in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2009-11-11 18:34:34 cri

A ran 9 ga wata an yi taron kasa da kasa kan kasuwannin yawon shakatawa na shekarar 2009, wato WTM, inda aka bayar da wani rahoto da ke cewa, rikicin kudi na duniya ya kawo babbar illa ga sha'anin yawon shakatawa a duk duniya, yawan kudin shiga da ake samu daga sha'anin yawon shakatawa ya ragu da kashi 40 daga cikin dari a watan Yuli na shekarar 2009, idan aka kwatanta shi da na watanni 12 kafin watan Yuli na bana, ko da yake haka ne, amma nahiyar Afirka ta zama daya daga cikin yankunan da suka fi samun karuwar yawon shakatawa daga kasashen waje a shekarar 2008, wanda ya karu da kashi 3 daga cikin dari sakamakon karuwar zuba jari da kyautata ingancin ma'aunin yawon shakatawa.

Rahoton ya ce, ziyarar shugaban kasar Amurka Barack Obama a kasar Ghana a 'yan watanni baya ba kawai ta mayar da nahiyar Afirka a wani matsayi mai muhimmanci a sha'anin yawon shakatawa na duk duniya ba, har ma ta sanar da babban boyayyen karfi ga 'yan asalin Afirka da suke zama a ketare domin su yi yawon shakatawa a kasahen Afirka.

A cikin rahoto, an fadi cewa, rikicin kudi na duniya ya kawo raguwar kudaden da jama'a kan kashe, da karuwar jama'a da suka rasa ayyukan yi, wadanda suka kawo babbar illa ga sha'anin yawon shakatawa. Sakamakon haka, yawan masu yawon shakatawa a kasa da kasa ya ragu da kashi 8 daga cikin dari, yawan kudaden shiga da otel-otel suke samu ya ragu da kashi 16 daga cikin dari, yawan kudaden shiga da hukumomin jiragen sama suka samu ya kai kashi 14 daga cikin dari. Hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta duniya wato IATA ta yi hasashen cewa, yawan hasarar kudin da hukumomin jiragen sama suka yi zai kai kudin Amurka dala biliyan 11 a shekarar 2009. Sabo da haka, sai zuwa shekarar 2013 ne, za a iya maido da sha'anin yawon shakata kan matsayinsa na lokacin kafin rikicin kudi na duniya.

Rahoton ya ci gaba da cewa, ya kamata a fi mai da hankali sosai a halin yanzu kan taron tinkarar sauyawar yanayi na MDD da za a yi a watan Disamba na shekarar da muke ciki, ta yadda za a bude wata sabuwar hanya da za a bi irin ta rage hayakin da ake fitarwa wajen samun sababbin masu yawon shakatawa.

Ban da wannan kuma, rahoton ya ce, yanzu ba a san yawon shakatawa irin na neman asalinsa sosai ba kamar Obama ya yi a Afirka, wato 'yan Afirka da dama suna zama a ketare, wasu daga cikin su sun je ketare sakamakon cinikin bay. To, wadannan jama'a suna da bukatar yawon shakatawa da neman asalinsu a Afirka, wannan zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka. A ganin rahoto, yawon shakatawa irin na neman asali zai iya kara kyautata siffar nahiyar Afirka a fannin yawon shakatawa, sabo da Obama ya zama wani wakili mai kyau, babu wani lokaci da ya fi yanzu kyau wajen yin farfagandar yawon shakatawar kasashen Afirka.

A ganin wannan rahoto da aka gabatar a gun taron duniya kan kasuwannin yawon shakatawa na shekarar 2009, wato WTM, an ce, ya fi muhimmanci ga kasashen Afirka su samu zaman karko kamar kasar Ghana, wadda ta zama kasa ta farko da ta karbi shugaban kasar Amurka Obama, yayin da ya kai ziyarar aiki a Afrika. Shafunan internet kuma sun taimaka wajen kara sani da fahimtar kasashen Afirka.

An ce, a yayin da Obama ya ci nasara a babban zaben shugaban kasar Amurka, jama'a sun fara mai da hankali sosai kan kasar Kenya, wadda ta zama asalin Obama, 'yan Afirka da dama da suke zama a kasar Amurka suna son kai ziyara da yawon shakatawa a kauyen Kogelo, asalin Obama, inda kakar Obama take zama a halin yanzu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China