3, wato kasar Sin ta soma shiga lokacin kara saurin yin amfani da motoci. Kuma sabo da halin da ake ciki a kasar Sin ya sha bamban sosai da na kasar Amurka, lokacin shigar motoci ga iyalan kasar Sin zai yi tsawo sosai. Mr. Yuan ya ce, "Tsawon lokacin shigar motoci ga iyalan kasar Sin zai kai shekaru 50 da 60 masu zuwa, wannan yana da bambanci sosai da na kasashen yammacin duniya wadanda suka ci gaba a harkokin masana'antu da tattalin arziki sosai."

A shekarar 2009, wata kalma ta daban da ta fi jawo hankalin jama'a kamar kalma "rikicin hada-hadar kudi" ita ce "sauyin yanayin duniya". Jama'a sun fi mai da hankalinsu kan yadda za a iya rage yin amfani da abubuwa masu dumama yanayi. Hakan ya sa masana'antun kera motoci na duniya suna kokarin nazarin sabbin motocin da za su iya yin amfani da makamashi maras gurbata muhalli. Masana'antun kera motoci na kasar Sin suna kuma yin haka. Dr. Zhao Fuquan, mataimakin shugaban kamfanin kera motoci kirar "Geely" ya bayyana cewa, a bana, kamfanin Geely zai nuna wa jama'a motocin da ke amfani da fasahar zuriya ta uku. Na ji Dr. Zhao ya ce, "Mun riga mun kammala nazarin fasahohin zuriya ta farko da ta biyu wajen kera motoci masu aiki da wutar lantarki kawai. Yanzu muna nazarin fasahar da ta shafi zuriya ta uku. Bisa wannan sabuwar fasaha, za a samar da motoci masu aiki da wutar lantarki da karfin hasken rana tare. A gun bikin nune-nunen motoci da za a yi a Beijing a shekarar 2010, za mu nuna wa jama'a motocin da za mu kera da fasahar zuriya ta uku."

Bugu da kari, yanzu kamfanonin kera motoci suna kuma mai da hankali wajen yada tambarin kayayyakinsu. Mr. Wang Wenbing, mataimakin babban direktan kamfanin kera motoci masu daukar fasinja kirar "Yutong", wato kamfani mafi girma wajen samar da motoci masu daukar fasinja a kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu kamfaninsa yana kokarin yada tambarin "Yutong" a duniya, ba a kasar Sin kawai ba. Mr. Wang ya ce, "Yanzu, kamfaninmu yana cikin lokacin samun bunkasuwa ba tare da wata tangarda ba a kasuwar cikin gida. Amma a kasuwannin ketare, muna kan matakin farko wajen yada tambarin motocinmu. Sabo da haka, dole ne mu yi kokarin yada tambarinmu a duniya."

Game da makomar kasuwar motocin kasar Sin a shekarar 2010, madam Zhu Yiping, mataimakiyar babban sakataren kungiyar masana'antun kera motoci ta kasar Sin ta bayyana cewa, "Ya kasance tamkar muhimmin tushen tattalin arziki, gwamnatin kasar Sin ba za ta canja goyon bayan da take nuna wa masana'antun kera motoci a shekarar 2010 ba. Mazauna masu dimbin yawa suna son sayen motoci kamar yadda suke yi a da. Matsakaicin saurin karuwar motocin da aka sayar a cikin jerin shekaru 15 da suka gabata ya kai kusan 17 cikin dari. Bisa wannan halin da ake ciki, mun yi hasashen cewa, yawan motocin da za mu kera kuma za mu sayar zai kai miliyan 15 a shekarar 2010." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China