in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lin Wending, dan kasuwa na Taiwan wanda ke noman bishiyoyin kofi a Hainan
2010-01-25 16:56:10 cri
A gundumar Chengmai da ke arewacin tsibirin Hainan na kasar Sin, akwai wani filin da fadinsa ya kai fiye da kadada 130, inda wani dan kasuwa na yankin Taiwan, wato Mr. Lin Wending ne ya zuba jari ya dasa bishiyoyin kofi. A cikin shirinmu na yau, za mu karanta muku wani bayani game da yadda Mr. Lin yake kula da wadannan gonakin bishiyoyin kofi.

Lokacin da yake hira kan kofi, ana tsammanin cewa, shi ne ya kware sosai wajen noman bishiyoyin kofi. Amma a hakika dai, yau shekaru 7 da suka gabata, shi ne mataimakin shugaban gundumar Tainan ta lardin Taiwan. Sabo da rashin sabawa da yanayin siyasar yankin Taiwan, hakan ya sa ya yi murabus daga mukaminsa, kuma ya soma yin kasuwanci. Mr. Lin ya ce, "Ni mutum ne mai gaban gadi, na fi son fadin kome da kome kai tsaye. Sabo da haka, na tsai da kudurin janye jiki daga siyasa."

Bayan da ya tsai da niyyar yin kasuwanci, ya gano cewa, muhallin zuba jari bai kasance a Taiwan kamar yadda yake fata ba, ana yin takara sosai a Taiwan. Sabili da haka, Mr. Lin yana son zuba jari a babban yankin kasar Sin. Kuma ya je biranen Beijing da Shanghai da sauran manyan biranen babban yanki, kuma ya ga yawan kofin da ake sha a babban yankin yana ta karuwa cikin sauri a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kuma yanayin lardin Hainan yana kusan daidai da na Taiwan, yana dacewa da noman bishiyoyin kofi. Sabo da haka, da farko dai, Mr. Lin Wending ya yi hayar gonakin da yawansu ya kai kadada 30 a lardin Hainan domin noman bishiyoyin kofi masu inganci. Amma a farkon lokacin nomansu, Mr. Lin ya sha wahala iri iri.

"Ko shakka babu, na sha wahala sosai. Na yi shekaru 20 ko fiye ina harkokin siyasa a Taiwan, amma ban taba daukar gatari ko sau daya ba. A da, ni dan siyasa ne, amma yanzu ni wani manomi ne. Na soma noman bishiyoyin kofi, ba kawai ina ketarewa a tsakanin sana'o'i daban daban ba, har ma dole ne na daidaita halin da nake ciki."

Lin Wending ya yi haka ne kamar yadda ya fadi. Shi da kansa ne ya kan noma bishiyoyin kofi fiye da dubu 30 da 'yan kwadago da ya yi haya. Kowace rana yana sare gonaki da cire ciyayi. Ko da yake ya sha wahalhalu da yawa a cikin shekaru da dama da suka gabata, amma Lin Wending bai yi kasala ba. Tun daga shekara ta 2002 zuwa ta 2005, tsawon shekaru 3 sun wuce, kuma bishiyoyin kofi sun girma sun soma samar da 'ya'yan kofi. Lokacin da Lin Wending yake jiran lokacin girbinsu, ba zato ba tsammani, guguwar iska mai suna "Dawei" ta shafi tsibirin Hainan baki daya. Yawancin bishiyoyin kofi sun mutu sakamakon wannan guguwar iska. Lin Wending ya yi hasara kwarai. Babu sauran hanya zai iya zaba, sai ya sake noman sabbin bishiyoyin kofi, kuma ya sake mai da hankali a kansu. Amma bayan sauran shekaru 3, wato daga shekara ta 2005 zuwa shekara ta 2008 sun wuce, an samu wata dusar kankara a yawancin yankunan kudancin kasar Sin. Lin Wending ya sake samun hasara sakamakon wannan bala'i daga indallahi. Lin Wending ya ce, "A jajibirin bikin bazara bisa kalandar wata ta kasar Sin na shekarar 2008, lokaci ne da bishiyoyin kofi suka soma nuna furanni. Amma an samu dusar kankara a yankunan kudancin kasarmu. Ko da yake ba a yi dusar kankara a tsibirin Hainan ba, amma an yi sanyi kwarai. Kowace rana zafin yanayi bai wuce digiri 10 ba a cikin wata daya ko fiye. Sakamakon haka, bishiyoyin kofi ba su nuna furanni ba. Wasu furanni sun bullo, amma sun mutu sakamakon sanyi. Ko da yake lokacin da nake Taiwan, na sani, ana yin aikin gona ne bisa yanayin duniya, amma lokacin da ake gamu da irin wadannan bala'u daga indallahi ba zato ba tsammani, yaya za a yi? wannan ikon Allah ne!"

Ko da yake ya sake gamuwa da bala'i daga indallahi, amma Lin Wending bai bar burin da yake son cimmawa ba. Ya yi kokarin fama da wadannan bala'u daga indallahi, kuma ya samu nasara. A shekarar 2009, a karo na farko ne Lin Wending ya yi girbin 'ya'yan kofi.

Lin Wending ya kara da cewa, lokacin da yake kokarin noman bishiyoyin kofi, hukumomin gwamnatin lardin Hainan da na gundumar Chengmai sun nuna masa goyon baya kwarai. Har ma gwamnatin Chengmai ta ware wasu kudi domin shimfida wata hanyar siminti da ke hade gandun gonakinsa da tagwayen hanyoyin mota. Lin Wending ya bayyana cewa, "A da, wannan hanyar da ke wajenmu hanya ce mai tabo. A shekara ta 2008, gwamnatin Chengmai ta kebe kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu dari 6 domin shimfida wannan hanyar siminti."

Yanzu, ba ma kawai Lin Wending yana noman bishiyoyin kofi ba, har ma yana da wata masana'antar sarrafa 'ya'yan kofi da kuma kantunan sayar da kofi a birnin Shanghai da lardin Zhejiang.

Yanzu Lin Wending ya dade yana zaune a lardin Hainan, wani dansa ma ya zo lardin, kuma ya auri wata mace a babban yankin kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China