in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai sauran rina a kaba wajen yaki da cutar sida a yankin da ke kudu da hamadar Sahara a Afrika
2009-12-25 17:36:44 cri
Yanzu, cutar sida ke ci gaba da kawo matsala ga yankin da ke kudu da hamadar Sahara a nahiyar Afrika, kuma ta kawo kalubale ga zaman rayuwar mutane da aikin samun bunkasuwa a wurin. Ko da yake bisa matakan da gwamnatocin kasashen Afrika suka dauka, an cimma nasara sosai wajen yaki da cutar sida a yankin, amma ya zuwa yanzu tsugune ba ta kare ba.

Bisa sabuwar kididdigar da hukumar tsara shirin yaki da cutar sida ta M.D.D ta bayar, an ce, a shekarar 2008, yawan mutanen da suka kamu da cutar sida a yankin da ke kudu da hamadar sahara a Afrika ya kai kimanin miliyan 22.4, kuma ya kai kashi 67 cikin kashi 100 daga cikin dukkan mutanen da suka kamu da cutar a duniya. Kana kuma, Yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar sida da dai sauran cututtuka da abin ya shafa a wannan yanki ya kai kimanin miliyan 1.4, kuma ya kai kashi 72 cikin 100 daga cikin dukkan mutanen da suka mutu sakamakon wannan cuta a duniya.

Amma yawan mutanen da suke kamuwa da cutar sida a yankin da ke kudu da hamadar Sahara a Afrika na samun raguwa a kai a kai.

Game da aikin yaki da cutar Sida, kasashen Afrika da dama sun dauki hakikanin matakai wajen yaki da cutar. A shekarar 1986, bayan da aka samu mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar Senegal, nan take kasar Senegal ta kafa kwamitin yaki da cutar sida, kuma ta kafa kungiyoyin ma'aikatan aikin jinya wajen yaki da wannan cuta. A ko wace shekara, gwamnatin kasar ta kan zuba kudin da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan guda wajen yaki da cutar sida, kuma an kokarta wajen yalwata matakan rigakafi. A cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, yawan mutanen da suka kamu da cutar a wannan kasa ya kai kashi 1.4 zuwa kashi 1.8 cikin 100, kuma Senegal ta zamanto wata kasa da ba a samun mutanen da suka kamu da cutar sida sosai kamar sauran kasashen Afrika.

Kana kuma, a kasar Kenya, sabo da fasahohin zamani da kwaroron roba da aka yi amfani da su, tun bayan shekarar 2002 zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar sida a cikin shekaru 7 da suka gabata ya ragu da kashi 29 cikin 100. Kana, a kasar Botswana da ke kudancin kasashen Afrika, yawan matakan rigakafi da aka yi amfani da su wajen yaki da cutar Sida ya kai kashi 95 cikin 100.

Haka kuma a kasar Swaziland, watau kasa ce da aka samu mutanen da suka kamu da cutar sida mafiya yawa a duniya, mata masu juna biyu da yawansu ya kai kashi 90 cikin 100, suka je asibiti domin neman shawarari wajen yaki da cutar ko samun magunguna ko aikin jinya. Ya zuwa yanzu, yawan yaran da suka kamu da cutar daga mahaifiyarsu ya ragu daga kashi 30 cikin 100 zuwa kashi 20 cikin 100.

Ban da fasahohin zamani da kara yin amfani da kwaroron roba da ba da shawara wajen cutar sida da dai sauran matakan rigakafi, wasu kasashen Afrika sun kokarta wajen yin amfani da sabbin hanyoyi wajen yaki da cutar. A wani asibitin gwamnati na birnin Dares Salaam hedkwatar kasar Tanzania, ana kokarin yin amfani da fasahohin magungunan gargajiya na Sinawa wajen lalubo bakin zaren yaki da cutar. Yanzu, wannan asibiti ya riga ya karbi mutanen da suka kamu da cutar da yawansu ya kai sama da 1000, kuma cikinsu kashi 75 cikin 100 sun samu kyautatuwa bayan da aka yi musu aikin jinya iri na kasar Sin.

Amma, ban da nasarorin da aka samu, aikin yaki da cutar sida a yankin Afrika da ke kudu da Sahara na fuskantar abubuwan cikas da ke shafar samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Alal misali, matsalar talauci ita ce babbar matsalar da ke haddasa yaduwar cutar sida a duniya, kana kuma, wannan matsala ta kara kamari a sakamakon rikicin tattalin arziki na duniya da ya barke a shekarar 2008, hukumar tsara shirin yaki da cutar sida ta M.D.D ta nuna cewa, kafin shekarar 2010, wannan hukuma zai fuskanci matsalar karancin kudaden da yawansu ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 11. A yayin da tun daga karshen rabin shekarar bana, sabo da karancin kudade, hukumomin da ke ba da aikin jinya a yankin gabashin kasashen Afrika, suka daina karbar sabbin mutanen da suka kamu da cutar, kuma su kan ba da magunguna ne kawai ga masu kamu da matsala.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China