in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Dokar motsa jiki" ta sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin motsa jiki a kasar Sin
2009-11-11 18:43:46 cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fid da wata doka ta musamman ga duk daukacin jama'ar kasar Sin game da motsa jiki wato "dokar motsa jiki", wannan doka doka ta farko ce da aka fid da kan batun motsa jiki a kasar Sin, kuma ta riga ta fara aiki daga ran 1 ga watan Oktoba na bana wato shekarar 2009 da muke ciki. To, ina dalilin da ya sa aka fid da wannan doka? Kuma ina ma'anarta? A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

"Dokar motsa jiki" tana hade da kashi shida, kuma tana hade da fannoni arba'in, makasudin fid da wannan doka shi ne domin kare hakkin halal na 'yan asalin kasar Sin yayin da suke motsa jiki, tana da babban amfani ga sha'anin motsa jiki na duk daukacin jama'ar kasar Sin. Kan wannan batu, shugaban babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin Liu Peng ya yi mana bayani a gun wani taron watsa labaran da aka shirya musamman ma domin yin farfaganda kan wannan doka a ran 7 ga watan Satumba na bana cewa,  "Wannan dokar motsa jiki ta dauki hakikanan matakai don warware matsalolin dake kayyade bunkasuwar sha'anin motsa jiki a kasar Sin. To, ina matsala mafi tsanani dake kasancewa a gabanmu? Mun yi bincike mun yi nazari, kuma mun tarar da cewa, kawo yanzu, bukatun motsa jiki na jama'ar kasar Sin suna kara karuwa a kwana a tashi, amma albarkatan wasannin motsa jikin da zamantakewar al'ummar kasar Sin ke iya samar mana ba su karu ba kamar yadda ya kamata. A sabili da haka, don kawar da wannan sabani, wannan doka ta tanadi cewa, dole ne a shigar da sha'anin motsa jiki a cikin shirin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma na kananan gwamnatoci na mataki daban daban. A daya wajen kuma, dole ne a shigar da kudin da ake bukata kan sha'anin motsa jiki a cikin kasafin kudi na kananan gwamnatoci na mataki daban daban. Ban da wannan kuma, za a kara zuba jari ga wannan sha'anin ta yadda za a ciyar da babban sha'anin gaba yadda ya kamata. A sa'i daya kuma, wannan doka ita ma ta tanadi cewa, za a kara yin amfani da dukkan dakuna da cibiyoyi na wasannin motsa jiki, musamman ma ga jama'ar kasar Sin ba 'yan wasa ba."

Tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin wato bayan shekaru talatin da suka gabata, sha'anin motsa jiki na jama'ar kasar Sin ya sami ci gaba a bayyane, ingancin lafiyar jikin jama'ar kasar Sin shi ma ya sami kyautatuwa a kai a kai. Amma yawan jama'ar kasar Sin ya riga ya zarce miliyan dari daya da talatin, ko a birane, ko a kauyuka, babu isasshen gine-ginen wasannin motsa jiki na jama'a, wannan ya kawo tasiri ga bunkasuwar sha'anin motsa jiki na duk daukacin jama'ar kasar Sin. Game da wannan, "dokar motsa jiki" da ta fara aiki ba da dadewa ba ta tanadi cewa, kamata ya yi kananan gwamnatoci na mataki daban daban su kara samar da abubuwan wasannin motsa jiki bisa shiri. Ban da wannan kuma, an tanadi cewa, dole ne a samar da abubuwan motsa jiki a cikin unguwannin gidajen kwana na mazauna birane, da haka, za su iya motsa jiki a koda yaushe kuma kamar yadda suke so.

Kan batun kudin da ake bukata, mataimakiyar shugaban babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin madam Xiao Min ta yi mana bayani cewa, "Wannan doka ta tanadi cewa, za a samu kudin da ake bukata daga taimakon gwamnati, ban da wannan kuma, ana iya samu daga kudin moriyar jama'ar da aka samu ta hanyar sayar da tikitin caca na wasannin motsa jiki."

Sha'anin tikitin caca na wasannin motsa jiki na kasar Sin ya fara ne daga shekarar 1994, kawo yanzu, shekaru goma sha biyar sun wuce, kuma ya riga ya samu ci gaba bisa babban mataki. A shekarar 2008, jimlar kudin da aka samu daga wajen sayar da tikitin caca na wasannin motsa jiki a kasar Sin ta kai kudin Sin Yuan biliyan 45 da miliyan dari shida. Bisa shirin da aka fid da, kullum za a kebe kashi 30 cikin dari na kudin da aka samu da ya zama kudin moriyar jama'a, daga baya kuma za a kebe kashi 60 cikin dari na kudin moriyar jama'a da ya zama kudin motsa jiki na jama'ar kasar Sin. Saura kashi 40 cikin dari kuwa, za a yi amfani da shi kan sha'anin wasannin Olympic. Tun daga shekarar 1996, kasar Sin ta riga ta kashe kudin Sin Yuan biliyan 8 kan sha'anin motsa jiki na jama'ar kasa, alal misali, gyara da gina gine-ginen motsa jiki, da kuma ba da taimako ga wuraren da ba su samu ci gaba sosai ba a fannin wasannin motsa jiki.

"Dokar motsa jiki" ta tanadi cewa, ya kamata a yi amfani da kudin moriyar jama'a na tikitin cacar wasannin motsa jiki kan sha'anin motsa jiki na duk daukacin jama'ar kasar Sin bisa ka'idodin da abin ya shafa. Madam Xiao Min ta gaya mana cewa,  "Tun daga shekarar 1994, kudin moriyar jama'ar da aka samu daga wajen tikitin cacar wasannin motsa jiki ya ba da babbar gudummawa ga ayyukan kara karfafa gine-ginen wasannin motsa jiki da kafuwar kungiyoyin wasannin motsa jiki na farar hula da kara ingiza aikin motsa jiki na duk daukacin jama'ar kasar Sin da sauransu."

Kazalika, wannan dokar motsa jiki ta tanada a fili cewa, dole ne a kiyaye ikon halal na 'yan asalin kasar Sin yayin da suke motsa jiki. A karo na farko ne aka buga irin wannan bayani a cikin doka a kasar Sin. Wannan doka ita ma ta jaddada cewa, kamata ya yi kananan gwamnatoci na mataki daban daban na kasar Sin su dauki hakki bisa wuyansu kuma su kara mai da hankali kan wannan sha'ani. Kuma kamata ya yi su yi kokarin shirya ayyukan gasar wasannin motsa jiki iri daban daban tsakanin jama'a da kuma samar musu jari da gine-gine da aikin hidima da sauransu.

A daya wajen kuma, wannan doka ta tanadi cewa, a kauyuka, a lokacin da ake taya murnar bikin gargajiya, ko a lokacin hutun noma, kamata ya yi hukumar kula da wasannin motsa jiki ta matsayin gunduma ta yi kokarin shirya ayyukan motsa jiki mai tsarin musamman na manoma; a birane, hukumomin gwamnati da kamfanoni su bukaci ma'aikatansu da su motsa jiki a lokacin hutu a kowace rana.

Abu mafi faranta ran mutane shi ne wannan doka ta tanadi cewa, dole ne daliban dake cikin makarantu su yi awa daya domin motsa jiki a kowace rana. Game da wannan, iyalan dalibai sun nuna fahimta da yabo. Direban tasi na birnin Beijing Liang Guping ya ce:"Yanzu dalibai suna shan karatu sosai, amma sun fi son motsa jiki, motsa jiki zai amfanawa lafiyar jikinsu."

Wannan doka ta tanadi cewa, za a mayar da ran 8 ga watan Agusta na kowace shekara a matsayin ranar motsa jiki ta jama'ar kasar Sin. (Jamila Zhou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China