in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Unguwar raya tattalin arziki da fasaha ta Beijing tana taimakawa masana'antun da ke ciki wajen tinkarar rikicin kudi
2009-11-16 10:18:25 cri

Unguwar raya tattalin arziki da fasaha ta Beijing wadda ke kudancin birnin Beijing ita ce unguwar raya tattalin arziki da fasaha daya tak da ke matsayin kasa a nan birnin Beijing, wadda ke kunshe da masana'antu da kamfanoni fiye da dubu 2 da dari 6, ciki har da masana'antu da kamfanoni 66 da suka fito daga masana'antu da kamfanoni 500 mafi girma a duniya. Wadannan masana'antu da kamfanoni sun zo ne daga kasashe da yankuna fiye da 30. Jimillar kudaden da masana'antu da kamfanoni suka zuba a cikin wannan unguwa ta riga ta kai dalar Amurka fiye da biliyan 20. Sabili da haka, wannan unguwa ta zama wurin da ke bayyana yadda tattalin arzikin birnin Beijing, har ma na kasar Sin yake ciki. Tun kashi na 2 na shekarar bara, wasu masana'antu da kamfanonin da ke cikin wannan unguwa sun gamu da illa sakamakon afkuwar rikicin hada-hadar kudi a duniya. Sabo da haka, gwamnatin da ke kula da wannan unguwa ta tsara manufofi da dama domin taimakawa masana'antu ta yadda za su samu saukin matsalar. Mr. Zhao Xinxin, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin unguwar raya tattalin arziki da fasaha ta Beijing ya ce, "Rikicin hada-hadar kudi na duniya ya kawo illa sosai ga tattalin arziki. Unguwar raya tattalin arziki da fasaha ta Beijing wadda ke hada kan kasuwannin duniya sosai ita ma ta gamu da illa, musamman tun daga karshen watanni 3 na shekarar bara zuwa karshen farkon watanni 3 na bana, an gano irin wannan illa ne a bayyane. Muhimmin dalilin da ya sa aka iya gano haka shi ne bayan afkuwar rikicin hada-hadar kudi, bukatun da ke da su a kasuwannin duniya sun ragu sosai. Amma ka sani, yawan kayayyakin da ake fitarwa ya yi yawa a cikin dukkan kayayyakin da ake samarwa a unguwarmu."

Mr. Zhao Xinxin ya kara da cewa, tun daga karshen shekara ta 2008, kusan dukkan masana'antu da kamfanoni 2600 da ke unguwar sun gamu da illa sakamakon rikicin hada-hadar kudi na duniya. Daga cikinsu, yawan masana'antu da kamfanonin da suka gamu da illa mai tsanani ya kai kusan dari 2. Amma, ba a samu al'amarin rufe masana'antu ko rage yawan 'yan kwadago da aka dauka ba.

Kamfanin Zhongxin International da hedkwatarsa yake birnin Shanghai babban kamfani ne daga cikin masana'antu da kamfanonin da suke gaba wajen shiga unguwar. Wannan kamfanin da ke neman ci gaba bisa kasuwannin ketare ya gamu da illa sosai sakamakon rikicin hada-hadar kudi na duniya. Amma, har yanzu bai sallami ma'aikaci ko guda ba. Madam Xia Ying wadda ke aiki a wannan kamfani na Zhongxin International ta gaya mana cewa, "Kamfaninmu Zhongxin International yana tsayawa tsayin daka kan matsayin cewa ba zai sallami ma'aikaci ko guda ba, kuma zai kula da ma'aikata har a karshen lokacin illa. Sabo da haka, gwamnatin da ke kula da unguwar raya tattalin arziki da fasaha ta Beijing ta samar mana da kudin tallafi da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 8 da dubu dari 6 domin tabbatar da guraban aikin yi. Sakamakon haka, ta karfafa gwiwarmu sosai."

Samar da kudin talllafi ga masana'antun da ke unguwar hanya ce da gwamnatin da ke kula da unguwar take bi domin taimaka musu wajen tinkarar matsalolin da suke fuskanta. A waje daya, kwamitin kula da harkokin unguwar raya tattalin arziki ta Beijing ya dauki matakai masu amfani iri daban daban a kokarin taimakawa masana'antu da kamfanonin da ke unguwar, alal misali, ya kyautata tsarin ba da hidima da na aiwatar da harkokin unguwar da kuma samar da ayyukan yau da kullum masu inganci da kiyaye yanayin unguwar. Bugu da kari kuma, ya taimaki masana'antu da kamfanonin da ke unguwar a fannin sha'anin kudi da dai sauransu.

Bisa kokarin da kwamitin kula da harkokin unguwar raya tattalin arziki ta Beijing ya yi, masana'antu da kamfanoni sun samu imani da fatan alheri ga makomarsu. Madam Xia Ying ta kamfani na Zhongxin International ta ce, "A cikin gasar tattalin arziki, wata masana'anta ita kadai ta kan ji ana raba ta da sauran takwarorinta, kuma a kullum tana tsammani ba za a iya taimakawarta ba lokacin da take fama da hadarurruka, kuma ba ta san makomarta ba. A lokacin da take cikin irin wannan hali, idan gwamnati ta fito ta taimake ta, za ta iya karfafa gwiwar masana'antu. Kuma za a iya taka rawa sosai ga kokarin tabbatar da guraban aikin yi da samun farfado da tattalin arzikin masana'antu bayan rikicin hada-hadar kudi."

Madam Xia Ying ta gaya wa wakilinmu cewa, yanzu kamfanin Zhongxin International yana kokarin fita daga mawuyacin hali sannu a hankali. A shekara mai zuwa, da fatan tattalin arzikinsa zai koma yanayin da yake ciki kafin afkuwar rikicin hada-hadar kudi na duniya.

Ya kasance tamkar wani muhimmin wurin da ke tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya, ko shakka babu, unguwar raya tattalin arzikin Beijing ta ci jarrabawar wannan rikici. Yanzu masana'antun da ke unguwar sun soma samun farfadowa, har wasu daga cikinsu sun soma samun ci gaba. Game da makomar unguwar, Mr. Zhao Xinxin, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin unguwar raya tattalin arziki da fasaha ta Beijing ya nuna imani da cewar, "Ya zuwa yanzu, a bayyane ne masana'antun da ke unguwarmu suna kan gaba da masana'antu na kasashen waje game da batun samun farfadowa. Yanzu muna iya fadi cewa, masana'antun da ke unguwarmu, musamman masana'antun da suka fi haduwa da illar rikicin hada-hadar kudi na duniya sun riga sun soma samun farfadowa, kuma suna kokarin komawa halin da suke ciki kafin afkuwar rikicin hada-hadar kudi. A ganina, ya zuwa karshen shekarar da ake ciki, masana'antun da ke unguwarmu za su samu ci gaba, har ma za su wuce halin da suke ciki yau shekara daya da ta gabata."

Bisa sabuwar kididdigar da unguwar raya tattalin arziki ta Beijing ta bayar kwanan baya, yawan kudin da masana'antun dake unguwar suka samar tun daga watan Afrilu zuwa watan Yuni na shekarar da ake ciki ya karu da kashi 12.6 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Yawan harajin da aka samu a farkon rabin shekarar da ake ciki ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 8.2. Sabo da haka, yanzu tattalin arzikin unguwar yana samun ci gaba kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China