in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da babban taro karo na 10 tsakanin 'yan kasuwa Sinawa dake ketare
2009-11-20 17:55:53 cri

Ranar 20 ga wata, a Manila, babban birnin kasar Philippines, an kaddamar da babban taro karo na 10 tsakanin 'yan kasuwa Sinawa dake zaune a ketare, inda shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Jia Qinglin ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai lakabin "Inganta mu'amala tsakanin 'yan kasuwa Sinawa dake zaune a ketare, da neman bunkasuwa tare". A jawabin, Jia Qinglin ya nuna babban yabo ga babbar gudummawar da Sinawa dake zaune a kasashen ketare suke bayarwa a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta kasar Sin, gami da muhimmiyar rawar da wannan babban taro ke takawa, inda ya ce: "Babban taron 'yan kasuwa Sinawa dake ketare ya kafa wani muhimmin dandali ga 'yan kasuwa Sinawa a duniya domin kara samun fahimta, da inganta mu'amala da cudanya tsakanin juna, haka kuma taron yana taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban, ciki kuwa har da raya tattalin arziki na kasar Sin da sauran sassan duniya inda 'yan kasuwa Sinawa ke zaune." A halin yanzu, akwai Sinawa sama da miliyan 30 wadanda ke zaune a sassa daban-daban a duniya, babban taron da aka yi ya samu halartar 'yan kasuwa Sinawa da adadinsu ya tasam ma dubu 3 daga kasashe da yankuna fiye da 20, wadanda za su yi shawarwari da tattaunawa muhimman batutuwa iri-iri, ciki kuwa har da yin kwaskwarima ga harkokin bankuna da hada-hadar kudi, da bunkasa masana'antun 'yan kasuwa Sinawa dake ketare da sauransu.
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China