in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2009-11-25 17:47:05 cri

Bisa yarjejeniyar hadin kai a tsakaninta da gwamnatin kasar Sudan, rundunar UNAMID ta bayar da taimako a fannin fasaha ga zaben da za a shirya a Sudan a watan Afrilu na shekarar 2010. Ma'aikatan UNAMID suna aiki a cikin kungiyoyi 69 da ke kula da harkokin zabe a arewacin yankin Darfur na kasar Sudan yayin da suke yin rajistar jama'a da suke da ikon kada kuri'a bisa doka.

Bisa abubuwan da aka tanada cikin shirin da abin ya shafa, an ce, an fara yin rajistar ne daga ran 1 ga watan Nuwamba, tsawon lokacin yin rajista zai kai kwanaki 30, amma a halin yanzu za a kammala aikin yin rajistar a ran 26 ga wata, sabo da za a yi Babban Sallah. Bisa shirin da aka yi, an ce, za a sanar da sunayen mutanen da suka yi rajista a ran 1 ga watan Disamba, bayan haka kuma, za a yi sauran ayyuka daga ran 2 ga watan Disamba zuwa ran 5 ga watan Janairu na shekarar 2010.

Jama'a, bayan haka kuma bari mu sake duba wani labari da muka samu daga shafin internet na Garowe Online na kasar Somaliya, wanda aka fitar a ran 23 ga wata, inda aka mai da hankali sosai kan wani taro cikin sirri a tsakanin jami'an kasashen Habasha da Somaliya.

Bisa labarin da muka samu daga shafin internet na Garowe, an ce, jami'an kasar Habasha sun wuce bakin iyaka sun shiga cikin makwabciyarta kasar Somaliya sun yi wani taro cikin sirri a wani kauye mai suna Yeed da ke kudu maso yammacin bakin iyaka, inda jami'an Habasha suka gana da da tsofaffin shugabannin Somaliya da ke yankin Bakool a kudancin kasar.

Wasu majiyai sun gaya wa Garowe Online cewa, a cikin wannan taron asiri, an fi mai da hankali kan karfafa karfin sojojin kasar Somaliya, domin yaki da masu daukar makamai da ke sarrafa yawancin muhimman wuraren yankin Bay, ciki har da garin Baidoa, babban garin yankin.

Majiyai sun ce, an shirya wannan taro ne cikin sirri, sabo da haka, ba su son bayyanawa manema labaru sakamakon da aka samu a gun taron. Amma sun ce, wani jami'in Somaliya da ya shiga cikin taron sirrin ya ce, bangarorin biyu da suka halarci taron sun yarda da hadin kai a tsakanin sojojinsu.

Jama'a, bayan haka kuma bari mu sake duba wani labari da muka samu daga jaridar 'Daily Nation' ta kasar Kenya, wadda aka buga a ran 23 ga wata, inda aka bayyana cewa, shguaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya riga ya jinkirtar da lokacin kai ziyara a kasar Zimbabuwe.

Jaridar 'Daily Nation' ta kasar Kenya ta ce, shugaba Zuma ya yanke shawarar jinkirtar da zuwa Zimbabuwei, masu ba da shawara gare shi sun nuna rashin jin dadi game da bangarorin da abin ya shafa dangane da rikicin siyasa na Zimbabuwei.

A ran 5 ga watan Nuwanba, wasu shugabannin da abin ya shafa na Afirka sun shirya wani taron koli a birnin Maputo, babban birnin kasar Mozambique, inda aka ba da wa'adi na tsawon kwanaki 15 zuwa 30 ga shugaban kasar Zimbabuwei Robert Mugabe da sauran bangarori da su kawar da bambancin ra'ayoyinsu. Amma kwanaki 15 sun riga sun wuce, kuma ba su shirya ko wane irin taron yin shawarwari ba. A halin yanzu, gwamnatin kasar Afirka ta kudu tana fatan za a iya kawar da rikicin siyasa na Zimbabuwei a ran 5 ga wata Disamba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China