in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin yabawa mutanen da suka bayar da gudummawa wajen sada zumunci a tsakanin Sin da kasashen Afirka
2009-11-12 17:06:17 cri
A ran 12 ga wata, kungiyar kasar Sin ta sada zumunta a tsakanin jama'arta da ta kasashen waje da kungiyar kasar Sin ta sada zumunta a tsakanin jama'arta da kasashen Afirka sun shirya bikin yabawa nagartattun mutane 15 na kasar Sin da na kasashen Afirka, ciki har da shugaban farko na kasar Zambiya Kenneth Kaunda da Mr. Salim Ahmed Salim, tsohon babban sakataren kungiyar hada kan kasashen Afirka wadanda suka bayar da gudummawa sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a karo na biyu.

Lokacin da yake ganawa da wakilinmu a gun bikin, dattijo Kaunda ya ce, wannan biki ne da aka shirya domin kara sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Mr. Kaunda ya ce, "Wannan kyakkyawan al'amari ne da ke bayyana kaunar da ke kasancewa a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Yanzu muna yin abubuwa da yawa, wannan al'amari na daya daga cikin manyan bukukuwa. Wadannan manyan bukukuwa su ne taya murnar al'amuran da suke faruwa a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, wato zumuncin da ke kasancewa a tsakaninsu."

Mr. Liu Hongwu wanda ya dade yana nazarin harkokin da ska shafi Afirka, kuma yana horar da kwararru masu nazarin Afirka, ya kuma zama daya daga cikin Sinawa 10 da suka girgiza jama'ar kasashen Afirka. Bayan da ya samu wannan yabo, shehun malami Liu Hongwu ya ce, "Yanzu gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da jerin tsare-tsaren raya huldar a tsakaninta da kasashen Afirka, kuma tana samun kyawawan sakamako sosai. A cikin dukkan kasashen duniya, ba wata kasa dake da cikakken tsari da manufofin raya hulda a tsakaninta da kasashen Afirka kamar kasar Sin. Muna da 'shirin raya hulda a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na shekaru uku-uku'. Sannan matakai 8 da kasar Sin ta dauka a Afirka a cikin shekaru 3 da suka gabata sun kuma samu kyakkyawan sakamako. Ina da imani cewa, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka za ta kai wani sabon mataki a cikin shekaru 3 masu zuwa."

Haka kuma, Mr. Abdul'ahat Abdulrixit, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma shugaban kungiyar kasar Sin ta sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta kasashen Afirka ya gaya wa wakilinmu cewa, "Dalilin da ya sa aka yabawa nagartattun mutanen da suka bayar da gudummawa sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a karo na biyu shi ne kara sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannoni daban daban. Ba ma kawai muna yaba wa Sinawa wadanda suka dade suna aiki a Afirka, kuma suka bayar da gudummawarsu sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannoni daban daban ba, har ma muna yaba wa abokanmu, wasu nagartattun mutanen Afirka, kamar dattijo Kenneth Kaunda wadanda suka bayar da gudummawa sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Sabo da haka, a ganina, irin wannan yabo yana da muhimmiyar ma'ana wajen kara raya huldar sada zumunci a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka."

Kungiyar kasar Sin ta sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta kasashen waje ita ce ta kafa dan bar ba da irin wannan lamba a shekara ta 2006. Tun daga shekara ta 2006, ana zabo wasu nagartattun Sinawa da mutanen kasashen Afirka wadanda suka bayar da gudummawarsu sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a kowadanne shekaru uku-uku.

Ban da dattijo Kenneth Kaunda na kasar Zambiya da Mr. Salim Ahmed Salim na kasar Tanzaniya, sauran nagartattun mutanen Afirka uku da suka samu wannan yabo su ne, Mr. Yusuf Wali, shugaban kungiyar kasar Masar ta sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Masar da ta kasar Sin, kuma tsohon mataimakin firayin ministan kasar Masar da Mr. Alfred Sesay, shugaban kungiyar kasar Saliyo ta sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Saliyo da ta kasar Sin kuma tsohon ministan albarkatun kasa na kasar Saliyo da Mr. Vital Balla, shugaban kungiyar kasar Congo Brazaville ta sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Congo Brazaville da ta sauran kasashen duniya, kuma shugaban kungiyar hada kan hukumomi da ba na gwamnati ba na kasar Congo Brazaville. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China