Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-18 20:11:32    
Za a shirya gasar karshe ta koyon Sinanci ta 'yan makaranta ta karo na biyu wato 'Gadar Sinanci' a birnin Chongqing na kasar Sin

cri

Bisa labarin da muka samu daga hedkwatar kwalejin Confucious, an ce, za a shirya gasar mataki na biyu, da kuma gasar karshe ta koyon Sinanci ta 'yan makaranta ta karo na biyu wato 'Gadar Sinanci' daga ranar 20 zuwa ranar 31 ga wata a birnin Chongqing na kasar Sin, a lokacin, 'yan makaranta 105 da suka zo daga kasashe 29 za su nuna fasahohinsu a fannonin Sinanci da al'adun Sin.

Hedkwatar kwalejin Confucious ta kaddamar da gasar koyon Sinanci ta 'yan makaranta wato 'Gadar Sinanci' ne a shekarar 2008, bisa makasudin ba wa matasa na kasashen waje karfin gwiwa wajen koyon Sinanci, da kuma sa kaimi gare su da su kara fahimtar Sinanci da al'adun kasar Sin. 'Yan makaranta da shekarunsu sun tashi 15 zuwa 20 da haihuwa, kuma harsunansu ba Sinanci ba suna iya shiga cikin gasar koyon Sinanci ta 'Gadar Sinanci', wadannan 'yan makaranta sun yi gasa a fannonin Sinanci da nuna fasahohi, za a ba 'yan makaranta da suka ci nasara damar zuwan kasar Sin domin karatu da kuma yin mu'amala.(Danladi)