in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin rigakafin raguwar darajar kudin RMB ya zama nauyi na farko da ke kan gwamnatin kasar Sin
2009-12-20 20:49:28 cri
A ran 7 ga wata, an rufe taron shekara-shekara kan aikin tattalin arziki da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya a nan birnin Beijing. A yayin taron, a bayyane ne gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta sanya aikin yin rigakafin raguwar darajar kudin RMB ya zama nauyi na farko da ke kanta a fuskar aikin tattalin arziki da za ta yi a shekarar 2010. Dr. Zhang Tao wanda ke nazarin tattalin arziki a cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin ya ce, "Bisa sabuwar kididdigar da aka bayar, an ce, sana'o'i 21 daga cikin muhimman sana'o'i 24 na kasar Sin suna samar da kayayyaki fiye da yadda ake bukata. Idan babu bukatu a kasuwa, shi ke nan, farashin kayayyaki zai ragu. Sabo da haka, a ganina, a cikin gajeren lokaci mai zuwa, ba zai yiyuwa a samu raguwar darajar kudin RMB na kasar Sin ba. An yi hasashen cewa, saurin hauhawar farashin kayayyakin masarufi zai ragu da kashi 0.5 cikin dari a duk shekarar da ake ciki. Amma a shekarar 2010, lokacin da tattalin arziki yake samun karuwa, an kiyasta cewa, saurin hauhawar farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin zai karu da kashi 2 cikin dari. Wannan adadi ne da ake iya amincewa da shi."

Nazarin da Dr. Zhang Tao ya yi ya yi daidai da sakamakon da bankin duniya ya bayar kwanan baya a cikin wani rahoto game da tattalin arzikin kasar Sin. A ganin bankin duniya, saurin hauhawar farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin zai ragu da kashi 0.8 cikin dari.

A irin wannan halin da ake ciki, a yayin taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, me ya sa aka jaddada cewa za a kara mai da hankali kan yadda za a yi rigakafin raguwar kudin RMB da za a yi ya jawo hankulan mutane? Wasu kwararru suna tsammanin cewa, a shekarar bara, gwamnatin kasar Sin ta bayar da jerin manufofin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, a waje daya, ta bayar da wasu manufofin kasafin kudi da na kudi masu sassauci da suke dacewa, kuma ta zuba dimbin jari kan ayyukan yau da kullum. A cikin farkon watanni 10 na shekarar da muke ciki, yawan karin rancen kudin da bankuna suka samar ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 9. Amma a farkon shekarar da muke ciki, an yi hasashen cewa yawan rancen kudin da za a samar a wannan shekara zai kai kudin Sin yuan biliyan dubu 5. Dimbin karin rancen kudin da aka samar ya zama matsala ga kokarin yin rigakafin aukuwar raguwar darajar kudi, kuma ya jawo hankalin gwamnatin kasar kwarai. Mr. Cheng Siwei, wanda ya shahara sosai wajen nazarin ilmin tattalin arziki a kasar Sin ya ce, "Ba za a iya kyale hadarin da mai yiyuwa ne zai haddasa raguwar darajar kudi ba. Bisa ilmin tattalin arziki, lokacin da ake samar da karin takardun kudi, ko yawan takardun kudin da aka bayar ya wuce bukatun da ake da su a kasuwa, tabbas hakan zai haddasa raguwar karfin kudi wajen sayayya, wato farashin kayayyaki zai yi ta karuwa. Amma wannan alama ba ta fito a bayyane ba tukuna sabo da ana bukatar wasu lokuta daga lokacin samar da karin takardun kudi zuwa lokacin samun karuwar farashin kayayyaki a kasuwa. Sabili da haka, kamata ya yi a yi rigakafin aukuwar wannan hadari."

Hadari daban da dole ne a yi rigakafinsa shi ne illar da farashin kayayyaki na kasuwannin kasa da kasa zai kawo wa farashin kayayyaki na kasar Sin. Dr. Zhang Tao ya kara da cewa, "Bisa sabon halin da ake ciki, an gano cewa, yanzu farashin man fetur da sauran muhimman kayayyakin da ake ciniki da su a kasuwannin duniya sun sake karuwa sosai. Alal misali, farashin man fetur ya karu da kashi 60 cikin dari bisa na farkon shekarar da muke ciki. Wani daban kuma shi ne darajar dalar Amurka tana raguwa cikin sauri. Sakamakon haka, kasashe da yawa suna kokarin sayen muhimman kayayyaki a maimakon dalar Amurka domin tabbatar da darajar kudin ajiya. Dimbin jarin da ake zubawa da kokarin magance hadari su ne suke haddasa hauhawar farashin kayayyaki. Lokacin hauhawar farashin muhimman kayayyakin da ake cinikinsu a kasuwannin duniya, an samu karuwar kudaden da ake kashewa domin yin kayayyaki a masana'antu. Sabo da haka, babu sauran hanyar da za a iya zaba, sai masana'antu su daga farashin kayayyaki domin tabbatar da samun riba. Sakamakon haka, masu sayayya suna fuskantar matsin lambar hauhawar farashin kayayyakin da suke saya a kasuwannin cikin gida na kasar Sin."

A hakika dai, a shekarar bana, farashin wasu kayayyaki ya riga ya karu a kasar Sin. Alal misali, an taba daidaita farashin dizal har sau 8, wato ya samu hauhawa har sau biyar, tare da raguwa har sau 3. Sakamakon haka, farashin dizal ya karu da kashi 27 cikin dari bisa na farkon shekarar da ake ciki. A waje daya, farashin abinci da na man girki da na ruwa da na wutar lantarki da na iskar gas ta girki da suke da nasaba da albarkatun kasa dukkansu sun soma karuwa. Game da wannan yanayi, Mr. Zhang Liqun wanda ke nazarin harkokin tattalin arziki daga dukkan fannoni a cibiyar nazarin neman ci gaba ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, muhimmin dalilin da ya sa farashin ruwa da na wutar lantarki da na iskar gas ta girki suka samu hauhawa shi ne ana yin gyare-gyare kan tsarin tabbatar da farashin kayayyaki lokacin da farashin kayayyaki yake arha sosai, ba ruwansa da raguwar darajar kudi. Mr. Zhang Liqun ya ce, "Dalilin da ya sa hauhawar farashin wadannan kayayyaki shi ne, gwamnatinmu tana kyautata tsarin tabbatar da farashin kayayyakin da suke da nasaba da albarkatun kasa domin kokarin cimma burin yin tsimin makamashi da kuma rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kuma masu dumama yanayin duniya. Wannan yana da ma'ana sosai wajen kafa wata sabuwar hanyar kawo arziki da ta yin rayuwa irin ta tsimin makamashi. A shekarar da muke ciki, farashin kayayyakin masarufi ba su tashi sosai ba, wannan ya zama wata dama ga kokarin yin gyare-gyare kan farashin albarkatun kasa. Sabo da ana daidaita farashin kayayyaki ne bisa manufofin da gwamnati ta tsara, ana iya kayyade irin wannan saurin, wato farashin kayayyaki ba zai samu karuwa cikin sauri ba a nan gaba, kuma ba ruwansa da maganar raguwar darajar kudi."

A yayin taron da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya ta fuskar tattalin arziki, a shekarar 2010, kasar Sin za ta ci gaba da manufofin kasafin kudi da na kudi masu sassauci da suke dacewa. Galibin masanan da ke nazarin tattalin arziki suna ganin cewa, saurin karuwar rancen kudi zai ragu a kasar Sin a shekara mai zuwa. Mr. Zhuang Jiansheng, wani muhimmin mai nazarin tattalin arziki a ofishin bankin raya kasashen Asiya da ke nan kasar Sin ya ce, mai yiyuwa ne babban bankin kasar Sin zai dauki wasu matakai a farkon rabin shekara mai zuwa domin kayyade saurin karuwar rancen kudin da ake samarwa a yunkurin raguwar darajar kudi. Mr. Zhuang ya ce, "Idan bankunan kasuwanci sun samar da rancen kudi fiye da kima a kowane wata na farkon rabin shekara mai zuwa, kuma farashin kayayyaki zai samu hauhawa sosai. A ganina, tabbas ne babban bankin kasar Sin zai dauki matakan daidaita irin wannan hali. Alal misali, mai yiyuwa ne zai samar da takardun babban bankin domin dawowar wasu takardun kudi daga kasuwanni, kuma zai ba da shawara irin ta jagoranci ga bankunan kasuwanci, har ma mai yiyuwa ne zai daidaita yawan kudin da ya kamata bankunan kasuwanci su ajiye a babban banki."

A gaban matsin lambar da ke kasancewa a nan kasar Sin sakamakon matsalolin kudi na kasuwannin kasa da kasa, wasu masana sun bayyana cewa, a gun taron shekara-shekara ta fuskar tattalin arziki da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya, an nemi a daidaita tsarin sana'o'in masana'antu da neman raya tattalin arziki da ke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli kadan da kuma a yi kokarin rage yin amfani da kayayyaki, musamman makamashin da ake shigowa da su daga kasashen waje. Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokarin karuwar yawan kudin da mazauna suke samu domin kara karfinsu na tinkarar hauhawar farashin kayayyaki. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China