in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Somalia na ci gaba da fama da yake-yake
2009-12-31 14:16:34 cri
A shekarar da za ta wuce ba da dadewa ba, a kasar Somalia da ke kuryar, kuma gabas a nahiyar Afirka, gaggaye dakaru suna ta tayar da rikici, kuma an yi ta samun hare-haren kunar bakin wake da fashe-fashen bama-bamai a gefunan hanya. Sa'an nan kuma, 'yan fashin teku ba su daina yin garkuwa da jiragen ruwa ba, ga tsananta matsalar jin kai. Dukkan wadannan almamu sun shaida cewa, bayan shekaru 18, ba a iya gano alamar daina yake-yake a Somalia ba tukuna, a maimakon haka, wannan kasa na ci gaba da fama da tsanancewar rikici.

Tun farkon wannan shekara, Somalia ta kara tsunduma mugun rikici na zubar da jini a tsakanin sojojin gwamnatin da 'yan tawaye. Gwamnatin wucin gadi ta kasar ta sha sanar da kafa zaman dokar ta baci a duk fadin kasar sau da dama, ta kuma yi kira ga kasashen da ke makwabtaka da ita da su tura mata sojoji domin taimakawa sojojinta.

Baya ga musayar wuta da aka yi a tituna, mutanen Somalia sun yi ta shan wahalar hare-haren kunar bakin wake da fashe-fashen bama-bamai a gefunan hanya, wadanda ba safai su kan fama da su a da ba.

Dagulewar halin da Somalia ke kasancewa ya sanya fashin teku ya zama ruwan dare, hakan ya yi tsananin illa ga tsaron hanyoyin jiragen ruwa da ke hada tekun Bahar Maliya da tekun Indiya. Kasashen duniya suna nuna kulawa matuka kan wadannan 'yan fashin teku.

Somalia ta fara fama da yakin basasa tun daga shekarar 1991, inda aka hambarar da gwamnatin Mohamed Siad Barre, wanda ya yi shekaru 22 yana mulkin Somalia. Daga baya, an kaddamar da yakin basasa domin neman mulkin kasar. A sakamakon taimakon kasashen duniya, an kafa gwamnatin wucin gadi a Somalia a shekarar 2004.

Amma ya zuwa yanzu, gwamnatin wucin gadi ta Somalia ba ta yi mulkin a duk kasar, tana da iko a kan wasu muhimman wurare da ke birnin Mogadishu, hedkwatar wannan kasa, kamar fadar shugaba da filin jirgin sama da tashar jirgin ruwa kawai. Sauran wuraren da ke Mogsdishu da kuma yawancin wuraren da ke tsakiya da kudancin kasar suna hannun 'yan tawaye. Manazarta sun nuna cewa, dalilin da ya sa da wuya a magance yakin basasa a Somalia ba shi ne tsananin matsalolin zaman al'ummar kasa ke rikitar da mutane.

Da farko dai, Somalia ta dade tana fama da wasu matsalolin da suka zama ruwan dare a wannan kasa. Akwai kabilu da yawa a Somalia, kuma dangantaka a tsakaninsu na da sarkakkiya. Yake-yake na dogon lokaci sun sanya wadannan kabilu ba sa ga maciji da juna, har ma suna nuna wa juna kiyayya. Somalia wata kasa ce ta Musulmi, amma rukunonin addinin Musulunci ba su cimma daidaito kan dangantaka a tsakanin Musulunci da ikon mulkin kasar ba.

Na biyu kuma, rikicin da Somalia ke fuskanta a gida da waje sun ingiza bullowar kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin addini. Gwamnatin wucin gadi ta Somalia ba ta iya kwantar da kurar yake-yake a gida ba, ta haka ba yadda za ta yi, sai dai ta yi dogaro da goyon baya daga kasashen waje. Amma jama'ar Somalia suna matukar adawa da tsoma bakin da kasashen waje suka yi wa kasarsu. Har kullum sun mayar da gwamnatin wucin gadi ta kasar a matsayin gwamnatin je-ka-na-yi-ka. Tsoma bakin da kasashen waje suka yi ya raunana goyon bayan da jama'ar Somalia suke nuna wa gwamnatin wucin gadi, ya kuma ingiza masu tsatsauran ra'ayin addini su inganta tasirinsu a wurin.

Na uku kuma, yake-yake da rikici suna taimakawa juna. Yake-yake na tsawon shekaru da dama sun tsananta matsalar jin kai da jama'ar Somalia suke fuskanta a kwana a tashi, sun kuma samar wa 'yan tawaye zarafin inganta tasirinsu a wurin, musamman ma a tsakanin matasa.

Bisa halin da ake ciki a Somalia, mun iya gano cewa, gwamnatin wucin gadi ta kasar da kuma dakarun da ke adawa da ita ba su amince da juna ba, ba su son sake yin kokarin daidaita rikici da maido da zaman lafiya ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari. Ta haka ya zuwa yanzu dai ba a ga iyakar yake-yaken da Somalia ke fama da su ba tukuna. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China