in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An soma safarar man gas daga kasar Turkmenstan zuwa kasar Sin
2009-12-14 18:43:06 cri

A ran 14 ga wata a wata masana'antar sarrafa man gas ta kasar Turkmenstan, an yi bikin soma safarar man gas ta bututun da aka shimfida a tsakanin kasar Sin da kasashen Turkmenstan da Kazakhstan da Uzbekistan wadanda suke yankunan tsakiyar nahiyar Asiya. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Turkmenstan da takwarorinsa na wadannan kasashe 3 dukkansu sun halarci wannan biki.

A yayin bikin, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke ziyara a kasar Turkmenstan ya bayar da jawabi, inda ya nuna cewa, aikin bututun safarar man gas da aka shimfida a tsakanin kasar Sin da kasashen Turkmenstan da Uzbekstan da Kazakhstan abin koyi ne da ke bayyana yadda wadannan kasashe hudu suke yin hadin gwiwa irin ta moriyar juna. Suna yin hadin gwiwa a fannin albarkatun kasa bisa ka'idojin moriyar juna da moriyar juna cikin adalci da kuma neman moriya tare.

Mr. Hu ya jaddada cewa, yanzu halin tattalin arziki da kasashen duniya ke ciki yana ta samun sauye-sauye sosai. Ya kamata kasashen hudu su yi fama da kalubaloli cikin hadin gwiwa domin ingiza samun ci gaban yankin da suke ciki tare.

Shugabannin sauran kasashe 3 sun kuma bayar da jawabai bi da bi, sannan sun bude makullin bututun tare.

Wannan bututun safarar man gas da tsawonsa ya kai kilomita 1833 ya tashi daga bakin iyakar da ke tsakanin kasashen Turkmenstan da Uzbekstan, sannan ya wuce kasashen Uzbekstan da Kazakhstan ya isa garin Holgos na kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China