in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kada mu manta da 'yan gudun hijira a Afirka
2009-12-03 13:32:38 cri
Batun 'yan gudun hijira da yake-yake da rikice-rikicen siyasa da na kabilu da na addini suka hadddasa na ta caza kan kasashen duniya matuka. 'Yan gudun hijira da suka fito daga Afirka sun fi jawo hankali. Batun 'yan gudun hijira ya kasance babban cikas wajen hana samun zaman lafiya da bunkasuwa a Afirka, a maimakon matsayin batun jin kai kawai. Bai kamata ba kasashen duniya su kyale batun.

Nahiyar Afirka na da fadi sosai kuma tana da albarkatu mai yalwa, amma a sakamakon mulkin mallaka na dogon lokaci da rashin kwanciyar hankali na tsawon goman shekaru bayan da suka samu 'yancin kai da kuma gazawa samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, batun 'yan gudun hijira na ta lalacewa. Bisa kididdigar da kungiyar Tarayyar Afirka wato AU ta yi, an ce, yanzu an samu 'yan gudun hijira fiye da miliyan 17 a duk fadin Afirka.

A cikin 'yan gudun hijira da ake samu a Afirka, yawan wadanda suka zama 'yan gudun hijira a sakamakon yake-yake da rikice-rikice ya zama na farko har kullum. Bayan da kasashen Afirka suka sami 'yancin kai, wasu kasashe su kan ta da rikici a tsakaninsu, har ma wasu kasashe kan samu yakin basasa. Ta haka fararen hula da yawa sun zama 'yan gudun hijira, haka kuma, mutane da yawa sun rasa wurin kwana, sun yi kama da yadda 'yan gudun hijira suke kasancewa, amma ba su ketare iyakar kasa ba. Bisa kididdigar da hukumar harkokin 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta samu, an ce, ya zuwa karshen watan Maris na shekarar bana, a kasashe 16 na tsakiya da na gabashin Afirka, yawan 'yan gudun hijira da wadanda suka rasa wurin kwana, ba su ketare iyakar kasa ba ya wuce miliyan 11.

Gazawa samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da saurin karuwar yawan mutane su ma sun kasance muhimman dalilan da suka sa ba a iya sassauta matsalar 'yan gudun hijira ba. Kafin kasashen Afirka sun sami 'yancin kai, an dade ana yi musu mulkin mallaka, bayan da suka sami 'yancin kai, kasashen yammacin duniya sun sarrafa muhimman fannonin tattalin arzikinsu. Kasashe da yawa na Afirka sun rasa kudin bunkasuwa, da yawa daga cikinsu sun ci basususka matuka. Makudan basusukan da suka ci sun kawo musu babban nauyi ta fuskar kudi tare kuma da kawo cikas a fannin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa. Rikicin kudi na duniya da ya auku a shekarar bara ya kara raunana bunkasuwar kasashen Afirka. Dadin dadawa kuma, hatsin da mutanen Afirka suka samu bai ishe su ba. Saurin karuwar yawan mutane ya haddasa matsalar karancin albarkatun halittu da bacewar albarkatun halittu a wasu yankunan Afirka. A wasu yankunan Afirka, tsananin kwararowar hamada ya haifar da tsananin sauyin yanayi da yawan aukuwar bala'u fiye da kima, ta haka wadannan wurare ba su dace da mutane ba, mazauna wurin sun zama 'yan gudun hijira a sakamakon sauyawar yanayi.

Haka zalika, gazawa samun saurin bunkasuwar tattalin arziki ta kawo cikas ga warware matsalar 'yan gudun hijira yadda ya kamata. Tsananin matsalar ta lalata kwanciyar hankali da bunkasuwar Afirka sosai. A wasu wurare, watakila a kan tsugunar da 'yan gudun hijira a kasashe masu kwanciyar hankali, amma a Afirka, kasashen da suka karbi 'yan gudun hijira kasashe ne da ke fama da talauci. 'Yan gudun hijira kan sha wahala matuka, ba su iya aika da kudi zuwa garinsu ba, sun tsananta wa kasashen da suka karbe su matsalar kudi. Sun kawo wa wadannan kasashe illa a fannonin bunkasuwar tattalin arziki da tsaron al'umma da daidaiton muhalli da huldar diplomasiyya.

Batun 'yan gudun hijira na Afirka na da nasaba da bunkasuwa da kwanciyar hankali a wannan nahiya. In ba a iya warware ta yadda ya kamata ba, a karshe dai zai yi illa ga kasashen Turai da Gabas ta Tsakiya da sauran wuraren duniya. Saboda haka, ya kamata kasashen duniya, musamman ma kasashe masu sukuni su rika bai wa 'yan gudun hijira na Afirka da kasashen Afirka hakikanin taimako.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China