in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar kyakkyawar dangantaka a tsakanin Sin da Afirka a idon Yang Jiechi
2010-01-12 17:13:42 cri

Game da batun inganta hadin kan Sin da Afirka a cikin sabon tsarin tattalin arzikin duniya domin samun nasara tare, Yang Jiechi ya furta cewa, Sin za ta tallafa wa kasashen Afirka wajen raya muhimman ayyukan yau da kullum, da kuma raya albarkatunsu domin su zama abubuwa masu rinjaye wajen raya kasashen Afirka. Kuma Yang ya kara da cewa, "A ganina, Sin da Afirka na iya taimaka wa juna a fannoni da yawa. Alal misali, Sin na iya tallafa wa Afirka a fannonin inganta raya muhimman ayyukan yau da kullum, da kyautata sharudan kiwon lafiya, kana da sa kaimi ga raya ayyukan gona. Bisa matakai 8 da Sin ke dauka don ba da Afirka tallafi, Sin za ta samar da cibiyoyi 20 na fasahohin ayyukan gona ga Afirka, da kuma aika da kungiyoyin ba da taimako 50 zuwa Afirka a cikin shekaru uku masu zuwa domin tallafa wa Afirka wajen raya ayyukan gona. Haka kuma Sin za ta tura dimbin kwararru a fannin ayyukan gona zuwa Afirka don horar da masu rike da fasahohin ayyukan gona na Afirka 2000."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China