in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin cika alkawarin tinkarar sauyin yanayi
2009-12-13 21:27:00 cri
A kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, ya zuwa shekara ta 2020, yawan hayaki mai dumama yanayi da za a fitar zai ragu da kashi 40 zuwa kashi 45 cikin dari bisa na shekara ta 2005, kuma gwamnatin kasar Sin za ta sanya wannan burin da take son cimmawa a cikin dogo da matsakaicin lokacin shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na kasar. A jajibirin babban taron Copenhagen game da batun sauyin yanayin duniya, kasar Sin ta bayar da wannan burin da take son cimmawa filla filla, wannan wani kalubale ne kuma wata dama ce ga kasar Sin wadda ke matsakaicin zango kan hanyar raya masana'antu. Mr. Xiong Bilin, wani jami'in da ke aiki a kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya ce, "Mun riga mun tsara ka'idoji masu tsanani wajen shigar da wasu masana'antu da sa ido kan yadda suke bin ka'idojin kiyaye muhalli da kuma yadda suke amfani da gonaki bisa doka. Kuma za mu aiwatar da manufofin kudi irin na kare wasu masana'antu da kuma kayyade bullowar wasu masana'antu lokacin da ake duba takardun neman izinin kafa irin wadannan masana'antun da mai yiyuwa ne za su gurbata muhalli. A waje daya, za a kara sa kaimi ga manyan masana'antu da su harhada wasu kananan takwarorinsu da kuma kafa tsarin yada bayanai da dai sauransu."

Mr. Xiong Bilin ya fadi haka ne sabo da yanzu kasar Sin tana daukar wani mataki na yin watsi da wasu masana'antu wadanda suke matsayin koma baya, kuma suke gurbata muhalli domin tabbatar da ci gaban masana'antu ba tare da tangarda ba da kuma cimma burin yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Wadannan masana'antu suna shafar masana'antun narkar da karfe da na yin siminti da na yin gilas wadanda suke amfani da makamashi da yawa kuma suke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli sosai.

Lokacin da take kayyade bunkasuwar masana'antu masu gurbata muhalli kuma masu yin amfani da dimbin makamashi, kasar Sin tana kuma sa kaimi ga kokarin sake yin amfani da kayayyaki da abubuwan da masana'antu suke jebarwa. A kwanan baya, injunan samar da wutar lantarki na kamfanin yin kayayyakin sinadari na birnin Zhangjiagang na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin sun soma aiki. Mr. Yuan Yafei, mataimakin babban daraktan wannan kamfani ya ce, wani abu daban na wadannan injuna shi ne ba su yi amfani da sauran makamashi ba, sai dai iskar da kamfaninmu yake fitarwa.

"Muna amfani da iskar da ake fitarwa lokacin da ake sarrafa sinadarori iri iri. Irin wadannan iska mai zafi suna iya samar da wutar lantarki da yawansa ya kai kilowatts dubu 50 a kowace awa. Sabo da haka, za mu iya yin tsimin kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan miliyan 250."

Yanzu kasar Sin tana kokarin canja tsarin makamashin da take amfani da shi, wato ba za ta yi amfani da kwal kawai ba, yanzu tana kokarin yin amfani da makamashi marasa gurbata muhalli, kamar su makamashin iska da hasken rana. Yanzu yawan makamashin iska da na hasken rana da kasar Sin ke amfani da su ya kai kashi 10 cikin dari bisa na jimillar makamashin da take amfani da su. Amma bisa shirin yin amfani da sabbin makamashi da ake tsarawa yanzu, gwamnatin kasar Sin za ta kebe kudaden da yawansu zai kai kudin Sin yuan biliyan dubu 3 wajen raya sana'o'in samarwa da kuma yin amfani da sabon makamashi mai tsabta. Kuma ana fatan yawan sabon makamashin da za a yi amfani da shi a kasar Sin zai kai kimanin kashi 15 cikin dari bisa na jimillar makamashin da ake amfani da shi a kasar.

A lokacin da ake kara saurin raya tattalin arziki bai daya a duk duniya, sana'o'in ba da hidima wadanda suke tsimin makamashi, amma darajarsu take samun karuwa sun riga sun zama sabon karfin raya tattalin arziki. Ya zuwa yanzu, yawan GDP da sana'o'in ba da hidima suke bayarwa a kowace shekara ya kai kimanin kashi 40 cikin dari bisa na jimillar GDP ta kasar. Amma a galibin kasashen da suka ci gaba, wannan adadi ya kai kashi 70 cikin kashi dari. Sabo da haka, a kwanan baya, Mr. Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan shigowa da fasahohin zamani daga kasashen waje domin kara saurin raya sana'o'inta na ba da hidima. Mr. Chen ya ce, "Kasar Sin za ta shigo da baki masu zuba jari bisa manyan tsare-tsare a fannonin zirga-zirga da kudi da inshora da kiwon lafiya da na zane-zane da kuma na sayarwa da dai makamatansu domin kara saurin kyautata kamfanonin ba da hidima. Sannan za a sa kaimi ga baki masu zuba jari da su shiga aikin nazari da kirkiro sabbin manhaja da neman kwangiloli a tsakanin kasa da kasa da kuma sana'o'in sufurin kayayyaki. Bugu da kari, za ta kara mai da hankali wajen shigowa da fasahohin zamani da hanyoyin zamani na gudanar da kamfanonin ba da hidima domin kara saurin zamanintar da su."

Amma ba abu ne mai sauki ba ga kasar Sin wajen cika alkawarinta da ta dauka kwanan baya. Ta kasance tamkar wata kasa mai tasowa, kasar Sin tana fuskantar matsalolin dimbin mutane da ingancin tattalin arziki da na zaman al'umma wadanda suke cikin halin koma baya da dai sauransu. Sabo da kasar Sin tana bukatar raya tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba, kuma tana bukatar samar da isassun guraban aikin yi ga jama'a, kuma tana bukatar kyautata ingancin zaman rayuwar jama'a, dole ne tana bukatar yin amfani da albarkatai da yawa. Sakamakon haka, tabbas ne yawan abubuwa masu dumama yanayin duniya zai ci gaba da karuwa a cikin wasu lokuta. A lokacin da yake yin shawarwari da shugabannin kungiyar EU a karo na 12 a nan kasar Sin a kwanan baya, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya kuma amince da cewa, kasar Sin za ta sha wahalhalu da yawa wajen cika alkawarinta. Amma a waje daya, ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ba za ta canja matsayi da niyyarta wajen mai da hankali sosai kan batun sauyin yanayin duniya ba. Tabbas ne kasar Sin za ta cika alkawarin da ta dauka. Mr. Wen ya ce, "An riga an yi nazari da kuma dudduba shirinmu har sau da yawa bisa ilmi da hanyoyin kimiyya. Wannan shiri yana dacewa da hakikanin halin da ake ciki kasar Sin. Mun dauki wannan alkawari da kanmu sabo da ba abin wasa ba ne. Za mu yi namijin kokarinmu wajen cimma wannan buri domin shi ne babbar gudummawar da kasar Sin za ta bayar ga duk duniya wajen tinkarar sauyin yanayin duniya. Tabbas ne za mu cika wannan alkawari kamar yadda muka dauke shi wajen neman ci gaba ba tare da tangarda ba."

Gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsai da kuduri cewa, za ta kebe wasu wurare domin gwada aikin raya tattalin arziki tare da yin amfani da makamashi mai kunshe da Carbon kadan, kuma za ta kafa tsarin dudduba yadda ake rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya. Sannan yanzu kasar Sin tana kara saurin nazarin fasahohin yin amfani da sabon makamashi maras dumama yanayi kuma maras gurbata muhalli. Haka kuma, tana kokarin yin amfani da irin wannan sabon makamashi a cikin masana'antu domin kokarin kafa tsare-tsaren masana'antu da gine-gine da zirga-zirga marasa gurbata muhalli wadanda suke tsimin makamashi. Har ma tana kokarin kirkiro sabon salon yin amfani da makamashi. Wannan ita wajababbiyar hanya da kasar Sin za ta bi domin neman ci gaba ba tare da tangarda ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China