logo

HAUSA

Babi18: Al'adu

2020-10-30 10:07:50 CRI

Babi18:Al'adu

>>[Bukukuwa]

Bikin barara na kasar Sin

Daidai kamar muhimmancin bikin kirsimati ga Turawa, bikin bazara ya zama biki mafi girma ga Sinawa daga cikin bukukuwan duk shekara. Ko da yake bisa sauye-sauyen zamani, aikace-aikacen da ake yi a gun bikin bazara suna ta canjawa, hanyoyin da mutanen ke bi don yin biki kuma suna ta canjawa, amma har ila yau matsayin bikin bazara da ke cikin zaman rayuwa da tunanin Sinawa ba za a iya yi mishi tashi-in-maye ba.

An ce, bikin bazara na kasar Sin yana da tarihin da ya shafe shekaru 4000, amma a farkon lokaci ba a kiransa bikin bazara, kuma ba a tsai da ranar bikin ba. Zuwa shekara ta 2000 da wani abu na kafin haifuwar Annabi Isa Alaihisallam, a wancan lokaci mutane sun dauki tsawon lokacin juyawar tauraron da ake kira Jupiter sau daya ta zama "Sui" daya, kuma akan kira bikin bazara da sunan "Sui". Kafin shekarar 1000 na kafin haifuwar annabi Isa Alaihisallam, mutane sun ba wa bikin bazara da sunan "Nian". A wancan lokaci kuwa, kalmar "Nian" tana da ma'anar samun amfanin gona mai armashi ne, idan an samu amfanin gona mai armashi, sai a ce "akwai babban Nian".

Bisa al'adar jama'ar kasar Sin, akan ce bikin bazara ya fara daga ran 23 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar, kuma ya dade har zuwa bikin Yuanxiao na ran 15 ga watan farko na sabuwar shekara, wato duk tsawon bikin ya kai wajen makonni 3. Cikin wannan lokaci, kwana daya da yini daya wato jajibirin sabuwar shekara na ran 30 ga watan Disamba da dare da ran 1 ga watan farko su ne suka fi kasaita, ana iya cewa su ne wani tashe na bikin bazara. Domin marabtar bikin bazara, daga birane zuwa kauyuka, mutane suna ta yin ayyuka daban-daban domin shirin bikin. A kauyuka, tun da aka shiga cikin watan Disamba na kalandar kasar Sin, sai a fara ayyukan share fage domin bikin, iyalan manoma da yawa sukan share daki, da wanke tufafi da barguna domin kau da rubabbun abubuwa ta yadda za a samu sabon halin zama. 'Yan iyali kuma sun yi ta sayen kayayyaki iri-iri daga kasuwa domin bikin bazara, kamar alewa da kayan zaki da nama da 'ya'yan itatuwa, ta yadda za su samu isashen abinci domin kansu kuma domin karbar baki a lokacin bikin. A manyan birane kuma, an fara ayyukan share fage tun tuni domin bikin, sassan al'adu da kungiyoyin 'yan fasaha sukan shirya wasanni da yawa masu ban sha'awa, gidajen rediyo mai hoto kuma sukan yi shirye-shirye iri daban-daban, ban da wannan kuma akan shirya baje-koli cikin manyan lambunan shan iska daban- daban, ta yadda mutane masu yawon shakatawa za su iya yin shagulgula masu nishadi wadanda yawansu ba a zo a gani ba ne, manyan kantuna kuma sukan yi odar hajjoji daga wurare daban- daban na duk kasa baki daya har ma daga kasashen waje domin biyan bukatun 'yan birni a gun bikin bazara. An taba yin kididdigar cewa, yawan kudin da Sinawa suka kashe domin sayen kayayyaki a lokacin bikin bazara ya kai sulusi har ma ya wuce haka bisa na duk shekarar.

A wurare daban-daban na kasar Sin, mutane suna da al'adun gargajiya iri daban-daban wajen yin bikin bazara, amma ko a arewaci ko kuma a kudancin kasar duk 'yan iyali sukan hadu don cin abinci tare a jajibirin bikin da dare, wannan ya zama wani wajibabbun abubuwa ne. A kudancin kasar, abincin nan yakan hada da nama da ganyaye wadanda yawan irinsu ya kai fiye da 10, daga cikinsu tilas ne da akwai irin abincin da ake kira Tofu wanda aka yi da wake, da kuma "Yu" wato kifi, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne sabo da kalmar "Fuyu" wadda lafazinta cikin Sinanci ya yi daidai da na kalmar "arziki". A arewancin kasar kuma, yawancin iyalai sukan ci irin abincin da ake kira Jiaozi a jabibiri da dare, 'yan iyali daya dukkansu suna yi Jiaozi tare, irin wannan abinci an yi shi ne ta hanyar kunsa daddatsattsen nama mai dadin ci cikin kullin garin alkama mai da'ira, kuma an dafa su cikin tafasassen ruwa, kuma an ci Jiaozi tare da kayan yaji, duk 'yan iyali suna zaune a kewayen tebur suna cin Jiaozi tare cikin halin annashuwa.

A jajibiri da dare, mutane sukan tsayawa ba su yi barci, suna yin wasanni iri-iri cikin murma da fara har duk dare, an yi haka ne domin wucewar tsohuwar shekara da shiga cikin sabuwar shekara. A da, a lokacin zuwan sabuwar shekara, mutane sukan harba wutar gimbiya domin murnar bikin. Ana bin wannan al'ada ce domin kaucewa miyagun shaidanu, amma domin samun kwanciyar hankali da kiyaye muhalli, an riga an hana yin haka a unguwoyin birnin Beijing da na wasu manyan birane daban. A safiyar rana ta farko ta sabuwar shekara, duk 'yan iyali manya da kanana sukan ci ado da tufaffin ranar biki, kuma sun fara karbar baki ko sun fita waje don yi wa mutane barka da sabuwar shekara. Lokacin da ake ganawa da juna, sukan ce "barka da sabuwar shekara", da "barka da bikin bazara" da sauran kalmomi masu kawo alheri domin nuna wa juna girmamawa, daga baya kuma sun koma gida sun sha alewa da 'ya'yan itatuwa, kuma suna shan ti suna yin zantakayya kan harkokin gida. Idan an yi sabani cikin shekarar da ta wuce a tsakanin dangogi da aminai, amma muddin sun yi wa juna bakunci a gun bikin bazara domin barka da sabuwar shekara, sai a ce sun kai fahimtar juna ke nan.

Aikace-aikacen da ake yi a bikin bazara suna nan iri daban- daban, a wasu wurare akan nuna wasannin kwaikwayo na wurin da finafinai, a wasu wurare daban kuma ana yin rawar zaki da yin raye- raye na gargajiya, da yin wasa na kwara-kwara, da kalaci baje-koli da aka yi cikin haikali, kai halin annashuwa na ranar bikin ya game ko'ina. Ba shakka yawancin mutane suna gida suna kallon telebijin, domin a lokacin bikin bazara gidajen rediyo mai hoto daban-daban sukan nuna shirye-shirye masu ban sha'awa kuma masu dacewa da mutane wadanda ke da shekaru daban-daban na haifuwa.

Manna takardun waka kwar biyu da zane-zane na sabuwar shekara, da kunna wutar fitilu masu launi, su ma aikace-aikace ne da ake yi domin murnar bikin bazara. A lokacin bikin, kasuwanni sukan sayar da zane-zane na sabuwar shekara da takardun waka kwar biyu iri daban-daban wadanda ke bayyana zaman jin dadin jama'a da ayyukan da suke yi cikin fara'a, wadannan kuma aka bar su don a zaba. Taron nune-nunen fitilu da aka yi a gun bikin bazara shi ma wani biki ne mai ban sha'awa kwarai, fitilu masu launi sun zama kayayyakin fasahar gargajiya ne na jama'ar kasar Sin, sana'ar yin fitilu ita ma ta samu bankasuwa a dauloli daban-daban, an buga hotonan dabbobi da wurare masu kayatarwa da jarumai daban-daban a kan jikin fitilu, sumfurorin fililu kuma iri daban-daban ne.

Bisa daguwar matsayin zaman rayuwar jama'a, hanyoyin da Sinawa ke bi wajen yin bikin bazara su ma suna ta sauyawa, daga cikinsu, hanyar zuwa sauran wurare domin yawon shakatawa ta zama wata sabuwar hanya ce da ake bi domin yin bikin bazara. (Umaru)

Bikin Qiqiao

Ran 7 ga watan Yuli bisa kalandar kasar Sin, ranar bikin Qiqiao ne na jama'ar kasar, an ce wannan rana kuma ta zama ranar haduwa ce da ake yi tsakanin tauraron da ake kira Altair da na Vega cikin aljanna.

A lokacin can can da, an yi rana sosai, kuma babu gizagizai ko kadan a sararin sama. Wani dodo na samaniya yana zaman kewa sosai, sai ya roki 'ya'ya mata 7 nasa da su yi kadi da wadari don yin tufaffi domin "aljanna". Zawwatin da 'ya'ya mata 7 suka saka ban da launin tsoka sai fari kawai, ba su da kyaun gani. Autar wadannan 'yanuwa mata 7 tana da basira, ta ga wani irin fure mai launuka iri 7 cikin lambun furanni, sai ta ciro irin wannan fure da yawa, kuma ta rina launuka masu kyaun gani a kan zare, sabo da kokarin da ta yi, a karshe an kada zare mai launi iri daban-daban. 'Yanuwa mata nata dukkansu sun yi farin ciki, sun yaba mata sabo da fasahar da ta nuna. Gaba dayansu suka tsai da kudurin cewa, idan an yi rana sai a sa wa "sararin sama" fararen tufaffi, a lokacin da ake ruwan sama sun sa masa fufaffi masu laurin toka, a kowace rana da safe da kuma magariba, sukan sa wa sararin sama tufaffi masu launi. Bayan da dodo wato ubansu ya san labarin, ya yi farin ciki kwarai, sai ya nada wa autarsa sunan "yarinya masakiya".

Yarinya masakiya tana sakar zawwati a kowace rana, lokacin da ta gaji sai ta huta cikin dan lokaci, kuma takan duba halin da mutane ke ciki a duniya. Da akwai wani saurayin da ya jawo hankalinta. Ta ga wannan saurayi wanda kullum yake yin noma shi kadai, a lokacin hutu sai ya yi magana da tsohon sa da ke gabansa, yarinya masakiya ta nuna masa tausayi, wannan saurayi kuwa shi ne mai kowon shanu.

Wata rana, tsohon sa ya gaya wa mai kowon shanu cewa, "Gobe rana 7 ga watan Yuli ne na kalandar gargajiya, 'ya'ya mata 7 na dodo za su sauka nan duniya don yin wanka. Lokacin da suke wanka, sai ka boye tufaffin yarinya masakiya, da haka ne kuwa za ta zama matarka". Da jin maganar tsohon sa, mai kiwon shanu ya jiku, kuma ya yi niyyar yin haka.

A wannan rana wato a ran 7 ga watan Yuli na kalandar kasar Sin, mai kiwon shanu ya boye kansa a tsakanin tsauren da ke bakin kogi, ba da dadewa ba sai aka ga gizagizai masu launi guda 7 suna tashi a sararin sama, kowane gizo-gizo ya tada wata mace da ta mutu ba. Bayan da wadannan matan da ba su mutu ba suka sauka a bakin kogin, dukkansu sun cire tufaffinsu, sun tsunduma cikin ruwan kogi mai tsabta. Da gani haka sai mai kiwon shanu ya zabura ya dauko tufaffin yarinya masakiya ya gudu, sabo da yana dugu da sauri, shi ya sa tsauren sun yi motsi sosai har sun firgitad da wadannan mata 7 wadanda suka yi saurin hawan kan gabar kogin, guda 6 daga cikinsu wadanda kowacensu ta sa tufaffinta na kanta, kuma sun tashi zuwa sararin samaniya, sai autarsu wato yarinya masakiya kawai ta dimauce ta tsaya a bakin kogi sabo da ba ta ga tufaffinta ba. Da ganin haka sai mai kiwon shanu ya fito ya yi i'ina ya ce wa yarinya masakiya, idan ta yarda ta yi wure da shi, sai ya mayar mata da tufaffinta. Da yarinya masakiya ta ga wannan saurayi wanda shi ne saurayin da take nuna masa kauna, sai ta karkada kanta cikin kanya wato ta yarda.

A wannan rana da dare, bisa shugabancin tsohon sa ne, mai kiwon shanu da yarinya masakiya suka yi bikin aure. Cikin shekaru 2 na baya, yarinya masakiya ta haifi jarirai 2 wato mace daya da namiji daya. Mai kiwon shanu da matarsa daya yana yin noma, dayar kuma tana sakar zawwati, suna cikin zaman jin dadi sosai.

Lokaci yana tafiya da sauri kamar kibtawa da bismilla sai ga shi shekaru 7 sun wuce, kwana daya na aljanna ya yi daidai da shekara daya ta duniya. A kowadanne ranaku 7 dodon yakan kirawo 'ya'yansa mata guda 7 sau daya, da ya ga yarinya masakiya ba ta koma fadar aljanna, kuma ta yi aure da wani mutumin duniya, sai ya yi fushi kwarai, a wannan rana wato a ran 7 ga watan Yuli na kalandar Gargajiya, ya aika da janar dodo da ya je ya komar da yarinya masakiya aljannar don yanke mata hukumci. Mai kiwon shanu ya ji bacin rai kwarai, ya sa dansa da diyarsa cikin manyan kwanduna 2 kuma ya dauke su da kafadarsu, yana biye da yarinya masakiya, tsohon sa ya yanke kahonsa daya kuma ya mai da shi wani kumbon da ya dauke da mai kiwon shanu da 'ya'yansa wadanda suka tashi zuwa sararin samaniya. Yaran 2 suna ta ruda cewa, "Uwa, Uwa"! Da yarinya masakiya ta ji kuwar mai kiwon shanu da 'ya'yanta, sai ta yi matukar kokari ta kubutar da kanta daga hannun janar dodo don haduwa da su. A wannan lokaci kuwa, sai dodon ya mika wani babban hannusa sosai, ya tsaga sararin sama ba zato ba tsammani, sai wani kogi mai manyan igiyoyin ruwa da ake kira "Milky Way" ya ratsa a tsakanin mai kiwon shanu da yarinya masakiya nan da nan. Amma a daidai wannan lokaci kuwa, wani irin tsuntsayen da ake kira Magpies masu yawan gaske sun tashi a sararin sama, har sun hauda wata gada bisa kogin, ta yadda mai kiwon shanu da yarinya masakiya za su iya haduwa da juna kan gadar. Dodon ya ga ba yadda zai yi, sai ya yarda da maikiwon shanu da yarinya masakiya da su hadu da juna sau daya a shekara wato a ran 7 ga watan Yuli a kan gadar Magpies.

Daga baya, a wannan rana wato a ran 7 ga watan Yuli bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, 'yan mata sukan "koyon fasaha" daga wajen yarinya masakiya, sun dauko jan igiyoyin zare masu launi da allurai 7, idan wata ta yi nasarar sa wa zare a hancin alluran ba tare da wata wahala ba, sai ta zama yarinya mai basira. An ce, a wannan rana da dare a karkashin tankar itatuwan inabi kuma, yara sukan iya jin rade-raden da ake yi tsakanin mai kiwon shanu da yarinya masakiya. (Umaru)

Bikin Chongyang

Ran 9 ga watan Satumba bisa kalandar kasar Sin, wani muhimmin bikin gargajiya ce ta jama'ar kasar Sin wato bikin Chongyang. A wannan rana ta kowace shekara, mutane dauke da tsofaffi da yara sukan je kallon furannin da ake kira Chrysanthemum da hawan dutse, kuma sukan dasa wani irin tsiren da ake kira Cornel wanda ake amfani da shi domin hada magani, da kuma cin cake mai launi.

Dalilin da ya sa aka samu sunan bikin Chongyang shi ne, sabo da mutanen zamanin da sun mai da lambar 9 a matsayin "lambar rana", rana 9 ga watan 9 wato watan Satumba ya zama 9 sau 2 ke nan, wato rana guda 2 ke nan, wanda ake kira bikin Chongyang cikin Sinanci, ya kasance da wata tatsauniya mai sha'awa sosai game da sunan bikin Chongyang. An ce, a karni na 3 na kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisallam, akwai wani mutam mai karfin iya yin abubuwa da yawa, sunansa Fei Changfang wanda ba ma kawai ya iya samar da isaka da ruwan sama ba, har ma ya iya aika da dodanni don kama aljanu. Bayan da wani saurayi mai suna Huan Jing ya samu wannan labari, ya nuna masa girmamawa sosai, kuma yana son mai da shi a matsayin malaminsa. Sabo da wanann saurayi yana da babbar niyya, sai Fei Changfang ya dauke shi almajirinsa, da koyar masa da fasahahi. Wata rana, Fei Changfang ya gaya wa Huan Jing cewa, "A ran 9 ga Satumba bias kalandar gargajiya, duk 'yan iyalinka za su gamu da wani babban hadari, ya kamata ka yi shiri sosai tun da wuri." Da jin haka sai Huan Jing ya dimauce, ya durkusa a gaban malaminsa nan da nan don rokon shi da ya ba shi dabarar kubutar da 'yan iyalinsa daga hadarin. Fei Changfang ya ce masa, "A ran 9 ga watan Satumba na kalandar kasar Sin, ya kamata ka dinka jakunkuna da yawa da jan zawati, kuma ka sa irin tsiren da ake kira Cornel a ciki, ka daure su a damatsanka, ka dauki barasar da aka jika furannin Chrysanthemum a ciki, kuma ka kai duk 'yan iyalinka tsofaffi da yara don hawa kan wani tudu kuma ku sha barasar a can, da haka ne za ku iya kauce wa wannan babban hadari". Huan Jing ya yi daidai abin da malamainsa ya fada cikin nitsuwa, wato a ran 9 ga watan Satumba da safe na kalandar kasar Sin, ya shugabanci duk 'yan iyalinsa da su hau kan wani tudun da ke kusa da gidansa, sun shafe yini daya suna zaune a can lami lafiya. A daren wannan rana, da Huan Jiang da 'yan iyalinsa suka koma gida suka duba, sun yi mamaki kwarai, wato duk shanu da awaki har da karnuka na gidansa sun mutu. Lalle sun kauce wa wani hadari. Daga nan ne, aikace-aikacen hawan tudu da kafa irin tsiren da ake kira Cornel da sha barasar furen Chrysanthemum abikin Chongyang wato bikin ran 9 ga Satumba na kalandar gargajiya sun zama wata al'ada wadda ta barbazu har fiye da shekaru 2000.

Da akwai wata waka ta tsohon zamani wadda ta samu karbuwa ko'ina a kasar Sin ta siffanta al'adar bikin Chongyang. Wakar nan wata shahararriyar waka ce mai sunan "Tunawa da 'yanuwa na lardin Shandong a ran 9 ga Satumba na kalandar gargajiya" wadda Wang Wei, babban mawaki na daular Tang wadda aka kafa daga shekarar 618 zuwa ta 907 ya rubuta. Duk wakar tana cewa haka, "Ni kadai ina wani wuri daban wato na zama bako ke nan, nakan tuna da dangogina sosai a duk lokutan manyan bukukuwa. Na san cewa a kan tudun da 'yanuwana ke hawa, an kafa tsiren Cornel ko'ina, amma an yi karancin mutum daya." A wancan lokaci, Wang Wei wanda yake da shekaru 10 da wani abu kawai da haihuwa ya zama bako yana zaune a hedkwatar kasar, ba shakka yakan tunawa da iyalinsa, musamman ma a lokutan bukukuwa, ya ga mutanen sauran iyalai sun taru gu daya cikin farin ciki, sai ya kara tunawa da dangoginsa. A lokacin bikin Chongyang, mutane 'yan iyalai daban- daban na hedkwatar kasa dukkansu suna lika tsiren Cornel a jikinsu, amma a gidansa na kansa an yi karancin wani mutum da ya lika Cornel, wannan mutum kuwa shi kansa ne.

Wata al'ada daban ta bikin Changyang ita ce cin cake na Changyang. Cikin Sinanci, lafazin kalmar cake da ta "sama" daya ne, ma'anarsa shi ne hawan mukamin sama, da samun wadata da arziki. Mutane sukan yi amfani da shinkafa mai yauki da rawayen shinkafa da kananan dabino don turara cake, kuma an kafa kananan tutoci masu launi a kan cake din wanda ake kiransa da suna "cake mai launi". Mutanen da suke zaune a filayen karkara, ba tudun da suke hawa a lokacin bikin, sai su ci cake da ya alamanta hawan tudu.

A zamanin da kuma, an ba wa bikin Chongyang ma'anar "tsawon rai", sabo da mutane suna ganin cewa, irin wadannan al'adun bikin Chongyan suna iya "bai wa mutane tsawon rai".

Har yanzu, mutane suna rike da al'adar hawan tudu da kallon furen Chrysanthemum a gun bikin Chongyang, a wannan rana kuma kantuna sukan sayar da cake mai launi. Ban da wannan kuma, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, mutane sun yi amfani da lafazin "ran 9 ga watan Satumba" ya yi daidai da na "lokaci mai tsawo", kuma an tsai da kudurin mai da wannan rana ta zama "bikin tsofaffi", wannan ba ma kawai yana da ma'anar bikin Chongyang ta da ba, kuma ya bayyana girmamawa da kaunar da ake nuna wa tsofaffi, da yi musu fatan zaman lafiya da tsawon rai. (Umaru)

Bikin Duanwu

Ran 5 ga watan Mayu na kalandar kasar Sin ranar bikin Duanwu ne, bikin Duanwu da bikin bazara da kuma bikin tsakiyar yanayin kaka sun zama "manyan bukukuwa guda 3 ne na kasar Sin".

Me ya sa aka ba wa bikin sunan haka wato "Duanwu"? A kashin gaskiya kuwa, kalmar "Duan" ma'anarta "farkon lokaci" ne, "ran 5 ga wata" kuma wato "Duanwu" ke nan, bisa dokokin da aka tsayar cikin kalandar kasar Sin an ce, watan Mayu wato watan "Wu" ne, shi ya sa ran 5 ga watan Mayu ya zama "Duanwu" ke nan.

Ya kasance da bayanoni da yawa wadanda suka sha bambam game da mafarin bikin Duanwu, wasu sun bayyana cewa, bikin Duanwu ya faru ne daga al'adar lokacin rani ta zamanin da, wasu kuma suna ganin cewa, ya faru ne sabo da girmamawar da mutanen da ke kwarin kogin Yangtse na zamanin da ke nuna wa dodon Totem, amma galiban mutane suna gani cewa, ana yin bikin Duanwu ne musamman domin tunawa da Qu Yuan, mawaki mai kishin kasa na zamanin da. Qu Yuan ya yi zaman rayuwarsa a karni na 3 na kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisallam a kasar Chu, bayan da wata kasar abokan gaba ta mamaye kasar mahaifarsa, ya yi haushi sosai har tsunduma cikin ruwan kogin Guluo ya mutu, ran nan kuwa ran 5 ga watan Mayu na kalandar kasar Sin ne. Daga baya kuma, a wannan rana ta kowace shekara, domin tunawa da halin kirki na Qu Yuan, mutane su kan sa shinkafa cikin fafaffiyar gora mai kauri don ba da sadaka gare shi. Daga baya kuma, fafaffiyar gora mai kauri da ke dauke da shinkafa ta sauya har ta zama wani irin abincin da ake kira Zongzi na yanzu.

Cin abincin Zongzi ya zama wata al'ada mafi muhimmanci a gun bikin Duanwu. A zamanin da, akan kira Zongzi da sunan "Jiaoshu", Zongzi kuma wani irin abinci ne da aka yi da shinkafa mai yauki, kuma an nade shinkafar da kunnuwan tsaure da na gora, kuma an daure su da zare, siffarsu kamar dala mai kusurwa 3, da matashin kai, kuma an turara su ko dafa su an ci. A jajibirin ranar bikin Duanwu da dare, iyalai daban-daban dukkansu sukan yi Zongzi, kuma sun dafa su ko turara su domin shirya abincikin bikin. Zongzi kuma ya zama kyauta ne da suke bai wa junansu, a lokacin da ake kai wa danginsu da aminansu ziyara a gun bikin Duanwu, mutane sukan ba wa junanansu kyautar Zongzi da iyalansu suka yi da kansu.

Cikin abincin bikin Duanwu, ban da Zongzi kuma akwai wasu ire-iren abinci daban a wurare daban-daban na kasar Sin, alal misali akan cin koyaye masu gishiri na agwagi, da shan irin barasar da ake kira Realgar, bisa abin da jama'a suka fada an ce, an yi haka ne duk domin kauce wa munanan abubuwa.

Ban da abinci kuma, ya kasance da al'adar jama'a ta kayan ado masu halin musamman a gun bikin Duanwu. A wannan rana, kowane iyali yakan rataya wata irin ciyawar da ake kira Mugwort da ta Cattail a bakin kofarsa, irin wadannan ciyayi 2 maganin gargajiya ne wadanda aka rataya su daga wani fanni domin kauce wa munanan abubuwa, daga wani fanni daban kuma sabo da a farkon lokacin rani, akan yi ruwan sama kuma da danshi, shi ya sa kwari masu guba sun karu kuma mutane sukan kamu wa da cututtuka, amma irin wadannan ciyayi 2 suna da amfanin yin rigakafi da kawar da ciwace-ciwace. Ban da wannan kuma, a gun bikin Duanwu, mutane sukan daure wani irin kayan wasa da igiyoyin zare masu launi domin yara, wannan yana nufin "tsawon rai", da dinkin kananan jakunkuna masu kamshi, siffarsu kamar damisa da duma wadanda aka sa turare a cikin, kuma akan rataya su da igiyar zare mai launi a gaban kirji na yara, da sa wa yara takalma masu siffar kawunan damisoshi, da sa musu wata irin riga mai siffar lu'u-lu'u da ke rufe ciki, wadda kuma aka yi dinkin surfanin damisa a kai, duk wadannan abubuwa an yi su ne domin kiyaye zaman lafiya da samun alheri ga yara.

Tseren kwale-kwalen da ake yi a sashen tsakiya da mashigar kogin Yangtze a teku da ke kudancin kasar Sin shi ma yana daya daga cikin muhimman al'adun bikin Duanwu. An ce wannan al'ada ita ma tana jibintar Qu Yuan, wato bayan da jama'a suka samu labarin tsundumar Qu Yuan cikin kogin, sun yi saurin tuka kwale- kwale zuwa wurin don cetonsa. Daga baya kuma wannan aiki ya sauya har ya zama al'adar yin tseren kwale-kwale agun bikin Duanwu. A lokacin bikin Duanwu na kowace shekara, akan yi gagaruman bukukuwan tsere-tseren kwale-kwale a bakin kogi ko tafki, a wasu wurare kuma har da kwale-kwale 50 zuwa 60 wadanda suka yi tsere-tsere, kuma an hauda kan dodo da aka sassaka da katako kan kowane kwale-kwale, dukkansu masu launi ne kuma masu siffofi daban-daban. Kuma an yi ta buga ganguna da kuge, da yin kirarin farin ciki a kan kwale kude, kwale-kwalen kuma suna tafiya da saurin gaske, kuma ga tutoci masu launi da aka kafa a bikin kogin suna ta karkadawa, ga mutane dubu-dubbai suna ta tada murya domin nuna fara'a. Tseren kwale-kwale mai ban sha'awa da aka yi ya ta da wani tashen bikin Duanwu. (Umaru)

Bikin Yuanxiao

Ran 15 ga watan Janairu bias kalandar kasar Sin, yana daya daga cikin bukukuwan gargajiya na kasar Sin wato bikin Yuanxiao wanda kuma ya kawo karshen duk bikin bazara.

Bikin Yuanxiao kuma akan kiran shi bikin Yuanxi, ko bikin Yuanye ko kuma bikin Shangyuan. Ranar bikin Yuanxiao da dare ya zama dare na farfo ke nan da da aka samu wata mai da'ira na sabuwar shekara ta kalandar gargajiya. A wannan rana da dare, jama'ar kasar Sin kullum suna da al'adar rataya fitilu masu launi iri- iri, sabo da haka akan kira bikin Yuanxiao da sunan "bikin nunin fitilu".

Kallon fitilu da cin wani irin abincin da ake kira Yuanxiao sun zama muhimman abubuwa guda 2 ne da akan yi a gun bikin Yuanxiao. Me ya sa akan rataya fitilu a gun bikin Yuanxiao? An ce, a shekarar 180 ta kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisallam, sarkin daular Xihan ta kasar Sin wato sarkin Hanwendi ya hau karagar mulki a ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar kasar Sin. Domin murnar wannan al'amari, sarkin ya tsai da kudurin mai da wannan rana da ta zama bikin nunin fitilu. A wannan rana da dare ta kowace shekara, yakan fita daga fadarsa domin yawon shakatawa, yana murna tare da jama'a. A wannan rana kuma, a kowane iyali kuma a tituna manya da kanana akan rataya fitilu masu launi kuma masu ban sha'awa iri daban-daban domin mutane su je su kalla. Zuwa shekarar 104 ta kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisallam, an tsai da bikin Yuanxiao da ya zama wani muhimmin bikin kasar Sin a hukunce. Kudurin ya kara habaka sikelin bikin Yuanxiao. Bisa dokokin da aka tsayar an ce, a wuraren jama'a da iyalai daban-daban, ya kamata a rataya fitilu da kyallaye masu launi iri-iri, musamman ma a unguwoyi masu wadata da cibiyoyin al'adu, ya kamata a shiyyya gagaruman bukukuwan nune-nunen fitilu. Mutane maza da mata, tsofaffi da yara suna kallon fitilu, da cinta ka-cici-ka-cici da aka rubuta kan fitilu, da yin wasan kunna fitilun dodo, daga baya kuma ana yin haka a kowace shekara har ya zama wata al'ada wadda aka tafiyar da ita a dauloli daban-daban. Bisa abubuwan da aka rubuta cikin littattafan tarihi an ce, a shekarar 713 na AD, daular Tang ta wancan lokaci ta kafa wani babban "dudun fitilu" wanda tsayinsa ya kai mita 7 wanda kuma aka kafa ire-iren fitilu masu launi fiye da dubu 50.

Fitilu masu launi na bikin Yuanxiao wadanda akan yi su ne da takardu masu launi iri-iri, wandanda kuma siffofinsu daban-daban ne ciki har da tudu da ruwa da gine-gine da mutane da furanni da tsuntsaye da dabbobi, daga cikin su kuma irin fitilar da ake kira fitilar ruwa ya fi gwada sigar musamman ta kasar Sin, fitilar ruwa wani irin fitilun kayan wasa ne, an ce irin wannan fitila tana da tarihi mai tsawon shekaru fiye da 1000. An hauda farfela cikin fitilar, bayan da aka kunna kyandir da ke cikin fitilar, sai tururi ya tashi sama har ya juya farfelar, sabo da haka takardar dokin da aka manna akan farfelar yana gudu da sauri. Inuwar takardar doki ta bayyanu a kan murfin titular, idan an duba daga waje sai a ga kamar ana yin kuwar dawaki ke nan, lalle yana da sha'awa kwarai.

Cin abincin Yuanxiao shi ma wata muhimmiyar al'ada ce da ake yi a gun bikin Yuanxiao. Kila a daular Song wadda aka kafa daga shekarar 960 zuwa ta 1279, lokacin da jama'a suke yin wannan biki, suka fara yin wani irin abinci mai ban mamaki, wato irin abinci kamar cincin da aka yi da garin shinkafa mai yauki, kuma an sa 'ya'yan itatuwa a ciki, bayan dafuwar sa kuma yana da kamshi da zaki kuma da dadin ci. Daga baya kuma, a yawancin wurare na arewacin kasar Sin akan kiran abincin da sunan "Yuanxiao", a mma a kudancin kasar kuma akan kiran shi da sunan "Tangyuan" da na "Tangtuan".

Bisa bunkasuwar da aka samu an ce, zuwa yanzu yawan ire- iren Yuanxiao ya karu har ya kai kusan 30, wato a cikin Yuanxiao akan sa wasu irin 'ya'yan itatuwa masu kaushin baya, da daddakakkan dabino, da markadadden wake da kwayoyin birana da sauran irin su guda 4, da ridi da kwayoyin koko da aka yi da cuku da kuma cakulan. Irin Yuanxiao da aka yi a wurare daban-daban su ma sun sha bambam, irin Tangyuan da ake yi a lardin Hunan da ke kudancin kasar launinsu fari fat, kuma suna da kamshi da zaki, irin Tangyuan na birnin Ningbo na lardein Zhejiang da ke gabashin kasar kuma ba su da garin shinkafa mai yauki da yawa, kuma an sa markadadden wake da daddakakkan dabono da sauran irin su da yawa a cikin, irin Tangyuan na birnin Shanghai kuma kanana ne, kuma suna da dadin ci, irin Yuanxiao masu zaki da ake yi da wani irin 'ya'yan itatuwa mai kaushin baya, da ridi da cuku a birnin Beijing su ma suna da halin musamman.

Ban da kallon fitilu da cin abincin Tangyuan a gun bikin Yuanxiao kuma, akan yi wasanni iri-iri, kamar na kwara-kwara ko mai gwangwala da yin raye-raye na gargajiya, da yin rawar zaki. Musamman ma ga rawar zaki wadda akan yi ba ma kawai a kasar Sin ba, har ma a duk wuraren duniya da Sinawa masu yawa ke zaune a lokutan sabuwar shekara da sauran bukukuwa. Kasar Sin tana da rukunoni 2 wajen yin rawar zaki wato "rukunin kudu" da "rukunin arewa". Rawar zaki da ake yi a kudancin kasar, akan yi ne ta hanyar mai da muhimmanci kan motsawar jiki da fasahar wasan, a galibi dai akan yi wasan ta da mutane 2, a lokacin da suke rawa, sukan yi motsi da yawa. Rawar zaki da ake yi a arewancin kasar Sin kuma, akan mai da muhimmanci kan gaggarumin hali mai kayatarwa, mutane fiye da 10 sukan yi rawar tare. Lokadin da ake yin rawar zaki kuma tare da kidan gargajiya na jama'ar kasar Sin, ko 'yan wasanni ko mutane masu kallon wasan dukkansu suna nuna himma ga yin wasan don nuna halin annashuwa na bikin Yuanxiao na ran 15 ga watan Janairu bias kalandar kasar Sin. (Umaru)

Al'adun bikin bazaar na kananan kabilun kasar Sin

Bikin bazara bikin tarraya ne na kabilu 56 na kasar Sin. Ban da kabilar Han, sauran kananan kabilu da yawa kuma suna murnar wannan bikin gagajiya ta hanyoyin musamman na kabilunsu na kansu.

Kabilar Li tana barbaje musamman a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. A jajibirin sabuwar shekara da dare, 'yan iyalin kabilar Li sukan taru gu daya suna shan giya da cin abinci masu dadi, a gun liyafar kuma sukan yi wake-wake domin barka da sabuwar shekara. A ran daya da ran 2 na sabuwar shekara na kalandar gargajiya ta kasar Sin, 'yan kabilar sukan yi farauta cikin kungiya- kungiya, ramun daji da suka samu sukan raba su kashi 2, daya a ba wa mutum na farko da ya harbo namun daji, daya daban kuma a rarraba wa sauran mutane, amma mata masu ciki sun iya samun rabo 2 na namun daji.

Kabilar Yi tana barbaje musamman a lardin Sichuan da ke kudu maso yammmacin kasar Sin. A lokacin bikin bazara 'yan kabilar Yi sukan yi wani irin rawar da ake kira "Axitiaoyue" domin murnar bikin. A rana ta farko da ta sabuwar shekara a wasu kauyuka ma akan bar maza da suka yi aikin gida, mata kuma sun huta, ta hanyar yin haka ne don nuna musu jejeto sabo da kokarin aikin da suka yi cikin shekarar da ta wuce.

Kabilar Miao tana barbaje musamman a larbin Hunan da na Guizhou na kasar Sin. 'Yan kabilar Miao suna kiran bikin bazara da sunan "Bikin sabuwar shekara ta Kejia", iyalai daban-daban dukkansu sukan yanke aladu da awaki don yin fatan kyakkyawan yanayi da samun babban girbi. Ban da wannan kuma, 'yan kabilar Miao sukan rera "wakar fara yanayin bazara", muhimmiyar ma'anar wakar ita ce yin tunani, da fatan zuwan yanayin bazara, da nuna sha'a da kuma yin begen rabuwa da yanayin.

Kabilar Man tana barbaje musamman a larduna 3 da ke arewa maso gabashin kasar Sin da birnin Beijing da kuma lardin Hebei na kasar. 'Yan kabilar Man sukan yi murnar bikin bazara sau 2 wato a ranar jajibiri da rana ta farko ta sabuwar shekara. A gabannin bikin bazara kuma sukan yi sukuwar dawaki da rakuma.

Kabilar Dong tana barbaje musamman a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A safiyar ran 1 ga watan farko na kalandar gargajiya, 'yan kabilar Dong sukan kama wasu kifayen da ake kira Carp daga tafkin kiwon kifaye kuma sun ajiye su a kan tebur din cin abinci, sun yi haka ne domin alamta cewa za a samu amfanin gona mai armashi kuma har da rana a cikin sabuwar shekara, domin lafazin kalmar "kifi" cikin Sinanci ya yi daidai da na "rara".

Kabilar Zhuang tana barbaje musamman a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin. 'Yan kabilar Zhuang suna son shirya abinci na ran 1 ga watan farko na kalandar gargajiya tun jajibiri da dare, sukan kira wannan abinci da sunan "abincin wucewar shekara". Wannan yana alamta cewa za a samu amfanin gona mai armashi cikin sabuwar shekara, da yin zaman jin dadi har da rana.

Kabilar Qiang tana barbaje musamman a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A lokacin bikin bazara, iyalai daban-daban na kabilar Qiang dukkansu suna yin hadaya da shanu da awaki domin ba da sadaka ga kakanninsu. Ban da wannan kuma, a jajibirin sabuwar shekara da dare, dukkan mutane suna zaune a kewayen babbar kwalabar giya, bisa shugabancin tsofaffin mutane ne suka yi amfani da wani haki mai tsawon mita daya don tsotson giya mai dadi daga cikin kwalbar bi da bi kuma daga hagu zuwa dama.

Kabilar Shui tana barbaje musamman a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A lokacin bikin bazara yaran 'yan kabilar Shui sukan je gidaje daban-daban domin neman samun alewa da 'ya'yan itatuwa daga wajen manyan mutane, ana dauka cewa wanda ya samu irin wadannan abubuwa mafiya yawa shi ne zai fi samun alheri, kuma zai yi basira da koshin lafiya a nan gaba.

Kabilar Bai tana barbaje musamman a lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A safiyar ran 1 ga watan farko na kalandar gargajiya, duk 'yan iyalin kabilar Bai tsofaffi da yara sukan cin abinci na farko wato sun jika babbakakken shinkafa cikin ruwa mai zafi, wannan yana nufin cewa, za a iya samun zaman jin dadi kamar zuma cikin sabuwar shekara.

Kabilar Korea tana barbaje musamman a lardin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Al'adar kabilar Korea ita ce iyalai daban-daban dukkansu sun manna takardun waka-kwar-biyu a jikin kofofinsu, kuma sun shirya abinci iri-iri, da cin irin shinkafar da ake kira "eight-treasure rice Pudding". A rana ta farko ta sabuwar shekara, da gari ya waye, sai mutane sun ci ado da tufafin ranar biki suna nuna wa mutanen zuriyar gaba gaisuwa domin barka da sabuwar shekara.

Kabilar Mongoliya ta na barbaje musamman a jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin. A safiyar ran 1 ga watan farko ta kalandar gargajiya ta kasar, samari maza da mata 'yan kabilar Mongoliya wadanda ke sanye da tufafi masu launuka daban-daban sukan hawa dawakin asbin don je bukkokin da da 'yan kabilar ke zaune don yi wa mutanen zuriyar gaba barka da sabuwar shekara. Ban da wannan kuma, 'yan kabilar Mongoliya sukan yi gagarumin bikin "yin rawar dodanni", mutane suna yin lullubinsu na karya suna waka suna rawa, wannan ya bayyana cewa, tsohuwar shekara ke wucewa, ana maraba da zuwan sabuwar shekara.

Kabilar Hani tana barbaje musamman a lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A lokacin bikin bazara, samari maza da mata 'yan kabilar Hani sukan taru gu daya suna shan giya, kuma suna waka suna rawa, sa'an nan kuma suna zabar masoyansu.

Kabilar Naxi tana barbaje musamman a lardin Yunnan da ke kud maso yammacin kasar Sin. A ran 1 ga watan farko na kalandar gargajiya, 'yan kabilar Naxi sukan yi babban biki domin yara masu shekaru 13 da haihuwa, in su 'yan mata ne sai a kira "bikin sa siket", don su yara maza kuwa sai a ce " bikin sa wando", ta hanyar yin wannan biki ne ake bayyana cewa, wadannan yara sun riga sun zama balagaggu.

Kabilar Pumi tana barbaje musamman a lardin Yunnan da na Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A safiyar rana 1 ga watan farko ta kalandar gargajiya, 'yan kabilar Pumi sukan fara yin bikin harba igwa, kuma suna busa katantanwar teku domin nuna murnar bikin.

Kabilar Buyi tana barbaje musamman a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A lokacin bikin bazara, samari maza da mata 'yan kabilar Buyi sukan ci ado da tufafin ranar bikin, kuma sukan je gaishe-gaishe wa junansu domin barka da sabuwar shekara, ko kuma sun yi yawon shakatawa, suna rawa suna waka, ba su komawa gida sai sun yi wasanni har sun yi farin ciki kwarai da gaske.

Kabilar Elunchun tana barbaje musamman a lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. A safiyar ran 1 ga watan farko na kalandar gargajiya, samari 'yan kabilar Elunchun wadanda da farko sukan mika wa mutanen zuriyar gaba wani kofin da ke cike da giya, kuma sun sara musu don nuna musu girmamawa da yin gaishe-gaishe. Daga baya kuma, mutane na zuriya daya sukan daga kofi don yi wa junansu fatan alheri. Bayan karya kumallo kuma, samari sukan taru gu daya don yin sukuwar dawaki da wasan harba kibiya da saura bukukuwa.

Kabilar Dawo'er tana barbaje musamman a lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. A safiyar ran 1 ga watan farko na kalandar gargajiya, samari 'yan kabilar Dawo'er wadanda hannayensu ke rike da tokar da ke kasa da tukunyar dafa abinci, kuma sun yi kokarin shafa wa fuskokin sauran mutane tokar, kyawawan 'yan mata sukan zama "mutane masu toka" sabo da tokar da samari maza suka shafe musu. An ce wannan yana nufin fatan samun amfanin gona mai armashi da zaman alheri. (Umaru)

Bikin Laba wato bikin ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin

A kasar Sin, akan kira watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin da sunan watan La, ran 8 ga watan Disamba na kalandar gargajiya na kasar Sin bikin Laba ke nan. Bikin Laba bikin gargajiya ne na al'ummmar kabilar Han ta kasar Sin, kuma ya zama kamar kidan farko ne na bikin bazara.

Bisa abin da aka rubuta cikin littafin tarihi an ce, a farkon lokaci bikin laba ya faru ne daga bikin Laji wato bikin ba da sadaka ga sarkin girki da aka yi a watan Disamba na zamanin da. Tun can zamanin da, kasar Sin ta mai da muhimmanci kan sha'anin noma. A duk lokutan da ake samun amfanin gona mai almashi, mutane na tsohon zamani sun bayyana cewa, wannan ya zama sakamako ne da aka samu sabo da taimakon da dukkan gumakan duniya da na samaniya suka bayar, shi ya sa sukan yi bukukuwan murnar samun amfanin gona mai armashi da nuna godiya ga gumakai, haka ake kiran "Laji" wato bikin ba da sadaka ga gumakai. Bayan da aka yi wannan biki, mutanen zamanin da sukan shirya liyafa, wato sun yi amfani da masara da gero da suka girba don dafa kunu, kuma sun sha kunun da suka dafa tare domin murnar bikin. Daga baya bikin Laji ya bunkasu har ya zama bikin da aka yi musamman domin ba da sadaka ga kakanin-kakani. A karni na 5 na AD, gwamnatin kasar ta tsai da cewa, ran 8 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin ya zama bikin Laba wato bikin ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiyar.

Bayan da addinin Buddha ya shigo nan kasar Sin, bisa al'adar da aka samu ta ba da sadaka ga kakanin-kakani da shan kunu a ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin, kuma an ba da wani labari cewa, ran 8 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin, rana ce da Sakyamuni wanda ya kirkiro addinin Budda ya zama dan addinin Budda. Muhimmin bayani na labarin shi ne, kafin Sakyamuni ya zama dan Budda, ya taba shan wahaloli da yawa domin bin addinin Budda cikin shekaru da yawa, ya rame sosai ya zama kashi da rai sabo da yunwa, sai ya tsai da kudurin barin aikinsa na bin addinin Budda. A wannan lokaci ya gamu da wata mace makiyayiya wadda ta ba shi wani irin abin sha da ake kira Chyle wanda aka yi da nono ya sha. Daga baya ya sake samun karfin jikinsa, sai ya zauna cikin inuwar itace da ake kira Badhi yana ta yin tunani sosai, har ya zama dan addinin Budda a ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin. Domin tunawa da wannan al'amari, 'yan addinin Buddha sun yi amfani da shinkafa da 'ya'yan itatuwa don dafa kunu don ba da sadaka ga Buddha a wannan rana, irin wannan abinci wanda ake kiran shi kunun Laba da ake yi da shinkafa da wake da 'ya'yan itatuwa a ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Tarihin shan kunun Laba da Sinawa ke yi yana da shekaru fiye da 1000. An fara bin wannan al'ada daga daular Song. A wannan zamani, a ran 8 ga Disamba na kowace shekara bisa kalandar kasar Sin, ko fadar sarkin kasa, ko kuma fadar gwamnati da haikali dukkansu suna dama kunun Laba. A tsakanin jama'a kuma, iyalai daban-daban su ma sun dama kunun Laba domin ba da sadaka ga kakanin-kakani. Sa'an nan kuma duk 'yan iyali sun hadu sun sha kunun, kuma sun ba wa dangogi da aminai kyautar kunun.

Akwai ire-iren kunun Laba da yawa. Bisa al'adar gargajiya da ake bi tsakanin jam'a an ce, cikin kunun Laba akwai muhimman abubuwa iri 8 da kayan zaki iri 8, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne, sabo da cikin Sinanci kalmar "Ba" wato takwas tana da ma'anar "alheri". Muhimman abubuwan da ake amfani da su domin dama kunun su ne wake da shinkafa, cikin waken da ake amfani da su kuma har da jan wake da koren wake da dogon wake da waken soya da sauran wakaikai iri-iri. Ire-iren shinkafa da ake amfani da su kuma su ne, gero da shinkafa da shinkafa da aka gyara ta sosai, da shinkafa mai yauki, da 'ya'yan wani irin ciyayi, da alkama da sha'ir masara da dawa da sauran shinkafa iri-iri. Mai gida ya iya zaben wasu irin shinkada da wake da yake so daga cikinsu.

Kayan zaki da ake amfani da su domin dafa kunun Laba wadanda kuma akan zaba daga cikin 'ya'yan itatuwa masu zaki da aka adana da wasu ire-iren 'ya'yan itatuwan da ake kira walnut da Chestnut da hazel da Pine nut wadanda bawonsu ke da kauri, da markadadden dabino, da kwayoyin bi rana, da 'ya'yan bado, da gyada da gujiya da zabiba.

Bayan da aka shirya muhimman abubuwa da kayan zaki, sai a dafa su tare da ruwa cikin wata irin tukunyar fadi-ka-mutu kan murhun da aka kunna wuta kadan, daga baya kuma a sa kayan zaki kamar sukari da rose da furen Osmanthus a ciki. Idan wasu iyalai wadanda suka mai da muhimmanci wajen abinci, kuma sukan mai da hankali wajen launin kunun Laba sosai, wato ba su yi amfani da wakakai wadanda launinsu masu duhu ba, maimakon haka sun dauki shinkafa mai yauki da kwayoyin hatsi da wani abu kamar bado da ke cikin ruwa, da 'ya'yan bado kawai, irin kunun da suka dama da irin wannan shinkafa fari ne fat kuma garau yeke wato kamar madubi, an kwashe shi cikin kasaken cin abinci masu kyau, lalle yana da kyaun gani kuma da dadin ci. A iya zaton cewa, cikin watan Disamba, ana sanyi kwarai har ma ga dusar kankara da ake yi, 'yan iyali daya sun zauna a kewayen tebur suna cin abinci, wato suna shan kunun Laba mai kamshi kuma mai zaki, lalle wannan ya za wani al'amari mai kyau kuma mai dadi sosai.

Tsofaffin mutanen birnin Beijing kullum suna daukar bikin Laba watao bikin ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin a matsayin alamar kusantowar bikin bazara, a wannan rana, iyalai daban-daban dukkansu suna shan kunun Laba. An taba rera wata waka kamar haka a birnin Beijing cewa, "Tsohuwa kada hankalinki ya tashi, da an wuce bikin Laba sai sabuwar shekara ta zo, a sha kunun Laba cikin 'yan kwanaki kadan, a kwana a tashi sai ran 23 ga Disamba bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin wato rana da sarkin girki zai tashi zuwa samaniya. ……"

A gun bikin Laba wato bikin Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin, ban da aikin dama kunun Laba, jama'ar arewancin kasar kuma suna da al'adar jika "tafarnuwar Laba". Uwargida ta iyali ta cire bawon tafarnuwa, ta ajiye su cikin kwalaba, kuma cika kwalabar da Vinegar, ta rufe bakin kwalabar a ran 8 ga Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin, kuma ta ajiye kwalabar a wani wuri mai dumi na cikin dakin. Ya zuwa jajibirin sabuwar shekara da dare, a lokacin da ake cin Jiaozi sai a fitar da tafarnuwan a ci. Tafarnuwan da aka jika launinsu kore shar ne, wato ya yi daidai da na irin lu'u-lu'un da ake kira jade, kuma ga Vinegar mai launin ja mai bakin ruwa, lalle suna da kyaun gani, sabo da haka, sun kara haddasa halin annanshuwa ga liyafar iyali. (Umaru)

Tatsuniyar jajibirin sabuwar shekara

A rana ta karshe ta watan Desamba da dare na kowace shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ana kiransa Chuxi. Kalmar Chu wadda ma'anarta wato kawar da wani abu ne, Xi kuwa dare ke nan. Chuxi wato kawar da dare na karshen shekarar da ake ciki da yin maraba da zuwan sabuwar shekara. A kasar Sin kuma akan kira jajibiri da sunan "kawar da dare", ko "daren shekara", ko kuma "Ran 30 ga Disamba na shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin".

Jama'ar kasar Sin suna da al'adu da yawa game da jajibirin sabuwar shekara. Al'adar tsabtar gama-gari a jajibirin tana da dogon tarihi. Cikin 'yan kwanaki na gabannin jajibirin, mutane sukan share dakunansu na gida da na waje sosai. Aranar jajibirin kuma akan mai da babban karfi wajen tsabtar gama-gari don "fid da rubabbu da daukar sababbi". Irin wannan al'ada ta zo daga tatsuniyar zamanin da, an ce a zamanin da sarkin Zhuanxu yana da wani dansa malalaci wanda ya ba ni kunya, yakan sa tufaffi tsumma da shan kunu a zaman yau da kullum. Ya mutu a jajibirin wata sabuwar shekara da dare a wata kusurwar dakinsa sabo da sanyi da yunwa. Sabo da haka, lokacin da mutane ke tsabtace dakunansu a ranar jajibirin, sukan fitar da tufaffi tsumma da abincin da suka yi musu saura, akan zubar da su kafin zuwan sabuwar shekara, wannan yana nufin cewa an hana shigowar talauci cikin gida.

Bayan tsabtar gama-gari, mutane sukan manna takardun waka-kwar-biyu a jikin kofofinsu, da rataye fitilu domin haifar da halin annashuwa. A jajibirin kuma mutane sukan sha wani irin abin sha da ake kira "Tusu" wanda aka yi da giya da ruwa. An ce, cikin wata bukkar da ake kira "Tusu", an zaunar da wani mutum da ba safai akan irinsa ba, wanda ya tono saiwoyin tsime musamman cikin dazuzzukan tuddai. A duk lokutan jajibiri, yakan ba wa iyalan kauyawa kyautar maganin gargajiya na kasar Sin da ya hada, kuma ya gaya musu cewa, dukkan 'yan iyalansu za su sha irin wannan magani a rana ta farko ta sabuwar shekara, da haka ne za su iya kawar da cututuka da masifa. Kuma ya gaya wa kauyawa irin saiwoyin tsime da ya yi amfani da su cikin magungunan da ya hada ba tare da rage kome ba, don haka kauyawa suke kira irin wannan magani da sunan "Tusu". A kashin gaskiya kuwa mene ne maganin "Tusu"? Bisa abubuwan da aka rubuta cikin littattafan magungunan zamanin da an ce, an hada shi ne da ire-iren magungunan gargajiya na kasar Sin har guda 7 ciki har da irin maganin da ake kira Rheum officinale da jijiyar lemu wadanda ke da amfani don yin rigakafi da warkar ciwace-ciwace.

A jajibirin sabuwar shekara da dare, akan hadu don cin abinci, kusan an ce wannan ya zama al'adar gargajiya ta kowace iyali. A wannan rana, duk wadanda suke aiki a sauran wurare, idan sun samu dama, sai su koma gida don haduwa da 'yan iyalansu, kuma sun dafa abinci iri-iri masu dadi don ci tare a jajibirin da dare.

A wurare daban-daban na kasar Sin, irin abincin da ake ci a jajibirin da dare su ma sun sha bamban. A kudancin kasar abincin yakan hada ne da nama da ganyaye wadanda yawan irinsu ya kai fiye da 10, daga cikinsu tilas ne da akwai irin abincin da ake kira "Tofu" wanda aka yi da wake da kuma kifi, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne sabo da kalmar "Fuyu" wadda lafazinta cikin Sinanci ya yi daidai da na "arziki". A arewancin kasar, yawancin iyalai suka ci abincin Jiaozi a jajibiri da dare, 'yan iyali duka suna yin Jiaozi tare, irin wannan abinci an yi shi ne ta hanyar kunsa daddatsattse nama mai dadin ci cikin kullin garin alkama mai siffar da'ira, bayan da aka kammala aikin yin Jiaozi, sai a dafa su cikin tafasassen ruwa, kuma an sa kayan zaki a cikin, duk 'yan iyalin sun zauna a kewayen tebur suna cin Jiaozi tare cikin annashuwa. "Jiaozi" yana alamta haduwar 'yan iyali.

A ranar jajibiri da dare, mutane sukan yi jagorar yaransu zuwa wajajen dangi da aminansu don ba su kyautar abubuwa, da yi musu barka da sabuwar shekara, haka ake kiran shi "Kuisui" wato ba da kyauta ga shekarar da ta wuce. Idan da baki sun zo sun ci abinci tare da 'yan iyali a jajibirin sabuwar shekara da dare, sai a ce "Biesui" ke nan wato yin ban kwana da shekarar da ta wuce. Bayan cin abincin, dukkan mutane sukan nuna wa juna godiya da yi wa junansu barka da sabuwar shekara, daga baya kuma kowa ya koma gidansa, wannan shi ake kira "Sansui" wato a tashi daga tsohuwar shekara. Cikin gida, ya kamata mutane matasa su nuna gaisuwa ga dattawa, mutane dattawa kuma su yi wa matasa wasu maganganun gargadi, kuma su bai wa yaran da ba su isa zuwa wurin aiki ba kudin kyauta domin murnar sabuwar shekara, kuma sun yi wa juna barka da sabuwar shekara, haka ake kira "ban kwana da tsohuwar shekara" A wannan lokaci, dukkan mutane ba su son su yi barci, 'yan iyali duka suna kallon talabijin, ko yin wasan kati, suna more zaman jin dadi har zuwa sabuwar shekara, haka ake kira "yin kwana zaune a jajibirin sabuwar shekara".

"Yin kwana zaune a jajibirin sabuwar shekara" ta zama wani aiki ne da aka saba yi a jajibirin. Cikin waka mai suna "Yin kwana zaune a jajibirin sabuwar shekara" da Lu You, mawakin tsohon zamanin kasar Sin ya rubuta, akwai jumloli masu kyau kamar haka, "Yara sun tsaya ba su yi barci ba, sun yi kwana zaune suna yin kwaramniya a tsakar dare". A lokacin da ake yin kwanan zaune a jajibirin sabuwar shekara, yara sun fi farin ciki, don su yara wadanda ake tsayawa sosai a kansu a kullum, su ma sun karya dokokin da aka yi musu a wannan lokaci, sun yi farin ciki tare da manyan mutane wajen yin kwana zaune har gari ya waye na rana ta farko ta sabuwar shekara, ana cike da kyakkyawan halin annashuwa na yi ban kwana da tsohuwar shekara da yin maraba da zuwan sabuwar shekara. (Umaru)

>>[Al'adun Jama'a]

Biki mai ban sha'awa na yanayin hunturu

Bikin shigowar hunturu yana daya daga cikin bukukuwan yanayin lokutan rana 24 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kuma wani bikin gargajiya ne na Sinawa. Tun zamanin Chunqiu na kasar Sin na kafin shekaru fiye da 2700 da suka wuce, an fara yin wannan biki wato "bikin shigowar yanayin hunturu".

Cikin Sinanci, kalmar "Zhi" ma'anarta innanaha ke nan. Wannan ba ya nufin cewa, yawan sanyi ya kai innanha a ranar bikin ba, amma an tsai da wannan biki ne bisa tsarin juyawar duniya da rana. Don su mutane wadanda suke zama a arewancin duniya, a wannan ranar biki, tsawon lokacin rana ya fi gajarta. Bayan bikin kuma, tsaron lokacin rana ya karu a kowace rana. Bisa abubuwan da aka rubuta cikin littattafan tarihi an ce, a gun bikin shigowar hunturu, sarkin kasa yakan rore kide-kide har kwanaki 5 tare da ministocinsa. Ko cikin gidajen manoma ma ana ta busa da kuma kada kayayyakin kide-kide. A wannan rana kuma, sarkin kasa yakan gayyaci masanan ilmin yanayin sama da tsarin kalanda don kyautata tsarin , sa'an nan kuma yakan yi bikin bautawa samaniya. Haikalin samaniya da ake kira Temple of Heaven na birnin Beijing wanda ya shahara a duniya shi ne wurin da sarkin kasa ke yin bikin da bautawa samaniya a wannan ranar bikin shigowar hunturu.

A zamanin da a ranar bikin shigowar hunturu, akwai al'adar "taya murnar hunturu". An yi bikin cikin halin annashuwa sosai. A wannan rana da safe, mutane manya da kanana sukan tashi daga barci tun da wuri, kuma suna sanye da tufaffi masu kyau, suna kai da kawowa domin taya wa junansu murna. Mutanen kasar Sin sukan kira bikin shigowar hunturu da sunan "shiga cikin cikin lokuta 9 na bayan bikin shigowar hunturu". Mutane sun saba yin kidayar kwanaki tara-tara na bayan bikin shigowar hunturu, wato kowadanne kwanaki 9 ya zama "tara daya", kwanaki 9 na farko ya zama "tara na farko", ranar bikin shigowar hunturu ta zo ne a kwana na farko na "tara na farko". Kwanaki 9 na biyu ya zama "tara na biyu". Ana ta yin haka, har zuwa "tara na tara", wato jimlar kwanaki ta ta kai 81, bayan kwana na 81 ya wuce, sai "furannin Peach" sun toho, kuma an fara shiga yanayi mai zafi. Jama'a kuma sukan rewa wata waka don bayyana tsarin sauyawar yanayin sama da aka yi daga bikin hunturu cewar, "Cikin kwanaki 9 na farko da na biyu, ba a iya mika hannu ba sabo da sanyi. Cikin kwanaki 9 na uku da na hudu, kyanwa da kare sukan mutu sabo da sanyi mai tsanani. Cikin kwanaki 9 na biyar da na shida, irin itatuwan da ake kira Willow sukan fara tsirowa. Cikin kwanaki 9 na bakwai, kankarar da ke cikin koguna ta fara narkewa. Cikin kwanaki 9 na takwas, dinyar da ba ta da gida suna ta zuwa. Cikin kwanaki 9 na tara kuma sanyi ya kare, yanayin bazara ya zo kuma furanni suna ta tohowa."

Jama'ar kasar Sin kuma suna da al'adar zana "hoton kawar da sanyi cikin kwanaki tara-tara daga ranar bikin shigowar hunturu. Da farko a zana wani reshen furen da ake kira Plum, amma ba mai launi ba ne, yawan kunnuwan furannin da aka zana ya kai 81, wannan yana nufin kwanaki 81 daga ranar bikin shigowar hunturu. Bayan bikin, kowace rana a zana kunnen fure daya da launi, bayan da aka kammala aikin zana duk kunnuwan furanni 81, sai yanayin bazara ya zo ke nan. Wasu mutane sun mai da hankali sosai wajen yin zane da launi, wato idan rana ta dushe, sai a zana kashi na sama na kunnen fure, idan an yi hasken rana, sai a zana kashi na kasa na kunnen furen. Idan an yi iska, sai a zana kashi na hagu, amma idan an yi ruwan sama, sai a zana kashi na dama na kunnen furen, idan an yi dusar kankara kuma sai a zana sashen tsakiya na kunnen furen. Sabo da haka ne, bayan kwanaki 81 da suka wuce, sai a kammala aikin cika wani jadawalin bayani mai ban sha'awa na yanayin sama. (Umaru)

Bikin share kaburbura

A lokacin bazara na kowace shekara, yanayi yana da kyau, furanni suna tohowa, kuma duk halittu masu rai suna farfadowa, a wannan lokaci ne sinawa suna marabtar wani bikin da ya barbazu tun da dadewa a tsakanin jma'a, wato bikin share kaburbura.

Bikin share kaburbura yana daya daga cikin bukukuwa 24 da aka tsayar cikin kalandar gargajiya ta kasar Sin, wanda yakan zo a farkon watan Afril ne bisa kalandar Gregorian wato kalandar Turawa. A wannan rana ta kowace shekara, mutane sukan je karkarar birane inda suke share kaburburan kakanin-kakaninsu domin yin tunaniya, ko kuma su yi yawon shakatawa na yanayin bazara, sukan yanke rassan wani irin itacen da ake kira Willow kuma sukan lika su a bakin kofa.

A wasu wurare ma ana kiran bikin share kaburbura da suna "bikin aljana", da haka ake iya ganin cewa bikin nan biki ne da ake yi domin tunawa da kakanin-kakaninsu. A gabannin ko a bayan bikin, iyalai daban-daban sukan je wajen kaburbura domin ba da sadaka da kuma nuna ladabi ga kakani-kakaninsu, sukan cire hakukuwa don tsabtacce kaburbura da zuba kasa a kai, sun kunna turaren wuta da kyandir, da kone takardun kudin jabu da ake kunnawa domin matattu, sun yi sujada ko kuma sun tsaya cik a gaban kaburbura don nuna alhini. A lokacin daular Song da aka kafa daga shekarar 960 zuwa ta 1279, an rubuta wata waka wadda ta siffanta al'adar tsabtace kaburbura da aka yi don tunawa da matattu cewar, "Akwai kaburbura da yawa a kan kuloluwan tuddai na kudu da na arewa, a gun bikin share kaburbura, mutane suna ta zuwa domin ba da sadaka ga kakanin-kakaninsu. Tokar takardun kudin jabu da ake kunnawa domin matattu ya tashi kamar fararen malaman bude littafi, hawaye da jini da aka zubar sun rina furen Azalea ya zama ja wur".

An ce bikin share kaburbura ya fara daga daular Han wadda aka kafa daga shekarar 206 ta kafin haifuwar annabi isa Alaihisallam zuwa shekarar 220 AD, zuwa daular Ming da ta Qing wadanda aka kafa daga shekarar 1368 zuwa ta 1911, an yi wani tashe wajen bin al'adar share kaburbura, wasu mutane wadanda ba ma kawai sukan je wajen kaburburan kakanin-kakaninsu don kona takardun kudin jabo ba, har ma sukan yi abinci iri 10 su ajiye a gaban kaburbura don ba da sadaka ga matattu.

Tsabtace kaburbura domin tsunawa da kakani-kakani a gun bikin share kaburbura ya zama wata al'adar jama'a , kuma ya barbazu har zuwa yanzu, amma yanzu ana bin wannan al'ada ta hanya mai sauki. A da akan bin wannan al'ada cikin iyali-iyali, amma yanzu akan yi bikin ne cikin kungiya-kungiya. A duk lokutan da aka yi bikin share kaburbura, mutane sukan je wajen kaburburan jarumai mazajen jiya, inda suka ba da kyautar wani daurin furanni, ko wani kambun furanni, ko kuma wani reshen itacen Pine domin nuna alhini da bege ga wadannan mazajen jiya.

Bikin share kaburbura ya zo ne a daidai lokacin bazara wato lokacin da duk halittu masu rai ke farfadowa, ko da yake an fara yin wannan biki domin tunawa da kakani-kakani, amma cikin dogon lokacin da ya wuce an samu bunkasuwa wajen yin bikin, wato akan yi tafiya don yin nishadi. Akan je karkarar birane domin yawon shakatawa. A wasu wurare ma akan kira bikin share kaburbura da sunan "bikin yawon shakatawa don yin nishadi".

A zamanin da kuma akwai wata al'adar tono gadali a lokacin da ake yawo don yin nishadi, har yanzu ana iya ganin irin wannan al'ada. A duk lokutan gabanni da kuma bayan bikin, da akwai wasu 'yan mata da mata wadanda suka je yawo don yin nishadi, kuma suka tono gadali, bayan da suka koma gida sukan yi wani irin abinci da ake kira Jiaozi da Yuanzi da gadalin, irin wadannan abinci suna da kamshi kuma suna da halayen musamman. Wasu 'yan mata kuma sukan lika kanana kuma fararen furannin gadalin a kan daurin gashinsu.

A gun bikin share kaburbura kuma, mutane suna da al'adar wasan tsuntsun takarda, da jan igiya da wasan lilo.

To, me ya sa ana kiran wannan bikin share kaburbura da sunan "biki mai tsabta kuma mai haske"? Dalili kuwa shi ne, sabo da a wannan lokaci, yanayin bazara ya zo, ana iska mai dumi amma ba sosai ba, ciyayi sun yi tsiro, duk halittu masu rai suna farfadowa, kila wannan ma'anar "mai tsabtace kuma mai haske" ke nan. Lokacin bikin share kaburbura kyakkyawan lokaci ne ga manoma wajen huda gonaki da baza iri wato lokacin bazara, manoma suna da karin magana da yawa game da bikin share kaburbura da yin sha'anin noma, alal misali, "Akan dasa kankana da wake a gabanni kuma a bayan bikin", "kada a dasa itatuwa bayan bikin share kaburbura, kome da aka dasa kafin bikin ko sanda ma za ta tsiro".

Ban da wannan kuma a zamanin da akan yi dashe-dashen bishiyoyi a gun bikin share karurbura, cikin wakokin da aka rubuta a tsohon zamnai akwai wannan jumla wato "Itatuwan Poplar da Willow masu kore shar da aka dasa a duk tituna sun yi kamar hayaki, wannan ya siffanta yanayin watan Maris na kalantar gargajiya ta kasar Sin". (Umaru)

Almarar nuna godiya ga sarkin girki

Cikin shekaru fiye da 2000 da suka wuce, kasar Sin kullum tana da al'adar ba da sadaka don tunawa da sarkin girki a ran 23 ga watan Disamba na kowace shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, an yi haka ne domin nuna godiya ga sarkin girki.

Sarkin girki wani gunki ne daga cikin labaran zamanin da, kuma wani jimi'i ne da sarki mafi koli na addinin Dao da ke sararin sama ya aike shi zuwa kowane iyali. Dole ne sarkin girki ya ba da rahoto ga sarki mafi koli na addinin Dao a kowace shekara, sabo da haka, mutane sukan nuna masa girmamawa. Domin yi wa sarkin girki fadanci, mutane sun yi haifar da al'adar ba da sadaka gare shi a kowace shekara. Da akwai tatsuniyoyi da yawa da suka shafi al'adar ba da sadaka ga sarkin girki, kuma suna da sha'awa sosai.

A zamanin da, an yi wani mai arziki mai suna Zhang Sheng wanda matarsa ke da suna Ding Xing wadda ke da fuska mai kwarjini, kuma tana da kirki. A farkon lokaci da akwai soyayya a tsakaninsu, kuma suna cikin zaman jituwa.

Wata rana, Zhang Sheng yana yin kasuwanci a wani wuri daban, inda ya ga wata mace kyakkyawa mai suna Haitang, sai ya nuna mata kauna nan da nan. Haitang ta ga Zhang Sheng mai arziki ne, kuma yana marawa mata baya cikin ganin damarsa. Ba da dadewa ba, Zhang Sheng ya auri Haitang zuwa gidansa. Haitang ta ga Ding Xiang ta fi ta kyau da sirantaka, ita ce kuma matarsa ta gaskiya, shi ya sa ta nuna mata kishi, ta tilsta Zhang Sheng da ya yi watsi da ita kuma ya kore ta daga gidansa.

Daga nan ne, Zhang Sheng da Li Haitang sun zama su ne masu nama kuma masu wuka, sabo da almubazarancin da suka yi, shi ya sa cikin lokacin da bai kai shekaru 2 ba kawai, sun mai da wani iyali mai arziki ya zama mai talauci. Haitan ta ga Zhang Sheng ya zama matsiyaci, sai ta bar shi gida ta auri wani namiji daban. Zhang Sheng ya zama mutum daya maras dangi, bai iya yin kome ba, ba yadda zai yi sai ya yi bara bisa tituna. Wata rana ana yin dusar kankara sosai, yana jin yunwa da sanyi, a karshe har ya suma kuma ya fadi a bakin kofar wani iyali mai arziki. Da yarinyar gida na wannan iyali ta ga wani mutum ya kwanta a kasa, sai ta gaya wa uwargida, kuma ta taimake shi don shiga cikin madafi. Ba da jimawa ba, uwargidan ta zo ganinsa, da Zhang Sheng ya gan ta, ya yi mamaki kwarai, ashe wannan uwargida Ding Xiang ce wadda ya kashe aure da ita yau da shekaru 2 da suka wuce, nan da nan ya ji kunya sosai. Yana son boye kansa, amma ya kasa, da ya farga, sai ya shiga cikin murhu. Da Ding Xiang ta shiga cikin madafi, ba ta ga kowa ba, ta yi mamaki sosai. Daga baya ta ga wani abu da ya toshe bakin murmu, ta je ta jawo shi waje, ashe Zhang Sheng ne wanda ya riga ya mutu sabo da konewar wuta. Ding Xiang tana ganin cewa, shi tsohon mijinta ne, ta yi bakin rai sosai, ba da dadewa ba ita ma ta mutu sabo da matukar bakin ciki sosai. Bayan da sarki mafi koli na addinin Dao da ke sararin samaniya ya ji wannan labari, yana gani cewa, Zhang Sheng ya gane kuskurensa, shi mutumin kirki ne, shi ya sa ya nada shi da ya zama sarkin girki. Daga baya kuma mutane sun dauki Ding Xiang a matsayin sarauniyar girki, ana ba da sadaka ga ita da kuma Zhang Sheng a cikin madafi.

A zamanin da, domin neman sarkin girki da ya yi musu yabo a gaban sarki mafi koli da ke sararin samaniya, mutane sukan yi amfani da alewar murhu domin nuna godiya ga sarkin girki. Alewar murhu wata irin alewa ce mai danko kuma mai zaki wadda ake yi da malt na sha'ir. Idan an ci irin wannan alewa, da yake ba ta da zaki sosai, amma takan kama hakora. Mutane suna son yin amfani da ita domin nuna godiya ga sarkin girki ta hanyar ba shi sadakar alewar, da sarkin ya ci salewar sai lebunansa sun kamu da juna, kuma zai yi wa mutane yabo da yawa amma ba zai yi musu batanci ba. Alhali kuwa wannan wani irin fata mai sha'awa kuma mai ban dariya ne kawai. (Umaru)

Al'adar aure ta kasar Sin

Kasar Sin tana da dogon tarihi da yankuna masu fadi. Daga tsohon zamani zuwa yanzu, kullum ana yin sauye-sauye wajen al'adar aure, amma halin da ake ciki a gun aure wato gagarumin halin annashuwa da murna da alheri ba su sake ba a ko yaushe.

Ya kasance da tsare-tsaren ladabi iri 6 wajen yin aure a tsohon zamanin kasar Sin, wadanda ake kiran su bukukuwa 6, ciki har da ba da kayan toshi domin neman aure da tabbatar da aure, da bikin daukan amarya. A da, idan wani saurayi yana son wata yarinya, sai ya roki kawaliya da ta je gidan yarinyar domin neman aure, a wannan okaci kuwa ba ma kawai iyalin saurayin ya ba wa kawaliya wasu abubuwa kyauta ba, har ma ya kamata ya roki kawaliya da ta mika masa wasu abubuwa kyauta ga iyalin yarinyar, sa'an nan kuma kawaliya ta yi musanyar kundayen da aka rubuta sunayen saurayi da yarinya da yawan shekarunsu da haihuwa a ciki tsakanin bangarorin 2. Idan bangarorin 2 sun yarda, sai su fara ganawa da juna, a wannan lokaci kuwa uwargidan saurayin ta zabi wata ranar sa'a ta je gidan yarinyar don kara samun labarinta, kamar halin tattalin arzikin iyalin yarinyar, da halin kirki da kuma siffarta, wasu iyayen yarinya su ma sun je gidan saurayi don ganin mijin diyarsu na nan gaba, amma a zamanin da, an hana 'yan mata da su je gidajen samari don ganin mijinsu na nan gaba. Yanzu abin ya zo da akasi, a karkashin rakiyar iyayensu ne, yawancin 'yan mata kan je gidajen samari domin samun labari, a wasu kauyuka da ke karkarar birnin Beijing, idan yarinya da iyayenta sun zauna kuma sun ci abincin a gidan saurayin, wannan ya bayyana cewa, sun amince da saurayin.

Bikin tsai da aure ya zama wani abu mafi muhimmanci da aka yi daga cikin bukukuwan aure, ko da yake bikin tsai da aure wata ala'ada ce ta jama'a, amma yakan taimaka ga dokokin shari'a. A gun bikin tsai da aure da aka yi iyalin saurayi kan ba da abubuwa kyauta ga yarinya da iyalinta. A birnin Wenzhou na kudancin kasar Sin, mutane suna daukar zobe guda 2 bisa matsayin da'ira, cikin rubuce-rubucen kalmomi na da masu kama da hotuna, "da'ira" tana alamta dauwamammiya wadda ta bayyana cewa, auren da aka yi tsakanin saurayi da yarinyar ba zai sauya ba. Bisa tunanin gargajiya an ce, idan an tsai da aure tsakanin wanin namiji da wata yarinya ba za a iya sake shi ba, kuma kada su yi aure da sauran mutane, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne, sabo da an dauki aikin tsai da aure bias matsayin wata irin dokar shari'a. Bayan da gefunan 2 suka yi aikace- aikace a jere, suka shiga cikin matakin daukan amarya, wannan ya zama wani bikin mafi yawan harkoki, mafi yamutsi, kuma mafi annashuwa daga cikin bubukuwan aure da aka yi a zamannin da ko a yanzu.

A ranar da ake daukan amarya wadda takan saye da jajayen tufafi don alamta alheri da fara'a, amma yanzu a wasu wurare akan sa dogon siket fari fat. Yayin da amarya ta bar gidanta, tana tafiya tana kuka domin nuna begen rabuwa da iyalinta. Bayan da amarya ta isa gidan ango, sai a fara bikin aure. A wasu wurare, bayan da amarya ta shiga cikin farfajiyar gidan ango, ya kamata ta ketare wata tasar kunna wuta, ma'anarta ita ce kone abubuwa marasa sa'a, ta yadda ango da amaryarsa za su yi zaman wadata a nan gaba. Bayan da amarya ta shiga cikin daki, sai a fara yin biki daya bayan daya. Biki na farko shi ne nuna godiya, da farko nuna godiya ga Allah, na 2 nuna godiya ga iyayen ango da na amarya, na 3 kuma ango da amarya su rusuna wa juna. Daga bisani kuma, sun sha giya a kofin junansu. A cikin dakin ango da amaryasa, kuma sun yanke gashin junansu kadan, kuma sun adana su a matsayin kyautar nuna amincewa.

Babban tashe na bikin aure shi ne liyafar aure wadda akan kira "liyafar murna". Sabo da haka mutane sukan ce, halartar bikin aure "shan giyar murna" ke nan. Jama'a sun mai da muhimmanci kan sikelin liyafar murna, sabo da wannan ya zama wani fanni da ya bayyana yawan kasaitaccen bikin aure da aka shirya, shi ya sa an mai da muhimmanci sosai a kan sa. A gun liyafar, ya kamata amarya ita kanta ta cika wa baki kofofin giyarsu, kuma ta kwashe musu nama da ganye domin nuna musu godiya ga halartar bikin. Dakin barci na ango da amaryarsa wanda akan kira shi da suna "dakin murna" ko "dakin aure", zolayar da aka yi wa ango da amaryarsa cikin dakin aure ta zama aiki na karshe na bikin aure, mutanen da suka yi wannan aiki yawancinsu samari maza da mata ne, wadanda suka yi iyakacin kokari don neman jin dadi, ko yi wa ango da amaryarsa tambayoyi masu wuyar ba da amsa, ko yi musu ba'a, ko neme su da su nuna wasanni, makasudin yin haka shi ne domin kara samun halin annashuwa ga bikin aure, ta yadda ango da amaryarsa ba za su manta da bikin ba muddin rayukansu. (Umaru)

>>[Al'adun Ci Abinci]

Al'adar shan ti ta Sinawa

Sinawa suna da tarihin fiye da shekaru 4000 wajen shan ti, daya daga cikin daga cikin abubuwan sha da Sinawa ba su rabuwa da shi cikin zaman yau da kullum shi ne ti, kamar yadda masu iya magana ke cewa, ti yana daya daga cikin abubuwa 7 wato "makamashi da shinkafa da man toya da gishiri da miya mai kauri da bininga da ti" wadanda ake gamuwa da su a kowace rana, daga nan ne ake iya gane muhimmanci shan ti. Karbar baki da ti ya zama wata al'adar Sinawa. Da bako ya shigo, mai gida sai ya mika masa ti mai kamshi kofi daya, suna shan ti suna zantakayya cikin halin sakin jiki da fara'a.

Al'adar shan ti tana da dogon tarihi a kasar Sin. An ce, kafin shekara ta 280, da akwai wata karamar kasa mai suna Wu da ke kudancin kasar Sin, yayin da sarkin kasa yake shirya liyafa domin ministoci, yakan ba su barasa su sha har su bugu. Daga cikinsu da akwai wani minista mai suna Wei Zhao wanda ba ya iya shan giya da yawa, sai sarkin kasa ya yarda da shi da ya sha ti maimakon barasa. Daga nan ne 'yan boko sukan yi amfani da ti don karbar baki. Ya zuwa dualar Tang, shan ti ya riga ya zama wata irin al'ada. An ce, irin wannan al'ada ta dangane da addinin Budda. Daga shekarar 713 zuwa ta 741, yayin da limamin Budda da masu bin addinin da ke cikin haikali suke zugum suna addu'a cikin dogon lokaci, sukan yi gyangyadi da cin abinci sabo da barci da yunwa suka ji, sai tsoffin limaman Budda sun yi wata dabara wato sun ba su ti su sha don kara kuzarinsu, daga baya wannan dabara ta barbazu zuwa wurare daban- daban. Sa'an nan kuma, iyalai masu arziki na dualar Tang sun bude dakunan musamman domin dafa ti da na shan ti da na karatu wadanda ake kiran su da sunan dakunan shan ti.

A shekarar 780, wani kwararren shayi mai suna Lu Yu na dualar Tang ya takaita fasahohin dasa itatuwan shayi, da na yin shayi da na shan ti, kuma ya rubuta littafin farko na kasar Sin dangane da ti wanda yake da sunan "Fasahohin ti". A dualar Song, sarkin kasa wato Songhuizong ya shirya liyafar ti don shagalta ministoci, kuma ya dafa ti shi da kansa. Cikin fadar sarakunan dualar Qing ba ma kawai an sha ti a gun liyafa ba, kuma an yi amfani da ti domin shagalta 'yan diplomasiya na kasashen waje. Yanzu a gun bikin sabuwar shekara da na bazara da sauran muhimman bukukuwan da ake shiryawa a kowace shekara, wasu hokumomi da kungiyoyi sukan shirya bukukuwan shan ti.

A kasar Sin, ti ya riga ya zama wani irin al'adu mai sigar musamman. Mutane suna daukar aikin dafa da kuma shan ti a matsayin wata irin fasaha. Daga tsohon zamani zuwa yanzu, an gina ire-iren dakuna masu hawa 2 da hawa daya na shan ti a wurare daban-daban na kasar Sin, a gefen babban titin Qianmen mai wadata na birnin Beijing ma akwai dakunan shan ti na musamman. A can, mutane suna shaye-shaye da taune-taune da kallon wasannin fasaha, suna hutawa da yin nishadi tare. A kudancin kasar Sin, ba ma kawai an gina dakuna masu bene ko marasa bene domin shan ti ba, har ma da akwai runfunan shan ti, irin wannan runfunan akan gina su ne a wurare masu kayatarwa, inda masu yawon shakatawa suke shan ti sa'an nan suke kallon wurare masu kayatarwa.

Wajen shan ti ma akwai al'ada, bari mu dauki shayi kamar missali, abubuwan da mutanen wurare daban-daban suke so wadanda ba su kasance iri daya ba, ire-iren shayin da suke so su ma sun sha bambam. Mutanen birnin Beijing suna son irin shayin da aka yi da furani, mutane birnin Shanghai ma suna son shan koren shayi. Amma mutanen lardin Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin kuma sun fi son shan jan shayi. A wasu wurare kuma, lokacin da ake shan ti akan sa wasu kayan kamshi a cikin, alal missali, a wasu wuraren lardin Hunan da ke kudancin kasar Sin, mutane sukan karbi baki da ti tare da citta da gishiri, wato ba ma kawai an sa ganyen shayi a cikin ti ba, har ma da akwai citta da gishiri da waken soya da ridi a ciki, lokacin da ake shan ti kuma ana karkada kofi, a karshe kuma an sa wake da ridi da citta da shiyi cikin baki ana ta yin taune-taune don jin kamshinsu, sabo da haka a wurare da yawa ana cewa "cin ti" maimakon "shan ti".

Hanyoyin da ake bi a wurare daban-daban su ma sun sha bambam wajen jikon ti. A gabashin kasar Sin mutane suna son yin amfani da manyan butocin shayi, da bako ya shigo, sai mai gida ya sa shayi cikin buta, kuma ya zuba tafasasshen ruwa a ciki, bayan da shayin ya jiku, sai ya zuba ti cikin kofi, kuma ya roki bako ya sha. A wasu wurare daban, kamar a yankin Zhangzhou na lardin Fujian da ke gabashin kasar Sin, ba ma kawai kayayykin shan ti suna da sigar musamman ba, har ma dabarar jikon ti ta sha bambam da ta sauran wurare, ta zama wata irin fasahar shan ti ta musamman.

A wurare daban-daban na kasar Sin, al'adar shan ti ma daban- daban ne, a birnin Beijing, mai gida ya dauki ti kofi daya, ya kamata bako ya tashi nan da nan, ya karbi kofin da hannaye 2, kuma ya yi "godiya". A lardin Guandong da jihar Guangxi da ke kudancin kasar Sin, bayan da mai gida ya kawo ti kofi daya, ya kamata bako ya buga tebur sau 3 da yatsun hannun dama domin nuna godiya, a wasu wurare daban kuma, idan bako yana son samun karin ti, ya kamata ya bar ti kadan cikin kofin, da mai gida ya ga haka sai ya kara wa bakon ti, amma idan bakon ya shanye ti duka da ke cikin kofin, sai mai gidan ya fahimci cewa, bakon ba ya son ci gaba da shan ti, sabo da haka ba zai kara masa ti ba. (Umaru)

Tsinken cin abinci mai sigar musamman

An ce, ya kasance da hanyoyi 3 da ake bi a duniya wajen cin abinci, wato yawanmutanen da suke daukar abinci da hannunsu kai tsaye ya kai kashe 40 bisa 100, mutanen da suke yin amfani da wuka da cokali mai yatsa don cin abinci sun kai kashi 30 bisa 100, mutanen da suke amfani da tsinken cin abinci kuma sun kai kashi 30 bisa 100.

Tsinken cin abinci wani babban abu ne da Sinawa suka kago. An fara yin amfani da tsinken cin abinci ne a daular Yin da ta Shang na kafin shekaru fiye da 3000 da suka wuce, amma a can farko sunan tsinken cin abinci ba kamar na yanzu ba wato "Kuai" ba. Bisa abubuwan da aka rubuta cikin littattafan tarihi an ce, a wancan lokaci, mutane sukan kiran shi da sunan "Zhu" ko "Jia". A karni na 6 da na 7, akan kira tsinken cin abinci da sunan "Jin". Me ya sa daga baya an canja sunansa da ya zama "Kuai"? Bisa abubuwan da aka rubuta cikin littattafan tarihi an ce, mutanen da ke kudancin kogin Yangtse na gabashin kasar Sin wadanda lafazinsu na "Zhu" wato tsinken cin abinci ya yi daidai da na "tsayawa", amma mutane masu tuka kwalle-kalle wadanda al'adarsu ta haramta musu fadar kalmar "tsayawa", sabo da haka maimakon sun ce "Zhu" sai suka ba shi sunan "Kuai" wato da sauri ke nan. Zuwa daular Song na karni na 10 kuma mutane sun kara kalmar "gora" a kan "Kuai" wajen rubuto, dalilin da ya sa suka yi haka shi ne sabo da yawancin tsinkayen cin abinci wadanda aka yi su ne da gora. Sabo da haka, irin wannan kayan cin abinci da Sinawa suka kago yana da sunan "Kuai" kamar yanzu na sanin kowa.

Ta yaya aka kago tsinken cin abinci? Wasu mutane sun yi tsammani cewa, a can can da, yayin da mutanen zamanin da suke gasa nama, sukan tsinke rassan itace guda 2 don yin amfani da su wajen daukan abinci su ci, ta yin haka ba za su ji zafi a hannunsu ba sabo da wuta, kuma sun iya cin abinci mai zafi, da haka ne aka samu tsinken cin abinci. Kasafin tsinken cin abinci yana da sauki sosai. Siffarsu kamar sanduna 2 ne sirara, irin tsinken cin abinci na kasar Sin yana da kauri a sama, a kasa kuwa siriri ne, a sama kewayayyen ne, a kasa kuwa da'ira ce, irin wannan samfuri na da amfani wajen saukin dauka, ba za su kubuce daga hannun mutane ba, kuma idan an ajiye su kan tebur ba za su iya mirginawa ba, sabo da wani sashen tsinken da'ira ce kuma mai santsi, shi ya sa lokacin da ake cin abinci da su kama ba za su raunana leben mutum ba. Bayan da tsinken cin abinci ya barbazu zuwa Japan, sai Japannawa su gyara siffarsu da ta zama kamar mazugi, dalilin da ya sa suka yi haka shi ne, sabo da sukan cin abincin da ba a dafa ba, kamar kifi da ake kira Sashimi, idan an ci irin wadannan abin da irin wanna tsinke, sai a sami sauki kwarai.

Ko da yake tsinken cin abinci yana da sauki, amma Sinawa sun mai da muhimmanci kuma sun yi ayyuka da yawa kan inganci da abubuwan ado na tsinken. Tun kafin shekaru fiye da 2000 da suka wuce ma da akwai tsinken cin abinci da aka yi da hauran giwa da kuma tagulla. Tun karni na 6 da na 7 zuwa yanzu, fadar sarakunan gargajiya da na jami'an gwamnati da iyalan masu arziki sukan yi tsinken cin abinci da ziyariya da azurfa, kuma sukan yi amfani da sakakkun lu'u-lu'u da murjani don kayatar da tsinken. Kuma an sanya azurfa a kawunan wasu tsinkaye don duba ko akwai dafi a cikin abinci, idan akwai guba cikin abincin, sai azurfa da ke kan tsinken ta canja launinta ta zama baki ko kore.

Tsinken cin abinci ya taka muhimmiyar rawa cikin al'adun gargajiya na Sinawa. A wasu wurare, lokacin da amarya ta je gidan ango, cikin kayan gara da aka shirya tabbas ne akwai tsinken ci abinci da kwanoni 2 wadanda ake daure su da jan igiya musamman domin ango da amryasa, wadanda kuma ake kiransu "kwanonin zuriyar nan gaba", wannan ba ma kawai ya nuna cewa, daga nan ne ango da amryarsa za su fara yin zaman tare ba, kuma lafazin "Kuai" wato tsinken cin abinci ya yi daidai da "sauri", wato ana fatan "za su haifi jariri da sauri". A kauyukan arewancin kasar Sin kuma akwai irin wannan al'ada wato a duk lokutan da ake yin zolaya a ranar bikin aure da dare, dangogi da aminai na ango da amaryarsa sukan jefa wasu tsinkayen cin abinci cikin dakin aure ta tagar dakin, wannan yana alamta zaman alheri da haihuwa jariri tun da wuri. Ko da yake tsinken cin abinci kananan sanduna ne guda 2 sirara kawai, amma idan ana son yin amfani da su cikin daidaici sosai wajen abinci, ya kamata a yi matukar kokari.

Fasahar da Sinawa suke nunawa wajen yin amfani da tsinken cin abinci ta kan jawo hankulan mutanen kasashen waje, a kasashen yamma har ma an kafa "cibiyar yin horo" ta musamman don koyar wa mutane dabarar yin amfani da tsinken cin abinci. Wasu masanan likitanci sun bayyana cewa, yin amfani da tsinken cin abinci yana iya jawo motsin gabobi fiye da 30 da tsoka fiye da 50 na jikin mutun, kuma yana da amfani ga motsin yatsun hannu da wasa kwakwalwa. Kasar Sin mahafar tsinken cin abinci ce, amma an ce "ma'adanar kayayyakin tarihi ta tsinken cin abinci" ta farko ta duniya tana Jamus ne. A cikin wannan ma'adanar kayayyakin tarihi, ana nuna tsinken cin abinci a aka yi da zinariya da azurfa da lu"u-lu'u da kasusuwan dabbobi da sauran kayayyaki daban-daban har fiye da dubu 10, wadannan tsinkayen cin abinci sun zo ne daga kasashe da shiyyoyi daban-daban, kuma daga lokutan tarihi da daban-daban, lalle suna da yawan gaske. (Umaru)

Al'adar cin abinci ta Sinawa

Sinawa suna da wani karin magana cewa, magani bai yi kyau kamar abinci wajen gina lafiyar jiki ba. Wannan ya bayyana cewa, a lokacin da ake kiwon lafiya da kasancewa cikin koshin lafiya, ya kamata a mai da hankali kan tsarin abinci, ko da yake wasu mutane suna shan wahala wajen tattalin arziki, amma suna iyakacin kokari domin shirya abinci da kyau, mutane masu arziki kuma suna kara mai da muhimmanci kan ingancin abinci. Sabo da haka, a kwana a tashi aikace-aikacen yin abinci sun barbazu cikin fannoni daban-daban na zaman rayuwar jama'a, har an bullo da al'adar abinci ta nuna ladabin da ake yi cikin zaman al'umma, da ta bikin sabuwar shekara da na sauran bukukuwa, da al'adar abinci ta addanai, da ta bikin aure da ta jana'iza, da ta bikin haihuwar mutane ko haihuwar jarirai.

Al'adar abincin nuna ladabin da ake yi cikin zaman al'umma ta bayyanu musamman a fannin mu'amalar da ake yi tsakanin mutum da mutum. Kuma ta fi bayyanuwa wajen mu'amalar da ake yi tsakanin dangi da aminai, a duk lokutan da dangi da aminai suka gamu da manyan al'amura, kamar haihuwar jariri da yin kaura, sukan ba da abubuwan kyauta, a lokacin kuwa, da farko mai gida yakan yi tunani cewa, wadanne irin abinci da kayan shaye-shaye zai shirya domin baki? Zai yi matukar kokari domin shirya abinci da ganyaye da yawa, ta yadda baki za su ji dadi. Ban da wannan kuma mutane suna sabawa da yin tallace-tallace a lokacin da suke cin abinci, suna cin abinci suna yin tayi, bayan da suka gama cin abinci kuma sun sa aya ga yin ciniki a tsakaninsu.

Sabo da al'adun wurare daban-daban sun sha bambam, shi ya sa abinci da ganyaye da aka shirya domin baki su ma sun sha bambam. A zamanin da a birnin Beijing, akan shirya taliya domin baki, ma'anarsa shi ne domin rokon baki da su kwana a gidansa, idan bakin sun yarda, sai mai gida yakan shirya wa baki Jiaozidon su ci, an yi haka ne don nuna karfin gwiwa. Lokacin da ake yin bakunci gidan dangi ko kai ziyara a wajen aminai, akan kai musu kyautar "abinci iri 8", wato kayan zaki iri 8. a wasu kauyukan kudancin kasar Sin, idan baki sun zo, da farko mai gida yakan shirya ti don su sha, daga baya sai ya shiga dakin girki don yin kayan zaki ko dafa wasu kwayaye, kuma ya sa sukari a ciki, ko kuma da farko ya dafa wasu gutsurarrun cake na sabuwar shekara, kuma ya sa sukari a ciki, sa'an nan kuma ya dafa abincin da aka saba ci.

A birnin Quanzhou na lardin Fujian da ke gabashin kasar Sin, akan gayyaci baki don cin 'yan'yan itatuwa da ake kira "Tiantian", wato dandana 'ya'yan itatuwa masu zaki, wadanda a ciki ba a rasa lemon zaki da tanjarin ba, dalilin da ya sa a yi haka shi ne, sabo da lafazin "lemo" ya yi daidai da na "alheri" a wurin, an yi haka domin fatan samun alheri ga baki, wato zaman rayuwarsu ya yi zaki kamar lemo.

Hanyoyin da ake bi a wurare daban-daban kan liyafar da aka shirya domin baki su ma sun sha bambam. A birnin Beijing a kalla akan shirya abincin ganyaye da nama na Dish wato tasoshi 8 na abinci masu sanyi da na kwanoni 8 masu zafi. A lardin Heilongjiang da ke arewancin kasar Sin, yawan ire-iren abincin da aka shirya domin baki dole ne ya zama lambobin da biyu ke iya shiga cikin su, wato kowane irin abincin da aka shirya yawansu ma ya yi haka. Ban da wannan kuma, a wasu wurare dole ne a dafa kifi, ma'anarsa shi ne za a samu rarar kudi cikin zaman rayuwa. Daya daga cikin ire-iren liyafar da ake fi ganin su cikin zaman yau da kullum su ne bukukuwan cin abinci iri daban-daban da aka shirya sabo da yin aure. Cikin bukukuwan da ake yi domin yin aure, akan shirya abincin gabatar da alkawarin aure, da abincin gani da kuma kiyasta cancantar abokin zama na nan gaba, da liyafar aure, da abincin da aka shirya yayin da amarya ta ziyarci iyalinta tare da ango. Daga cikin su liyafar aure ta fi kasaita. Alal misali, a wasu wuraren lardin Shanxi da ke yammacin kasar Sin, kowane irin abincin da aka shirya a gun liyafar yana da ma'ana. Abinci na farko shi ne nama mai launin ja, ma'anarsa ita ce "iyali yana cike da murna da fara'a", abinci na 2 sunansa "Quanjiafu", wato "duk 'yan iyali sun hadu, kuma suna more zaman alheri tare". Abinci na 3 shi ne shinkafa da aka dafa tare da abubuwa masu daraja iri 8, ciki har da shinkafa mai yauki da dabino da wani irin 'ya'yan itatuwan da ake kira Lily da 'ya'yan bado, ma'anar wannan shinkafa ita ce ango da amaryarsa za su yi zaman jituwa har su yi furfura wato har su tsufa. A gun bikin aure da aka yi a kauyukan lardin Jingsu da ke gabashin kasar, akan shirya abinci har kwanoni 16 ko 24 ko kuma 36, a cikin biranen lardin kuma akan yi bikin aure cikin gagarumin hali, duk wadannan abubuwan da aka yi suna da ma'anar samun alheri. Liyafar da aka shirya domin murnar ranar haifuwa shi ne bikin shan gara domin taya murnar ranar haifuwa ga tsofaffi, muhimmin abincin da aka shirya a gun liyafar shi ne taliya wadda ake kira taliyar tsawon rai. A birnin Hangzhou da wasu wuraren da ke arewancin lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin, akan ci taliya a rana, a dare kuma akan shirya bikin shan gara. Ya yin da mutanen Hangzhou suke cin taliya, kowane mutun yakan kwashe taliya daga kwanonsa zuwa kwanon wanda ake taya shi murnar ranar haifuwa, haka ana cewa "kara masa tsawon rai", kuma dole ne kowa ya ci taliya kwanoni 2, amma ba su cika ba, an yi tsammani cewa, im ba haka ba, ba za a samun zaman alheri ba. (Umaru)

Likitancin abinci da abincin magani

A zamani da, kasar Sin ta sami magungunan sha daga halittu, ta wannan hanya ce aka haifar da magungunan gargajiya masu halin musmman na kasar Sin. Irin wannan ilmin hada magunguna yana jibintar abincin mutane sosai. Ana iya sa magunguna cikin abinci, kuma ana iya mai da abinci da a matsayin magunguna, da haka ne aka warkar da cututtuka ta hanyar abinci wato da abincin magani, mutanen kasar Sin sukan cewa, "magani bai yi kyau kamar abinci wajen gina lafiyar jiki ba, warkar da cututtuka ta hanyar abinci ta fi ba da magani". Warkar da cututtuka ta hanyar abinci ta samu maraba sosai daga wajen jama'ar kasar Sin ko a zamanin da ko kuma a yanzu, har ta zama wani fure mai kyau da ke cikin babban lambun furannin al'adar abincin kasar Sin.

Tun daga daular Zhou wato daga shekarar 1046 wuwa ta 256 ta kafin haifuwar Annabi Isa Alaihisallam ma aka fara bayyana al'adar haduwar magani da abinci cikin tsarin yin likitanci da dafa abinci. Cikin littattafan tarihi an rubuta bayanoni da yawa game da yin likitanci ta hanyar abinci, cikin littattafai guda 2 masu sunan "Qianjinfang" da "Qianjinyifang" da Sun Simiao, likitan likitoci na daular Tang wadda aka kafa daga shekarar 618 zuwa ta 907 ya kebe shafunan musamman domin bayyana likitancin da ka yi ta hanyar abinci, wannan ya jawo babban tasiri ga bunkasa ilmin likitancin abinci na zamanin da.

Sun Simiao ya bayyana cewa, ya kamata a gina lafiyar jiki bisa harsashin abinci mai inganci, amma kada a sha magani yadda aka ga dama. Ya kamata da farko likita ya fahimci dalilin ciwon, kuma da farko ya warkar da ciwon ta hanyar abinci, idan da ba a samu sakamako mai kyau ba, sai a ba da magani. Duk hanyoyin da ake bi a kasar Sin wajen warkar da cututtuka ta hanyar abinci da daukar abinci a matsayin magani sun zo ne daga ra'ayoyin da Sun Simiao ya bayar wajen yin likitanci ta hanyar abinci.

Sun Simiao shi kansa yana da shekaru fiye da 100 a duniya, wannan hakikanin abu ya sa mutanen wancan zamani da wadanda suka zo daga baya dukkansu sun amince da hasashensa na yin likitanci ta hanyar abinci da kiwon lafiya. A kwana a tashi, yin likitanci ta hanyar abinci da daukar abinci a matsayin magani sun zama wata hanyar da jama'ar kasar Sin ke bi domin gina lafiyar jiki da yin rigakafin cututtuka da kuma warkar da su.

Likitancin abinci ma'anarsa shi ne daukar abinci a matsayin magani. A kasar Sin, akan yi amfani da ganyaye da abincin da ake ci a zaman yau da kullum domin warkar da ciwace-ciwace, wannan abun sanin kowa ne. Idan mura ta kama wani mutum cikin iyali, sai a sa wasu yankakkun citta da wasu guntun sandunan albasa , kuma a dafa su cikin ruwa tare da jan sukari, sai mai kamu da mura ya sha tun da suke zafi, kuma ya yi gumi da yawa, ba shakka zai samu sauki. Lokacin da ake kiwon lafiya a zaman yau da kullum, akan ce haka, "a hau kan gado a ci jan yalo, a sauka daga gado a ci citta", wato da safe a ci citta, da dare kuma a ci jan yalo. Jama'a suna yin binciken gishiri da bininga da citta da albasa da tafarnuwa da sauran kayan yaji kan taimakon da suke bayarwa wajen warkar da cututtuka, kuma suna ta sumun ci gaba a wannan fanni. Yanzu da akwai wasu mutanen da suke yin abin sha ta hanyar yin amfani da binninga da Coca-Cola don gina lafiyar jiki, dabarar nan ta bazu ko'ina.

Wajen yin likitanci ta hanyar abinci kuma, "abincin furanni" ya zama wani muhimmin kashi ne daga cikin su. Abin da ake kira "abincin furanni" ma'anarsa shi ne, a yi dish wato ganyen da ake ci da furanni. An fara yin irin wannan abinci ne daga lokacin Chungiu da na yake-yaken sarakuna na Zhanguo na karni na 6 zuwa na 7 na kafin bayyanuwar annabi Isa Alaihisallam, kuma ya shahara a daular Tang ta karni na 7.

Ya kasance da furanni iri-iri fiye da 1000 a kasar Sin, a arewancin kasar ma da akwai ire-iren furanni wadanda yawansu ya kai fiye da 100 wadanda kuma ake iya yin amfani da su domin dafa abinci, an ce a lardin Yunnan da ake kira "mulukiyar tsire-tsire" da ke kudu maso yammacin kasar Sin, yawan ire-iren furannin da ke iya dafa abinci da su ya kai fiye da 260.

Abincin furanni sun iya warkar da ciwace-ciwace, musamman ma ga mata, idan mata sun ci abincin furanni da yawa, yana da amfani sosai gare su. Alal misali, furen rose wanda ke alamta soyayya yana da amfani ga kara karfin jini da daidaita al'adar mata da kyautata hasken fuska da kuma gina lafiyar jiki. Idan an hada furannin Peach blossom da kifi ko jatalande don dafa abinci tare, to haka yana da amfani ga kara karfin jiki da kara kuzari, da kyautata aikin saifa da tumbi, haka ma ga kyautata hasken fuska.

Abincin magani kuwa shi ne a dauki magani a matsayin abinci, wato an warkar da ciwace-ciwace da yin rigakafin su ta hanyar abinci amma ba magani ba. Abincin magani ya barbazu daga zamanin da zuwa na yau a kasar Sin, yanzu kuma yana ta kara samun maraba daga wajen mutane, cikin abincin magani da akan ci kuma har da kunu, da abincin da aka yi da garin alkama kamar cincin da miya da abincin ganye da nama, kuma an bude dakin sayar da abincin magani na musamman. Abincin magani yana da iri daban-daban, amma dukkansu an yi su ne cikin nitsuwa, alal misali, da akwai wani irin abincin maganin da ake kira "kunun yara" wanda aka dafa da doya da kwayoyin hatsi da busassun wani irin 'ya'yan itatuwa da ake kira Shibing da kuma shinkafa, wanda kuma ake iya yin amfani da shi domin kyauta aikin saifa da tumbi na yara. Ban da wannan kuma da akwai irin abincin maganin da ake kira "romon wani irin maganin da aka samu daga lardin Sichuan na kasar Sin da busasshen bawon lemo" wanda ke iya warkar da mura da tari, da "romon ruwan gadali" wanda ke iya gina lafiyar jikin marasa lafiya da na tsofaffi.

"Dokar tsabtataccen abinci" ta kasar Sin ta tanadi cewa, , kada a shigar da magunguna cikin abinci, wannan ya saba wa abincin magani na jama'a. Domin daidaita wannan sabani, sassan da abin ya shafa sun sanar da sunayen ire-iren magungunan gargajiya na kasar Sin fiye da 10 wadanda ake iya shigar da su cikin abinci, ciki har da dabino, da busasshen citta, da wani irin 'yan'yan itatuwa mai kaushin baya, da mint.

Abincin maganin kasar Sin ba ma kawai ya shahara a cikin kasar Sin ba, har ma ya shiga cikin kasuwannin kasashen duniya. Alal misali giyar furen da ake kira Chrysanthemum, da ti din busasshen bawon lemo, da wata irin wainar da aka sa wani abu a ciki da maganin zaitun da sauran abincin magangunan kasar Sin suna nan suna ta kara shiga cikin zaman rayuwar abincin mutanen kasashen waje. (Umaru)

Abincin manyan bukukuwa 3 na kasar sin wato Yuanxiao da Zongzi da Yuebing

Halayen musamman na abincin gargajiya na kasar Sin suna ta kara bayyanuwa a bikin sabuwar shekara da sauran bukukuwa. Bikin bazara da bikin Duanwu da bikin tsakiyar yanayin kaka bukukuwa guda 3 ne mafiya muhimmanci na al'adun gargajiya na kasar Sin, abincin musamman na wadannan manyan bukukuwa 3 wato Yuanxiao da Zongzi da Yuebing sun zama abincin manyan bukukuwa 3 na kasar. To, jama'a masu karanta shafunan Internaet na Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin, yanzu za mu yi muku bayani kan abincin Yuanxiao da Zongzi da Yuebing.

Bikin sallar bazara wato bikin sabuwar shekara na kalandar kasar Sin biki ne mafi kasaita na jama'ar kasar Sin, akwai wani cikakken tsarin abinci a lokacin sallar bazara, Yuanxiao , wani irin abincin da ake ci ne a gun bikin nunin fitilu, wato ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar kasar Sin ya zama abincin karshe na sallar bazara. A wannan rana, iyalai daban-daban dukkansu kan ci Yuanxiao, amma sunan Yuanxiao ya sha bamban tsakanin kudanci da arewacin kasar Sin, wato mutanen kudancin kasar sukan kira shi da sunan "Tangyuan", kuma akwai bambanci tsakanin Tangyuan da Yuanxiao wajen fasahar yin su.

A arewacin kasar Sin, akan yi Yuanxiao ta hanyar mirginawa, hakikanan matakan da aka dauka wajen yin sa su ne, an hada sukari da ridi da gyada ko markadadden wake, kuma an gauraya su da tsinkaye har sun zama kananan kwayoyi, kuma an yayyafa ruwa kadan a kan su, sa'an nan kuma an dauki wani kwando wanda aka sa garin shinkafa mai yauki a ciki, kuma a zuba wadannan kananan kwayoyi a cikin kwandon kuma yi ta mirginawa, sai garin ya yi ta haduwa da kwayoyin, don haka kwayoyin suna ta girma har girmansu ya yi kamar kananan kwayoyi, da haka ne aka kammala aikin yin yuanxiao. Yanzu mutane suna shan aiki, ba su mirgina Yuanxiao su da kansu, amma sukan sayi Yuanxiao daga kantuna. A duk lokutan da ake yin bikin nunin fitilu, a duk tituna manya da kanana, aka gani 'yan kasuwa da suka kafa manyan kwanduna wadanda tsayin da'irarsu ya kai fiye da mita daya suna ta mirgina Yuanxiao. A nan birnin Beijing, Yuanxiao din da kantuna 2 masu dogon tarihi wato "Daoxiangcun" da "guixiangcun"ke sayarwa sun fi samun maraba daga wajen mutane.

Idan an kwatanta mutanen kudancin kadar Sin da arewacin kasar, sai a ga mutanen kudancin kasar sun fi son yin "Tangyuan" da hannunsu a gun bikin nunin fitilu. Sun hada ruwan zafi da garin shinkafa mai yauki, kuma sun cakuda garin har ya zama kamar cincin, sa'an nan kuma sun hada irin 'ya'yan itatuwa da ake kira Hetao wanda bawonsa ke da karfi da gyada da ridi da markadadden dabino da na wake kuma sun gauraya da hannayensu har sun zama kullin garin shinkafa mai yauki kamar cincin, sa'an nan kuma sun sa gutsul-gutsul a cikin su, kuma sun murda su da hannaye biyu har sun zama kulli masu santsi. Tangyuan da suka fi shahara a kudancin kasar Sin su ne, irin Tangyuan da aka yi a birnin Ningbo da ke gabashin kasar da irin "Laitanyuan" da aka yi a birnin Chengdu na lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar.

Ko Yuanxiao ko kuma Tangyuan, dukkansu ana ci ne ta hanyar dafawa cikin ruwa, suna da kamshi kuma da zaki, suna da dadin ci sosai. Lafazin Yuanxiao da Tangyuan ma'anarsu "haduwa" ce cikin Sinanci. Jama'a suna cewa haka, an ci Yuanxiao ko Tangyuan a gun bikin nunin fitilu domin samun "haduwar juna".

Ran 5 ga watan Mayu na kalandar kasar Sin ranar bikin Duanwu ne, abincin mafi muhimmanci na wannan rana shi ne Zongzi. Zongzi kuma abinci ne da aka yi da shinkafa mai yauki , kuma an nade shinkafar da kunnuwan gora da na tsaure, kuma an daure su da igiyar zare, siffarsu kamar dala mai kusurwa uku, da matashin kai ko sauran siffofi, a karshe kuma an dafa su ko turara su. Sabo da dandanon mutanen wurare daban-daban na kasar Sin sun sha bambam, shi ya sa abubuwan da aka shirya domin yin Zongzi da fasahar yin su su ma sun sha bambam. Biranen Suzhou da Jiazing da Ningbo da ke bakin kogin Yangtse na gabashin kasar Sin sun zama"jihar da ta shahara kwarai wajen noman shinkafa da aikin su", irin zongzi da aka yi a wadananan wurare suna wakiltar Zongzi na kudancin kasar, muhimman abubuwan da aka sa a cikin zongzi su ne markadadden wake da wani irin 'ya'yan itatuwa da ake kira Lizi wanda bawonsa ke da karfi da markadadden dabino da nama, amma a arewancin kasar kuma akan yi amfani da dabino da 'ya'yan itatuwa masu zaki da aka adana.

Zongzi yana da dogon tarihi bisa matsayinsa na abincin biki. Mutane sukan ce, cin abincin Zongzi a bikin Duanwu makasudinsa shi ne domin tunawa da Qu Yuang, babban mawaki mai kishin kasa na zamanin da. An ce, a karni na 3 na kafin haifuwar Annabi Isa Alaihisallam, an mamaye kasar mahaifa ta Qu Yuan, sabo da haka Qu Yuan ya yi haushi sosai, har ya tsunduma cikin ruwa ya mutu a ran 5 ga watan Mayu na kalandar kasar Sin. Daga baya, mutane sun tsai da wannan rana da ya wama bikin tunawa da Qu Yuan. A wannan rana ta kowace shekara, mutane sukan sa shinkafa mai yauki cikin fafaffiyar gora mai kauri, kuma su jefa gorar cikin kogin domin tunawa da nuna girmamawa ga Qu Yuan. Daga baya akwai almara cewar, dodannin da ke cikin kogin sun sace irin wannan abinci sun ci, sabo da haka sai mutane suka yi amfani da kunnuwan itace don kunshe fafaffiyar gora mai kauri, kuma sun daure su da igiyoyin zane masu launi, an ce dodanni sun fi jin tsoron wadannan abubuwa guda 2 wato kunnen itace da igiyar zane mai launi. A kwana a tashi, fafaffiyar gora mai kauri da ke dauke da shinkafa mai yauki ta sauya har ta zama Zongzi na yanzu.

Zongzi ba ma kawai ya zama abincin bikin Duanwu ba, kuma ya zama kyauta ce da jama'a ke ba wa junansu. A duk lokutan bikin Duanwu, mutane sukan kai ziyara a gidajen danginsu da aminansu dauke da daurin Zongzi.

Ran 15 ga watan Augusta na kalandar Kasar Sin ranar bikin tsakiyar yanayin kaka ne, a wannan rana da dare wata ya fi da'ira, sabo da haka akan kira shi da sunan "bikin haduwa". A wannan rana da dare kuma akan yi kallo da nuna ban girma ga wata, a lokacin kuwa wainar Yuebing ta zama wajibabben abinci ne ga mutane. Yuebing wata irin waina ce da aka yi da garin alkama kuma aka sa sukari da markadadden dabino da sauran abinci masu dadi a ciki. Bambancin da ke tsakanin Yuebing da sauran waina shi ne, akan buga hotuna a kansa wadanda ke bayyana abubuwan da suka faru cikin tatsuniyar "Chang'e ta tashi zuwa wata" da furanni da wata wadanda ke bayyana yanayi masu kyau da zaman jin dadin jama'a.

A ranar tsakiyar yanayin kaka da dare, yayin da wata mai da'ira ke fituwa, mutane sukan sa wainar Yuebing da 'ya'yan itatuwa iri daban-daban bisa matsayin abubuwan sadaukarwa cikin hasken wata domin nuna ladabi ga wata. Bayan haka, mutanen iyali daya sun rarraba wa junansu Yuebing sun ci, wannan ya bayyana nufinsu na neman "haduwa".

Wainar Yuebing na wurare daban-daban na kasar Sin su ma sun sha bambam, Yuebing din birnin Beijing da na Suzhou da ke gabashin kasar Sin da na Guangzhou da na Chaozhou da ke kudancin kasar sun fi shahara a kasar Sin.

Sakamakon daguwar matsayin zaman rayuwar jama'a , abubuwan da ake sa wa cikin Yuebing su ma sun sami sabbin sauye-sauye. Ban da sukari da markadadden dabino da na wake da nama da 'ya'yan bado da akan yi amfani da su a kullum, kuma an yi amfani da kwayaye masu gishri na agwagi da 'ya'yan itatuwa da kuma madarar kwakwa.

Daidai kamar sauran kayayyakin abinci domin dangi da aminai, a duk lokutan gabannin bikin tsakiyar yanayin kaka kuma akan sayar da Yuebing iri daban-daban wadanda aka kunshe su da kyau cikin kasuwanni da kantuna, wannan ya tuna da mutane cewa, "daren haduwa" tsakanin danki da aminai ya zo. (Umaru)

Abincin Jiaozi na kasar Sin

Idan an ce Jiaozi wani kashi ne na al'adun kasar Sin, wannan maganar gaskiya ce zalla. Bisa matsayinsa na wani irin abincin gargajiya na kasar Sin, idan mutanen iyali daya su da kansu suka ci, sai ya almanta haduwar iyali, idan an yi amfani da su don shagalta baki, sai ya nuna alamar girmamawa da karimci. Wani bako ya zo kasar Sin, idan bai ci Jiaozi ba, bayan da ya koma gida kila a yi masa ba'a cewa ya yi wata tafiyar banza.

A takaice dai, Jiaozi abinci ne da aka yi da garin alkama, kuma an sa gutsul-gutsul din mana da ganye a ciki, bayan haka sai a dafa su cikin tafasasshen ruwa. A da, an yi abincin nan musamman domin murnar bukukuwa, musamman ma a jajibirin sabuwar shekara ta kalandar kasar Sin, Jiaozi ya zama wajabtaccen abinci ne da iyalan Sinawa daban-daban suka ci. Cikin al'adun gargajiya na kasar Sin, da akwai tsare-tsare da yawa wajen yin abincin Jiaozi da siffarsa da kuma dabarar cin sa.

Da farko, bari mu tabo magana kan yadda aka shirya abubuwan da aka sa cikin Jiaozi. Daga cikin wadannan abubuwa har da nama da ganye, kuma akan hada nama da ganye. Aiki mafi muhimmanci da aka yi shi ne a daddatsa nama da ganye da kayan yaji bisa tsari. Lokacin da aka daddatsa nama da ganye a kan katako,akan ji muryar "Peng-Peng", wani sa'i muryar ta tashi sama wani sa'i kuma ta yi kasa-kasa, kamar ana yin wani kida mai dadi wanda ya barbazu zuwa gidajen makwabta. Dukkan mutane suna son muryar da ta fita daga iyalinsa ta fi karfi kuma ta fi tsawon lokaci. Lafazin kalmar "nama" da "ganye" na Sinanci shi ne "akwai kudi", idan wani iyali ya daddatsa nama da ganye da karfi kuma cikin tsawon lokaci, sai a ce wannan iyali yana yin Jiaozi da yawa, wato yana cikin zama mai wadata ke nan.

Bayan da aka gama daddatsa nama da ganye, sai a fara yin Jiaozi, wato an sa markadadden nama da ganye cikin kullin garin alkama, an ba da muhimmanci kan siffar Jiaozi, a yawancin wurare akan mai da shi kamar hilalin wata. Lokacin da ake yin Jiaozi, akan ninka rigar Jiaozi, haka akan ce da shi "ninka alheri" ke nan. Wasu iyalai kuma sukan hada kahonni 2 na Jiaozi gu daya, siffarsu ta yi kama da irin kudin zinariya ko na azurfa na tsohon zamanin kasar Sin, wannan ya alamanta arziki wato gidansa yana cike da zinariya da azurfa. A kauyuka kuma akan hada bakin Jiaozi kama da siffar dunkulin alkama, wannan kuma yana alamanta cewa, za a samu amfanin gona mai armashi a shekara mai zuwa.

Idan aka gama aikin yin Jiaozi, sai a dafa shi. Da farko an dafa ruwa har ruwan ya tafasa, sa'an nan an sa Jiaozi a ciki, a lokacin kuwa sai ka ji kamar an sa kayayyakin fasaha a cikin ruwa mai tsabta. Daga baya kuma akan yawaita gauraya Jiaozi don kada su kama kasar tukunya. A lokacin da aka dafa Jiaozi, akan zuba ruwan sanyi kadan cikin tukunyar har sau 3, haka ana cewa "kara samun alheri" ke nan. Bayan da aka shafe mintoci 10 zuwa 20 ana dafawa, sai Jiaozi mai dadin ci ya dafu.

A lokacin da ake cin Jiaozi kuma an tsai da dokokin gargajiya. Akan samar da kwano na farko na Jiaozi domin kakani don nuna girmamawa da tunaniya ga kakanin gare su. Kwano na 2 na Jiaozi kuma akan samar da shi ne ga dodon Zaoshen da sauran dodannin jama'a, tsofaffi kuma sukan yi addu"a suna waka kamar haka:

-- Jiaozi daya yana da kahonni 2 sirara,

dafa su da yawa cikin tukunya daya.

-- A kwashe su da koshiyar zinariya, kuma

a dauke su da kwanon azurfa.

-- A ajiye kwanon a kan tebur

domin nuna ban girma ga Allah.

-- Da dodo ya gani ya yi fara'a,

ya tabbatar da zaman lafiya a duk shekara.

Sai kwano na 3 na Jiaozi ne kawai 'yan iyali suka fara ci da kansu. Lokacin da aka ci Jiaozi ya kamata a yi kidaya, ya fi kyau yawan Jiaozi da aka ci ya zama lambobin da biyu ke iya shiga cikin su, kada ya zama lambobin da biyu ba ya iya shiga cikinsu. Wasu tsofaffi suna ci suna yin magana cewa, "ganye ya yi yawa, kudi ya yi yawa" da sauran tsofaffin maganganu. Bayan cin abinci akan ajiye tasoshi da kwanoni har da tukunyar da aka dafa Jiaozi a kan murfin tukunya, kuma dole ne a bar wasu Jiaozi da suka yi saura amma yawansu ya zama lambobin da biyu ke iya shiga cikin su, wannan ya bayyana cewa, "akwai rara a kowace shekara".

A jajibirin kowace shekara, Jiaozi yakan zama abincin dole da ake ci. Ko wadanda suke aiki ko yin karatu ko kuma yin kasuwanci a sauran wurare ma, sukan yi kokarin komawa gida don haduwa da 'yan iyalinsu. 'Yan iyali daya suna yin Jiaozi kuma suna ci tare, sun yi murnar sallah cikin halin annashuwa.

A hakika kuwa, cikin zaman yau da kullum, ban da Jiaozi yana da ma'ana wajen al'adu kuma, da akwai abubuwa da yawa da suka shafi Jiaozi sun sami sauye-sauye . Alal misali, yanzu a cikin birane, mutane ba safai sukan yi Jiaozi su da kansu ba, a duk lokatan da ake yin bukukuwa, akan sayi daskararrun Jiaozi daga babban kanti, sai a dafa a ci kawai, ko kuma 'yan iyali daya su je dakin cin abinci don cin Jiaozi tare. Ko a kauyuka ma yawan ladabin gargajiya da aka nuna wajen cin Jiaozi ma sai kara raguwa suke. (Umaru)