in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon ci gaban da aka samu wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a shekarar 2009
2010-01-05 15:47:56 cri
Kwanan baya yayin da Mr. DaiYan, tsohon shugaban hukumar watsa labaru na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, kuma tsohon mashawarcin jakadan kasar Sin a kasar Ghana ya amsa tambayoyin da manema labaru na tashar yanar gizo wato internet ta jama'a suka yi masa ya waiwayi sabon ci gaban da aka samu wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a shekarar 2009, kuma ya yi watsi da zacen banza da wasu kasashen yamma suka yi na wai yin barazana daga kasar Sin domin bata sunan kasar.

Dai Yan ya ce, a shekarar 2009 dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ta shiga wani sabon mataki, manyan shugabannin bangarorin 2 sun yi ta yin ziyarce-ziyarce ya junansu.

A farkon shekarar da ta wuce shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kai ziyara a kasar Sa'udiya da sauran kasashe 4 na nahiyar Afirka, muhimmin dalilin da ya sa shugaba Hu ya yi wannan ziyarar shi ne domin sa kaimi ga tabbatar da wasu matakan da aka dauka a wurin taron koli na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ta yadda dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka za ta kara samun bunkasuwa.

A watan Nuwamba na shekarar da ta wuce, firayim ministan ksar Sin Wen Jiabao ya je kasar Masar don halartar bikin bude taron ministoci a karo na 4 na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kuma ya yi jawabi a wurin bikin. Ban da wannan kuma Wen Jiabao ya yi cudanya sosai da shugabannin kasashen Larabawa da na kasashen Afirka inda ya gabatar da sabbin matakai da dama domin kara dankon zumunci da hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2. Wannan ziyarar ta zama wata saduwa mai ma'ana sosai, kuma wata ziyara ce da ta samu sakamako mai armashi a fannin sada zumunta da hadin gwiwa.

Mr. Dai Yan ya ce, kwanan baya an yi sambatun banza a kasashen duniya cewar wai kasar Sin ta yi barazana ga kasashen Afirka, da ra'ayin wai yin sabon mulkin mallaka da yin kwace-kwacen albarkatun kasa, ban da wannan kuma akwai ra'ayin shirme na wai cin zarafin jama'ar dake wurin da haramta musu damar samun aikin yi, da kuma kazamtar da muhalli. Ainihin ummalaba'isin da ya haifar da wadannan sambatun banza ya shafi fannoni daban-daban. Da farko mun tabbatar da cewa a farkon shekarar 2006, mun bayar da takardar bayani game da manufar da muka dauka kan nahiyar Afirka, cikin bayanin mun gabatar da cewa, bangarorinmu 2 za su amince wa juna a fannin siyasa da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna a fannin tattalin arziki, da yin mu'amalar juna wajen al'adu domin kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa muhimman tsare-tsare. Mun riga mun tabbatar da wannan manufar a wurin taron koli na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Daga nan ana iya gane cewa, ko kusa ba gaskiya ba ne yin barazana daga kasar Sin.

Yayin da Dai Yan ya tabo batun hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannin albarkatun kasa, ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ake yi wajen bunkasa albarkatun kasa a tsakanin bangarorin 2 ya zama wani jigo ne daga cikin hadin gwiwar da kasashen Afirka ke yi tare da kasashen waje, kuma wani kashi ne daga cikin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasa da kasa a fannin albarkatun kasa. Bisa ka'idojin da kasashen duniya suka saba da su da kuma dokokin kasuwanci, ba wanda zai iya yin gardama kansa game da hadin gaiwar da ake yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wannan hadin gwiwa zai taimaka ga bangarorin 2, kuma ya samu maraba a ko'ina daga jama'ar kasashen Afirka, sabo da haka, irin sambatun banza da aka yi na wai kasar Sin ta wawashe albarkatun kasa na Afirka ba shi da tushe balle makama. (Umaru)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China