
Zhou Yongkang ya ce, Sin tana son yin kokari tare da kasar Sudan wajen kara yin hadin gwiwa don inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu. Zhou Yongkang ya nuna yabo ga jama'ar kasar Sudan da suka yi kokari wajen kiyaye ikon mallakar kasar da cikakken yankin kasar da kuma sa kaimi ga samun sulhuntawa tsakanin kabilu, kana yana fatan kasar Sudan za ta ci gaba da gudanar da yarjejeniyar samun zaman lafiya a dukkan fannoni don samun hadin kai da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwa.
Al-Bashir ya ce, kasar Sin amintacciyar abokiya ce ta kasar Sudan, hadin gwiwarsu ya kawo wa kasar Sudan man fetur da kuma zaman lafiya, kasar Sudan tana son kara hadin gwiwa kan raya aikin gona tare da kasar Sin. Kuma ya nuna yabo ga kasar Sin da ta ba da gudummawa wajen raya kasashen Afirka, da nuna godiya ga kasar Sin da ta nuna goyon baya ga kasar Sudan da ta kiyaye kwanciyar hankali da hadin kai, kana ya bayyana cewa, za a gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kungoyoyi daban daban don samun sulhuntawa tsakanin kabilu.(Zainab)

