Wannan masallaci an fara gina shi ne a karshen zamanin daular Ming, sannan kuma aka sake gina shi a zamanin mulkin Kangxi na daular Qing.
A shekarar 2004 ne aka yi masa kwaskwarima tare da fadada shi amma ba tare da canza tsohon fasalinsa ba na gargajiya.
Sabon masallacin a halin yanzu yana da fadin murabba'in mita 2,800, yayin da fadin filin da aka yi gine gine na harabar masallacin ya kai fadin murabba'in mita 4,000. Yana da kyakkyawar haraba da kuma kayayyakin amfani na zamani. Babban zauren da ake ibada dake tsakiyar harabar masallacin yana iya daukar mutane sama da dari da hamsin a lokaci guda. |