A ran 19 ga wata a birnin Beijing, wani jami'in ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasa ta kasar Sin Kui Yanwei ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan ci gaba da yin kokarin shiga aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. don ba da gudummawa wajen bunkasa aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
A ran nan, mista Kui Yanwei ya yi bayani kan yadda sojojin yantar da jama'ar kasar Sin suka yi aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. ga 'yan jaridu na Sin da na waje kimanin hamsin.Ya ce, tun da aka tura sojoji 'yan kallo guda biyar zuwa hukumar sa ido kan dakatar da bude wuta ta M.D.D. a shekarar 1990, Sin ta tura jami'ai da sojojin kiyaye zaman lafiya 14650 don shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya guda 18. A halin yanzu dai, jami'ai da sojoji 1956 suna gudanar da aiki a yankuna tara da hukumomin kiyaye zaman lafiya na M.D.D., kuma adadin sojojin da Sin ta tura zuwa ayyukan kiyaye zaman lafiya dake karkashin jagorancin M.D.D. ya yi yawa a cikin zaunannun kasashe na kwamitin sulhu.
Ban da haka kuma, an gabatar da cewa, tun kasar Sin ta shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na M.D.D., ta gina tare da gyara hanyoyin da tsawonsu ya kai kilomita fiye da dubu 8 da gadoji dari biyu ko fiye, kuma ta gano da kau da boma-bomai dubu 8 da dari 7, kana ta yi jigilar kayayyaki da nauyinsu ya kai ton sama da dubu 430, ban da wannan kuma, yawan mutane marasa lafiya da aka duba da yi musu jinya ya wuce dubu 60. Hakan ya ba da babbar gudummawa wajen sa kaimi kan warware rikici ta hanyar zaman lafiya da kiyaye kwanciyar hankali a yankuna, da kuma gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a wasu kasashe da abin ya shafa.(Asabe)

