Filin wasan kwallon raga na rairayin bakin teku domin wasan Olympic

A cikin kyakkaywan wurin yawon shakatawa na Chaoyang da ke nan birnin Beijing, akwai wani karamin tsibiri a tsakiyar tabki. A kansa kuma, an shimfida rairayi. Wato shi ne filin wasan kwallon raga na rairayin bakin teku da za a yi amfani da shi a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar gobe.

Filin wasan kwallon raga na rairayin bakin teku da ke wurin yawon shakatawa na Chaoyang na Beijing na matsayin filin wasa na wucin gadi domin taron wasannin Olympic. Ya hada da babban filin wasa guda daya da filayen wasan dumamar jiki guda 2 da kuma filayen wasa na horo guda 6. An samar da kujeru dubu 12 ga 'yan kallo. Kuma an shimfida rairayi mai nauyin ton dubu 17 ko fiye a cikin wannan filin wasan kwallon raga, wadanda aka yi jigilarsu daga bakin teku na tsibirin Hainandao na kasar Sin kai tsaye, a maimakon a kawo daga kasashen ketare. An fara gina wannan filin wasa a watan Disamba na shekarar 2005, aikin ginawa ya kawo karshe a watan Yuni na shekarar da muke ciki.

Gina filin wasan kwallon raga na taron wasannin Olympic na Beijing a kan karamin tsibirin da ke tsakiyar tabki na matsayin zayyana mafi ban sha'awa a idanun mutane, saboda ruwa na kewayen wannan filin wasan kwallon raga.

Girman wannan tsibiri ya kai misalin mita 300, kuma yana kewaye ne da ruwa, an hada shi da sauran wurare da kananan hanyoyi 2 a kudancinsa. Ana shuka kwarran tsire-tsire a bakin tsibirin, wadanda suka raba kyan karkara na tabkin daga birnin Beijing mai kara kwata-kwata. A cibiyar tsibirin, an gina babban filin wasa, sa'an nan kuma, an gina filayen wasa na horo a kan bakin tabkin da mutane suka shimfida a yammacin tsibirin. Gine-ginen gudanar da harkokin yau da kullum suna kasancewa a bakin tabkin da ke gabashin tsibirin, inda aka dasa bishiyoyi masu dimbin yawa. In wani ya hango daga nesa, to, babban filin wasa da sauran gine-ginen gudanar da harkokin yau da kullum suna kasancewa tamkar kwallon raga ya yi karo da yatsar hannun mutum.

A sakamakon matsayin filin wasa na wucin gadi, shi ya sa bayan taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, za a rushe filin wasan kwallon raga da ke wurin yawon shakatawa na Chaoyang na Beijing. Amma duk da haka, masu zayyana sun yi shirin musamman game da yin amfani da shi bayan gasa tukuna. Bayan taron wasannin Olympic na Beijing, za a kashe kudade kalilan wajen bunkasa wannan filin wasan kwallon raga da gine-ginen da ke dab da shi zuwa wurin yawon shakatawa kan ruwa bisa wuraren da suke kasancewa da kuma halin da suke ciki.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


Adireshi da Tel

Adireshi: 7 Madian South Road, Haidian District, Beijing

Tel: 8610--62019208

Lokacin budewa: 8:30 am zuwa 5:30 pm a kullun

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040