Filin wasan kwallo na zamani wato softball na Fengtai da ke birnin Beijing

Filin wasan kwallo na zamani na softball na Fengtai da ke kudancin Beijing filin wasa ne na farko a nan Beijing da aka kammala ginawa da kuma fara aiki da shi don taron wasannin Olympic na shekara mai zuwa.

Fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 15 ko fiye. Akwai kujeru din din din dubu 4 da dari 7 da kuma na wucin gadi dubu 5 a cikin babban filin wasa, sa'an nan kuma, akwai kujerun wucin gadi 3500 a cikin filin wasa na ko-ta-kwana, ta haka 'yan kallo fiye da dubu 13 na iya kallon gasar wasanni a nan. Wannan filin wasa na hade da babban filin wasa da filin wasa na ko-ta-kwana da filayen horo guda 2 da dakin gudanar da ayyuka da hanyoyi da wuraren ajiye motoci da filayen ciyayi da kuma wasu na'urorin jama'a na wucin gadi.

Bayan da aka gama gina shi ba da jimawa ba, filin wasan kwallo na zamani na softball na Fengtai ya sami damar bakuncin gasar fid da gwani ta wasan kwallo na zamani na softball ta mata ta duniya a karo na 11. A lokacin gasar, ingancin wannan filin wasa ya sami babban yabo daga Hadaddiyar kungiyar wasan kwallo na zamani na softball ta kasa da kasa da 'yan wasa da malaman horas da wasanni da kuma alkalin wasa. Shugaba Don E. Porter Hadaddiyar kungiyar wasan kwallo na zamani na softball ta duniya ya yi wannan bayani a gun babban taron kwamitin gudanarwa ta kungiyar da sauran wurare da yawa cewar, mai yiwuwa ne filin wasan kwallo na zamani na softball na Fengtai zai kasance mafi kyau a tarihin wasan kwallo na zamani na softball.(music)

Don gina wani filin wasan Olympic na zamani na matsyin koli, masu gina filin wasan kwallo na zamani na softball na Fengtai sun sha yin dabara.

Jar kasa da ke cikin filin wasan kwallo na zamani na softball na da muhimmanci sosai. Saboda 'yan wasa da kan zame a cikin gasar wasanni, shi ya sa kada jar kasa ta yi yauki sosai, kada kuwa ta yi tauri sosai, ta kasance cike da rabin rairayi. Don haka, an kashe kudin Sin yuan miliyan 2 domin sayen jar kasa daga kudancin kasar Sin, an shimfida shi a filayen horo na filin wasan kwallo na zamani na softball na Fengtai. Jar kasa da ke cikin babban filin wasa da filayen wasan na ko-ta-kwana ne aka sayo daga ketare.

Ko da yake an kashe dimbin kudi wajen sayen jar kasa, amma an yi tsimin kudi a fannoni da yawa a wannan filin wasa. Ana amfani da fitilu da kayayyakin wanka irin na tsimin makamashi a wannan filin wasa, sa'an nan kuma, ana amfani da hasken rana wajen samar da ruwa mai zafi a filin wasan, ta haka an yi tsimin dimbin makamashi.

Dadin dadawa kuma, filayen ciyayi da aka shimfida a wannan filin wasa na iya shan ruwan sama cikin sauri, ta haka, bayan awa daya da aka dauke ruwa, za a iya yin gasa. Ta hanyar bututun da ke karkashin filayen ciyayi ne aka tattara ruwan sama, an iya sake amfani da ruwa.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


 

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040