Dakin abinci na Kaorou Wan dakin abinci ne mai dadewa da ya yi suna wajen dafa abincin musulmai a nan birnin Beijing. Mutane da yawa su kan tafi wannan dakin abinci domin cin naman da aka gasa a wannan dakin abinci.
Dakin abinci na Kaorou Wan yana mai da hankali wajen zabar naman da za a gasa. Nauyin shannun da yake zaba ya kai fiye da kilo dari 1 da hamsin da aka kiwo a wani wurin musamman, shekarun haihuwa ya kai tsakanin 4 da 5. Ana gasa nama ne da kiraren itatuwan pine da dabino da pear. Kaurin naman da aka fere ya kai kimanin milimita 6. A lokacin da ake gasa nama, ana amfani da man ridi da soyan sauce da man shrink da giyar girki da ruwan citta da sugar da ka-fi-zabo, sabo da haka, irin wannan naman da aka gasa tana da kyamshi sosai lokacin da ake ci.
Ban da naman da ake gasa, ana kuma dafa miyan musulmai da gasassiyar agwagwa ta Beijing. |