Masallacin NIUJIE

Wannan masallaci shi ne mafi dadewa, kuma mafi girma a Beijing, sannan kuma masallacin da ya fi yin fice a kasar Sin. Wannan masallaci yana iya daukar masallata sama da dubu daya a lokaci guda. A shekarar 996 ne aka gina wannan masallaci, kuma yana da dogon tarihi na sama da shekaru dubu daya, sabo da haka ya kasance muhimmin wurin tarihi da gwamnati ke ba shi kariya.

Masallacin ya kunshi babban gini na yin ibada da sauran gine-gine a cikinsa. Babban ginin zauren yin sallah na wannan masallaci ya kunshi muhimman sigogo biyu. Na farko dai an yi amfani da tsarin yin gini na gargajiya na kasar Sin wajen gina masallacin, sannan aka yi amfani da salon ado na Larabawa domin yi wa masallacin kwalliya. Kuma yana iya daukar masallata dubu daya a lokaci guda. Har yanzu akwai mahimman kayan tarihi na musulunci wadanda aka yi rubutu a kansu a cikin wannan masallaci, dukkansu suna da amfani sosai wajen nazarin tarihin musulunci a kasar Sin. A shekarar 2005 an yi wa wannan masalaci kwaskwarima domin kyautata halin da masallacin ke ciki.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


Adireshi da Tel

Adireshi: No.88 Titin Niujie, gundumar Xuanwu, Beijing

Tel: 8010--63532564

Lokutan budewa: 8:30 na safe zuwa 5:30 na yamma a kullun

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040