Dakin cin abinci na KAOROU JI

A cikin harshen Sinanci, ma'anar "kao rou" ita ce "gasassiyar nama", "Ji" sunan kakanin-kakanin ne na wani mutum. Yau da shekaru da yawa da suka gabata, wato lokacin da ake mulkin Daoguang da Xianfeng na daular Qing a nan kasar Sin, wani mutumin da ake kiran shi Ji Decai da ya yi zama a karkarar gundumar Tongzhou da ke gabashin birnin Beijing ya yi kokari sosai wajen neman kudi domin renon iyalansa. A lokacin da ya kai shekaru 20 da wani abu da haihuwa, ya kan tuka wani karamin keken da ke da taya guda kawai ya shiga cikin birnin Beijing a kowane loakcin zafi ya gasa naman akuya da shannu, kuma ya sayar da su a wani wurin da ke arewacin birnin Beijing domin neman kudin zaman rayuwa. Domin naman da ya gasa yana da dadin ci kwarai, mazauna birnin Beijing sun ba shi suna "Kaorou Ji". Ji Decai da dansa Ji Zongbin dukkansu mutanen kirki ne, ba su cuci tsoffi da yara, balle ma sauran mutane. Sabo da haka, an kaunarsu da naman da suka gasa sosai.

Yanzu "Kaorou Ji" wani babban dakin abinci ne da ya yi suna sosai a nan birnin Beijing.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


Adireshi da Tel

Adireshi: No.14, gabar gabas ta Qianhai dake kan titin Di'anmenwai, gundumar Xicheng, Beijing

Tel: 8610?64042554, 64045921

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040