in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantaka a tsakanin kasashen Namibia da Sin za ta kara samun ingantuwa, in ji shugaban farko na kasar Namibia Sam Nujoma
2009-12-09 21:05:12 cri
Kasar Namibia kasa ce mafi kankanta a Afirka, kasar Sin ta taba ba ta taimako yayin da take neman fita daga mulkin mallaka da kuma samun 'yancin kanta. Shugaban farko na kasar Namibia Sam Nujoma tsohon amini ne na jama'ar kasar Sin tun bayan shekaru 60 ko 70 na karnin da ya gabata. Ko da yake yanzu Mr. Nujoma ba shugaban kasar Namibia ba ne, amma yana taka muhimmiyar rawa a kasar. A kwanan nan, yayin da Mr. Nujoma ke zantawa da wakilinmu a birnin Windhoek, babban birnin kasar Namibia, ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen Namibia da Sin za ta kara samun ingantuwa. To yanzu ga cikakken bayani.

A cikin shekaru kusan 20 da suka gabata bayan da kasar Namibia ta samu 'yancin kanta, kasar ta samu manyan nasarori a fannoni daban daban wajen raya kasar. Mr. Nujoma ya yi alfahari sosai da wannan, a waje daya kuma ya fahimta cewa, in wata kasa tana son kara samun ci gaba, to tabbas ne a kyautata ingancin jama'a da kuma kara kebe kudade a fannin ba da ilmi. Mr. Nujoma ya kara da cewa,

"bayan da Jam'iyyar Swapo ta kasar Namibia ta hau karagar mulkin kasar a shekara ta 1990, kasar ta samu babban sauyi. Kafin kasar ta samu 'yancin kai, ba mu da hanyar mota zuwa kasar Botswana, amma yanzu hanyoyin mota da muka shimfida ba kawai sun hada da kasashen Botswana da kasar Afirka da Kudu ba, hatta ma sun isa zuwa birnin Maputo na kasar Mozambique. A arewacin kasarmu kuma, hanyoyin mota sun isa zuwa bakin iyaka a tsakanin kasarmu da kasar Angola. Ba kawai gwamnatin kasarmu ta shimfida hanyoyi ba, a'a har ma ta gina asibitoci da makarantun sakandare da jami'ar Namibia da kwalejin fasahohin wasanni. Ko da haka, muna fahimtar cewa, ya kamata mu kara kebe kudade a fannin ba da ilmi da kuma shirya kwasa-kwasan horaswa."

Bisa sakamakon babban zabe da aka bayar a ran 4 ga wata, an ce, Jami'yyar Swapo da ke kan karagar mulkin kasar Namibia cikin dogon lokaci ta samu kujeru 54 daga cikin kujeru 72 na majalisar dokokin kasar, kuma shugaba Hifikepunye Pohamba na kasar ya sake lashe zabe. Yayin da muke tabo zance kan wannan nasarar da jam'iyyar ta samu, Mr. Nujoma ya ce, ya fi son daukar ra'ayi kan batun a matsayin nahiyar Afirka. Ya ce,

"An kafa Jam'iyyar Swapo ne bisa ra'ayin neman samun hakikanin 'yanci da 'yancin kai, wanda kuma ya kamata ya samu amincewa daga dukkan kasashen da ke son zaman lafiya. Jam'iyyar ba ta taba yin watsi da wannan ra'ayi ba ko kusa, kuma tana daukar ra'ayin mallakar albarkatu na kasar Namibia. Za mu yi kokari tare da sauran kasashe membobin kungiyar AU domin dukufa kan samun hadin kan dukkan nahiyar Afirka. In an cimma wannan buri, to Afirka za ta zama wata nahiyar da ta samu amincewa sosai a duniya, musamman ma a fannin albarkatu."

Ran 1 ga watan Oktoba na shekarar bana, Mr. Nujoma ya halarci bikin taya murnar cika shekaru 60 da karfuwar sabuwar kasar Sin bisa gayyatar da aka yi masa a matsayinsa na wani tsohon amini na jama'ar Sin. Game da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, Mr. Nujoma ya ce,

"Na ziyarci kasar Sin ba da jimawa ba yayin da take murnar cika shekaru 60 da kafuwarta, ko da yaushe mu kan kiyaye dangantaka ta kud da kud tare da Sin. Kuma dangantakar za ta kara samun ingantuwa."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China