Liang Guanglie ya bayyana cewa, bayan an sake kafa dangantakar diplomasiya a tsakanin Sin da Senegal, bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa a fannoni daban daban. Senegal ta nuna goyon baya ga babbar manufar dinkuwar kasar Sin cikin lumana, kuma kasar Sin ta nuna godiya ga kasar Senegal da ta nuna goyon baya ga kasar Sin wajen manyan batutuwa na duniya. Ban da haka kuma, kasar Sin ta mai da hankali a kan bunkasuwar dangantakar a tsakaninta da sojojin kasar Senegal, kuma tana son yin kokari tare da Senegal wajen ci gaba da daga dangantakar hadin gwiwa a tsakanin sojojin kasashen biyu zuwa sabon matsayi.
Abdoulaye Fall ya nuna godiya ga taimako da goyon baya da kasar Sin ta samar wa Senegal. Ya bayyana cewa, sojojin kasashen biyu suna daukar nauyin tsaron kasa da ba da taimako ga bunkasuwar tattalin arziki da sa kaimi ga tsaron yankuna da kasa da kasa. Bangaren sojojin kasar Senegal yana son ci gaba da kara yin hadin gwiwa tare da sojojin kasar Sin, don kara fahimtar juna da amincewa juna, da ba da gudumawa ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.(Abubakar)

