in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2010-01-15 16:44:01 cri

A cikin shirinmu na yau, bari mu duba wani labari da muka samu daga shafin internet na VANGUARD na kasar Nijeriya, wanda aka buga a ran 13 ga wata, inda aka bayyana cewa, jihar Lagos ta kasar Nijeriya ta shirya sosai wajen bunkasa wasannin motsa jiki.

A ran 13 ga wata, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin wasannin motsa jiki na jihar Lagos ta kasar Nijeriya mista Agboola Dabiri ya bayyana cewa, kwamitinsa ya jaddada aikinsa, kuma yana iya tinkarar kalubale na bunkasuwar wasannin motsa jiki a jihar. Mista Dabiri ya nuna aniyar kwamitin wasanni na cimma tudun dafawa a fannonin wasannin motsa jiki, ya ce, a shirye yake a halin yanzu.

A 'yan kwanakin baya, gwamna Tunde Fashola na jihar Lagos ya ba da umurni da a raya wasannin motsa jiki. Mista Dabiri ya amsa wannan umurni ne da gwamna ya yi masa. Mista Dabiri ya jaddada nauyi a kan kwamitin da ke kula da harkokin wasannin motsa jiki wajen raya harkokinsu, ya ce, babu lokaci da ya fi yanzu kyau da a dauki matakai da kansu domin samun bunkasuwar wasannin motsa jiki.

Shugaban kwamitin da ke kula da harkokin wasannin motsa jiki na jihar Lagos ta kasar Nijeriya mista Agboola Dabiri ya bayyana cewa, ya yaba wa gwamnan jihar Lagos mista Tunde Fashola da ya dauki hakikanan matakai. Sakamakon haka, kamata ya yi kwamitin da ke kula da harkokin wasannin motsa jiki ya gudanar da ayyukansa ba tare da kasala. Ya ce, kwamitin ya dauki nauyi a kansa.

Dabiri ya kara da cewa, ya kasance da ayyuka da yawa a gaban ma'aikatan kwamitin wasanni, amma wata hanyar da ta fi kyau gare su ita ce, su yi kokari tare bisa makasudi daya, wato su kara daga matsayin jihar Lagos a kasar Nijeriya. A ganinsa, jihar Lagos tana da nagarta a duk kasar Nijeriya, sabo da haka bai kamakata kwamitin ya bata rai na jama'a da gwamnati ta jihar Lagos ba. Mista Agboola Dabiri ya fadi cewa, kwamitin wasanni ya san burin jama'a, ya riga ya tsara shiri na gudanar da jerin gasanni masu yawa domin neman 'yan wasa da suke da kwarewa. Da farko dai kwamitin wasanni zai gudanar da shirin wasanni na tsawon wata guda wato Lagos Sports Month a wata mai zuwa.

Wannan shirin wasanni na tsawon wata guda zai bayar da wata kyakkyawar dama ga kwamitin wasanni da jihar Lagos da su nemi sababbin 'yan wasa da suke da kwarewa, haka kuma za su iya shiga cikin wasanni a yamma maso kudancin Nijeriya, wadanda za a shirya a birnin Ilaro na jihar Ogun ta kasar Nijeriya. Mista Agboola Dabiri ya yi kira ga ma'aikatan kwamitin wasanni da su fahimci aniyyar gwamna da kuma burin jama'a, ta yadda za su iya gudanar da ayyuka yadda ya kamata domin jin dadin jama'a da gwamnati.

Mista Agboola Dabiri ya ce, har kullum an yi tsammani cewa, jihar Lagos ta fi kyau a duk kasar Nijeriya a fannonin wasannin motsa jiki. Sabo da haka, kamata ya yi dukkan jama'ar Lagos su yi kokari tare, domin maido da matsayin da jihar Lagos take da shi a wasannin motsa jiki na duk kasar Nijeriya karo mai zuwa, wadanda za a shirya a birnin Portharcourt da ke jihar River ta kasar Nijeriya. A ganin Mista Agboola Dabiri, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin wasannin motsa jiki na jihar Lagos ta kasar Nijeriya, ko shakka babu za a cim ma burin daga matsayin wasanni na Lagos bisa ga umurnin da gwamna Tunde Fashola ya ba shi. Ya ci gaba da cewa, ko da yake ayyukan da suke shafar wasanni suna da wuya wajen gudanarwa, amma a karshe dai kwamitin zai ci nasara, wato ba zai bata ran jama'ar Lagos da gwamnatin jihar ba.

Bisa labarun da muka samu, an ce, kungiyar 'yan wasa ta kasar Nijeriya ta riga ta samu iznin shiga cikin wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya, wadanda za a shirya a wannan shekarar da muke ciki a kasar Afirka ta kudu, amma a ran 13 ga wata, kungiyar 'yan wasa ta kwallon kafa ta maza ta kasar Masar ta lashe Neijriya da ci 3 da 1 a wasannin cin kofin kasashen Afirka, wadanda aka shirya a kasar Angola.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China