in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya gana da Zhou Yongkang
2009-11-20 15:11:35 cri

A ran 18 ga wata, a Pretoria, babban birnin kasar Afrika ta kudu a fannin siyasa, shugaban kasar Afrika ta kudu kuma shugaban Jam'iyyar ANC Jacob Zuma ya gana da zaunannen wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma sakataren hukumar harkokin shari'a ta tsakiyar kasar Sin Zhou Yongkang dake ziyara a kasar.

A yayin ganawar, mista Zuma ya ce, a shekarun baya, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu musamman a fannin siyasa ta samu inganta da bunkasuwa. A halin da ake ciki, kamata ya yi kasashen biyu su kara karfafa yin mu'amala da daidaito a kan manyan batutuwa na duniya da yankuna, da kuma sa kaimi kan hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Mista Zhou Yongkang ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 11 da suka gabata tun da aka kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, dangantakar a tsakaninsu ta samu bunkasuwa da sauri a dukkan fannoni, kuma amincewar juna a fannin siyasa tana karuwa, kuma an samu sakamako mai kyau wajen hada kai a dukkan fannoni.

Mista Zhou ya kara da jaddada cewa, gwamnatin Sin ta sanar da sabbin matakai guda takwas a yayin taron ministoci karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika. Kasar Sin tana fatan hadin kai da kasashen Afrika don tabbatar da wadannan matakai, da ci yar da dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afrika ta kudu da sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afrika gaba.(Asabe)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China