Masallacin DONGSI

Wannan masallaci na Dongsi, an gina shi ne a shekarar 1447 a gundumar gabashin Beijing. Ya kunshi zauren yin sallah da kuma zaurukan yin wa'azi guda biyu, wato zauren kudu da zauren yamma. Sannan kuma akwai ginin dakin karatu da dakin kayan amfanin yau da kullun da yake fuskantar yammaci. An yi rubutun ayoyin al Qur'ani a fuskar wadannan zauruka guda ukku na wannan masallaci.

Babban zauren yin sallah na wannan masallaci yana iya daukar masallata dari biyar a lokaci guda. Akwai muhimman kayan tarihi na musulunci a wannan masallaci. Daga ciki kuwa akwai wani tsohon al Qur'ani mai girma wanda yana daya daga cikin tsaffin al Qur'anai na kasar Sin.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


Adireshi da Tel

Adireshi: No.13, Dongsi ta kudu, gundumar Dongcheng, Beijing

Tel: 8610--65257824

Lokutan budewa: 8:30 na safe zuwa 5:30 na yamma a kullun

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040