in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar kyakkyawar dangantaka a tsakanin Sin da Afirka a idon Yang Jiechi
2010-01-12 17:13:42 cri

Matsalar kudi ta duniya da kuma sauyawar yanayi kalubale ne da ke gaban duk duniya. Kasashe dadan daban suna inganta hadin kansu domin tinkarar matsalolin. Game da wannan, Yang Jiechi ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da inganta hadin kai tare da Afirka. Ya ce, "matsalar kudi ta duniya ta yi illa sosai ga Sin da Afirka, haka kuma sauyawar yanayi ta kawo illa ga Afirka. Matsalar kudi ta duniya ta haddasa raguwar yawan kayayyakin da kasashen Afirka suka samar da aka sayar da su a kasuwar duniya, wasu kasashe kuma sun rage yawan kudin taimako da za su bai wa Afirka. Haka kuma sakamakon dumamar yanayin duniya, ayyukan gona na Afirka sun samu mummunan tasiri sosai. A cikin wannan halin da ake ciki, ya kamata kasashe masu tasowa ciki har da Sin da kasashen Afirka su inganta hadin kansu domin tinkarar matsalar kudi tare."(Kande Gao)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China