in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin samar da man fetur na Sin ya kulla yarjejeniyoyi 3 da Sudan
2009-11-20 16:31:12 cri
A ran 20 ga wata, bisa labarin da aka bayar an ce, kamfanin samar da man fetur na Sin (CNPC) ya kulla yarjejeniyoyi 3 a fannin man fetur da gwamnatin Sudan a kwanan baya.

Daya daga wadannan yarjejeniyoyi 3 shi ne, kamfanin CNPC da ma'aikatar makamashi da ma'adinai ta Sudan, sun sami fahimtar juna kan aikin habaka kamfanin tace makamashi a zagaye na 2 dake Khartoum. Bisa labarin da aka bayar, an ce, an kafa kamfanin tace makamashi dake Khartoum a watan Yuni a shekarar 1997 wanda a yayin shirin habaka shi, kamfanin CNPC da ma'aikatar makamashi ta Sudan dukkansu suna da hannun jarin wannan kamfani kamar kashi 50 bisa 100. An yi amfani da wannan kamfani a watan Mayu a shekarar 2000. A watan Yuli na shekarar 2006, an kammala aikin habaka kamfanin a zagaye na 1, yawan gurbataccen man fetur da kamfanin ya tace ya kai ton miliyan 5 a ko wace shekara. Kawo yanzu, kamfanin ya samar da man fetur kamar kashi 80 bisa 100 na bukatun kasuwannin Sudan.

Sauran yarjejeniyoyi biyu su ne, kara samu fahimtar juna ta fuskar yin hadin gwiwa kan ayyukan man fetur a Sudan, ta biyu ita ce, samun fahimtar juna a fannin cinikayyar gurbataccen man fetur.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China