in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da "Sanarwar Singapore" a yayin taron koli na APEC
2009-11-15 18:26:00 cri
Bisa "Sanarwar Singapore" da aka bayar a gun kwarya-kwaryar taron shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pacific, wato APEC a ran 15 ga wata, an ce, ba za a canja burin da mambobin kungiyar APEC suke son cimmawa ba, wato za a yi kokarin karuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin yankunan Asiya da na tekun Pacific ta hanyar bude kofa a fannin yin cinikayya da zuba jari.

Cikakken taken wannan sanawa shi ne "Ci gaban tattalin arziki mai dorewa da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakanin shiyya-shiyya ----Sanarwar kwarya-kwaryar taron shugabannin mambobin kungiyar APEC a karo na 17". A gun bikin sanar da wannan sanarwa, Mr. lee Hsien Loong, firayin ministan kasar Singapore, kuma masaukin wannan kwarya-kwaryar taro ya ce, yankin Asiya da na tekun Pacific yana kan gaba wajen farfadowa da tattalin arzikin duk duniya, amma ba a iya komawa sabuwar hanyar neman ci gaban tattalin arziki da ake sabawa ba, mambobin kungiyar APEC suna bukatar sabon shirin karuwar tattalin arziki, wato neman ci gaba cikin daidaito da amincewa da juna da kuma ba tare da tangarda ba. Irin wannan hanya za ta iya tabbatar da ganin an farfado da tattalin arziki cikin dogon lokaci da samar da karin guraban aikin yi da kuma kawo moriya ga jama'a.

Wannan sanarwa ta kuma nuna cewa, mambobin kungiyar APEC za ta ci gaba da daukar kwararan matakan sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki har a tabbatar da farfadowa da tattalin arziki mai dorewa a bayyane.

Game da tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, wannan sanarwa ta nuna cewa, shugabannin mambobin kungiyar APEC sun jaddada cewa, za a sa kaimi ga kammala zagaye na Doha na shawarwarin da kungiyar WTO ta shirya a shekara ta 2010, kuma za a iya samun sakamako. Bugu da kari kuma, za a yi kokarin cimma burin da aka yi a Bogor, kuma za a kara saurin raya tattalin arzikin yankunan Asiya da na tekun Pacific bai daya.

Haka kuma, a cikin wannan sanarwa, an sanya kokarin tinkarar kalubalen samar da isashen abinci a gaban kalubalolin da kungiyar APEC ke fama da su, kuma an yi alkawarin kyautata tsarin kiwon lafiya domin kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin rigakafi da kuma shawo kan sabbin ciwace-ciwacen da suke annoba a duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China