
Ran 20 ga wata ranar yara ta kasa da kasa. Kuma a wannan rana a nan birnin Beijing, mataimakin shugabar ofishin kula da harkokin kwamitin mata da yara na majalisar gudanarwa ta Sin Madam Su Fengjie ta furta cewa, yanayin bunkasuwar yara da Sin take ciki ya sami kyautatuwa a sakamakon kokarin da Sin ta yi.
A ran 20 ga wata a nan birnin Beijing, asusun yara na MDD da kafar yada labaru ta Xinhua sun gabatar da littafi mai suna "bayani kan yaran kasa da kasa" da Sinanci domin murnar cika shekaru 20 da aka gabatar da yarjejeniyar hakkin yara. Su Fengjie ya furta haka yayin da ya halarci wannan biki cewa, bayan kokarin da Sin ta yi, kasar Sin ta samu ci gaba sosai kan fannonin lafiyar jiki, da abinci mai gina jiki, da kuma aikin koyarwa da sauransu na yara, hakan ya biya bukatun shirin bunkasa ayyukan yara daga shekarar 2001 zuwa 2010 da burin samun bunkasuwa a cikin shekaru 1,000 masu zuwa na MDD. A karshen shekarar 2008, yawan mutuwar mata masu juna biyu ya ragu da kimanin kashi 2 bisa 3 idan an kwatanta shi bisa na shekarar 1989 yayin da yawan mutuwar jarirai ya ragu da kashi 2 bisa 3 ko fiye idan an kwatanta shi bisa shekarar 1991. Yawan yaran da suka shiga makaranta a lokacin da aka tanada ya kai kashi 99.54 bisa 100. Ban da wannan kuma, gwamnati da al'umma sun ba da kariya ta musamman ga yara masu talauci da nakasassun yara da kuma yara masu gudun hijira, hakan ya sa yanayin al'umma na kawo ci gaban yara da kyautatuwa.(Amina)

