in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen warware batun Darfur
2009-11-19 09:30:58 cri
A ran 18 ga wata a birnin Doha na kasar Qatar, an gudanar da taron shawarwari kan yadda za a shimfida zaman lafiya a yankin Darfur. Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da batun Darfur Liu Guijin ya yi wani jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen warware batun Darfur.

Liu Guijin ya jaddada cewa, Sin ta sa lura kan batun Darfur sosai, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen warware batun. Sin ta nuna goyon baya da shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur, wadda ta kasance kasa ta farko a waje da nahiyar Afirka da ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa yankin Darfur don gudanar da aiki. Ya nuna cewa, Sin ta dora muhimmanci kan ba da taimako ga yankin Darfur wajen bunkasa tattalin arziki da kuma kyautata halin jin kai, ya zuwa yanzu, ta riga ta samar da kayayyakin gudummawa da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan 160 ga wannan yanki. Liu Guijin ya bayyana cewa, Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da bangarori daban daban da abin ya shafa don warware batun Darfur tun da wuri.

Ban da wannan, shugaban kwamitin kungiyar AU Jean Ping ya bayyana cewa a wajen taron shawarwari tsakanin kungiyoyin fararen hula na yankin Darfur, shigar kungiyoyin za ta yi babban tasiri ga bangarorin daban daban da suke yaki da juna a yankin wajen samun sulhuntawa.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China