in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar kyakkyawar dangantaka a tsakanin Sin da Afirka a idon Yang Jiechi
2010-01-12 17:13:42 cri

Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya yi ziyarar aiki a kasar Kenya daga ran 6 zuwa ran 8 ga wata, inda ya yi shawarwari tare da shugaba Mwai Kibaki da firayim minista Raila Odinga kana da takwaransa Moses Wetangula na kasar Kenya. Bangarorin Sin da Kenya sun tattauna kan raya dangantakar da ke tsakaninsu da kuma sa kaimi ga hadin kansu a fannoni daban daban. To yanzu ga cikakken bayani.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, ma'aikatar harkokin waje ta Sin tana da wata al'ada, wato yin ziyarar aiki a kasashen Afirka a farkon sabuwar shekara domin sheda muhimmancin da Sin ke sanya wa Afirka. Ya zuwa yanzu an dade ana bin wannan al'ada har tsawon shekaru 20. Yanzu dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka tana ta samun ingantuwa, kuma ya yi wannan ziyara ne domin karfafa ta. Yang Jiechi ya ce, "Na yi imanin cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka tana ta samun bunkasuwa. A fannin siyasa, muna kiyaye kai wa juna ziyara domin kara amincewar juna. A fannin tattalin arziki kuma, bangarorin biyu suna kara zuba jari ga juna a fannoni daban daban. Haka kuma Sin da Afirka suna ta yin cudanya a tsakaninsu a fannin al'adu. Sin da Afirka suna daukar matsayi gu daya a kan wasu muhimman al'amuran duniya da na shiyya-shiyya kamar tinkarar sauyawar yanayi da matsalar kudi ta duniya. Don haka ana iya gano cewa, makomar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka na da kyau sosai. Kuma na yi wannan ziyara ne domin inganta irin wannan dangantaka."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China