Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-09 16:28:59    
Labarin garin Xuebu

cri
Zhao Juming mai shekaru 68 da haihuwa yana zaune a garin Xuebu na birnin Jintan a lardin Jiangsu na kasar Sin. A kwanan baya, ya yi farin ciki matuka saboda ya ci jarrabawar tukin mota, ya samu lasin a karshe, ko da yake ya taba shan kaye sau 2 a da. A farkon wannan shekara, ya sayi wata mota da ta kai kudin Sin yuan dubu 50 ko fiye. Ko da yake ya taba tukin tarakta da babur, amma shi ne wani sabon hannu ne wajen tukin mota, dan haka ya je koyon tukin mota a makaranta, tare kuma da sayen litattafan koyon tukin mota. A sakamakon haka, Zhao Juming ya kan je renon furanni da itatuwa a gonakinsa da rana, ya kuma yi kokarin koyon tukin mota da dare. Namijin kokarinsa ya taimake shi wajen samun lasin tare da wani sharadi na cewa, tilas ne ya yi binciken lafiyarsa a garinsa a ko wace shekara saboda ya tsufa ainun.

Game da yadda ya samu lasisinsa, a ganin Zhao Juming, wannan na da ban sha'awa sosai, inda ya ce,"Na fi tsufa a cikin dukkan wadanda suka shiga jarrabawar tukin mota. Jami'in jarrabawa ya yi mamaki saboda wani tsoho kamar ni ya nemi samun lasin. Na gaya masa cewa, na sayi wata mota, amma in babu lasin, ba zan iya tuka motata ba. A karo na 3 ne na ci jarrabawar, tare da wani sharadi na cewa, tilas ne na yi binciken lafiyata a ko wane watan Yuli a garina."

Garin Xuebu da Zhao Juming yake zaune yana da albarkatun tudu, ya shahara a matsayin garin furanni da itatuwa a lardin Jiangsu. A shekarar 2008, fadin gonakin da ake renon furanni da itatuwa a kai ya kadada 1500 a garin Xuebu, wanda ya kai kashi 30 cikin dari bisa duk fadin wannan gari. Kuma kudin sayar da furanni da itauwa da garin ya samu ya wuce yuan miliyan 200.

Zhao Juming shi ma ya zama mai hannu da shuni saboda renon furanni da itatuwa. Ya yi matukar farin ciki a sakamakon kyautatuwar zaman rayuwarsa. A hakika, a garin Xuebu, sauran 'yan garin su ma sun zama masu albarka ta hanyar renon furanni da itatuwa. Zaman rayuwarsu ya samu kyautatuwa kwarai da gaske. Zhao Juming ya gaya mana cewa,"A wasu lokuta, na iya samun yuan dubu 100 ko fiye a shekara guda. A bara, na samu yuan dubu 100 ko fiye domin sayar da kananan itatuwa. Duk garinmu, kudin shiga na sayar da kananan itatuwa ya wuce miliyan 2. Ko wane iyali na renon itatuwa. In itatuwan da muke reno sun biya bukatun kasuwanni, za mu iya samun yuan dubu 70 zuwa dubu 200. 'Yan garinmu dukkansu sun sayi motoci da kayayyaki masu aiki da wutar lantarki, sun kuma sayi sabbin gidaje."

Yanzu Zhao Juming ya kan sayi maganin kashe kwari cikin motarsa. A ganinsa, tukin mota na da dadi sosai. Inda ya ce,"Na kan tuka mota domin yin bulaguro da kuma sayen maganin kashe kwari. Sayen maganin da kuma dawowa gida na bukatar rabin awa ne kawai. Tukin mota na da dadi sosai bisa na hawan babur."

Garin Xuebu ya yi suna sosai a fannin renon furanni da itatuwa, shi ma wani muhimmin gari ne ta fuskar masana'antu. A shekarun baya, hukumar garin tana yin kokarin ganin garin Xuebu na taka rawa wajen sa kaimi kan tattalin arzikin yankin da yake ciki. Ta haka, wannan karamin gari na samun saurin ci gaban tattalin arziki. Yana kan gaba a kasar Sin a matsayin wani gari mai wadata.

Xu Luofeng tana tafiyar da wani kanti a garin Xuebu har na tsawon shekaru 20 ko fiye. Ta gaya mana ra'ayinta kan bunkasuwar tattalin arzikin garin Xuebu a shekarun baya. Tana mai cewa,"Yau da shekaru 20 da suka wuce, babu manyan gine-gine da yawa a garinmu. Sannu a hankali, manyan gine-gine sun kafu a kewayen babban ginin da muke zaune. Haka kuma, mutane sun fi son yin saye-saye. A da, sai a gabannin muhimman bukukuwa ne kawai, mutane su kan sayi kayayyakin masarufi. Yanzu sun fi son kayayyaki na babban aji."

Domin gaggauta raya garin Xuebu, hukumar garin ta dauki matakan karfafa gwiwar mazauna kauyuka su kaura zuwa garin. A shekaru 3 da suka gabata, garin Xuebu ya rubanya kokarinsa wajen gudanar da aikin gina gidaje bisa ma'aunin bai daya domin ganin mazauna garin sun yi amfani da na'urorin jin dadin jama'a na bai daya cikin yanayi mai kyau. Madam Xu ta ce,"Ga misali, hukumar garin ta tsara shirin samar da manyan gine-gine a mataki mataki bayan asibitinmu. Bayan da aka kammala gina manyan gine-gine guda 50 zuwa 60 na rukuni na farko, mutane sun zo sun gano cewa, muhalli na da kyau a nan, kuma ko wane iyali na da wani lambu. Dan haka, mutane da yawa sun yi shirin sayen manyan gine-gine na rukuni na 2. A sakamakon samun kudi da yawa, mutane suna neman kyautata wuraren kwana. Manyan gine-gine na rukuni na 2 ba su ishe su ba, ta haka an gina manyan gine-gine na rukuni na 3."

Aikin raya kananan garuruwa ya sa kaimi kan bunkasuwar zaman al'umma a garin Xuebu daga dukkan fannoni. A shekarun baya da suka wuce, hukumar Xuebu ta yi ta kyautata hidimar kiwon lafiya, ta inganta karfinta na tabbatar da lafiyar mutane. Yanzu dukkan mazauna garin sun sayi inshorar kiwon lafiya. Ko wane manomi na bukatar biyan yuan 10 ne kawai a ko wace shekara domin kiwon lafiyarsa, sun ci gajiya da yawa.

Game da wannan, Zhao Juming ya nuna mana ra'ayinsa da cewa,"A ko wace shekara, muna sayen inshorar kiwon lafiya. Baya ga kudin da hukumar kauyenmu ta kan bayar, mu manoma mun biya yuan 10 ne kawai a shekarar bara. Mun iya samun kashi 50 cikin dari na kudin da muka kashe domin ganin likita daga asibitin garin Xuebu bisa rasidi kan kudin. Wannan yana da kyau matuka. Musamman ma in mun kamu da tsananin ciwo. Ko wanenmu na da katin sayen inshorar kiwon lafiya."

Chen Xiwen, wani jami'in kasar Sin mai kula da harkokin kauyuka ya yi bayani da cewa,"A nan kasar Sin, tilas ne a bi hanyar raya garuruwa mai halin musamman na kasar Sin, wato a tabbatar da raya birane manya da kanana da kananan garuruwa tare yadda ya kamata. A ganina, muhimmin dalilin da ya sa muka tsara wannan manufa shi ne kasar Sin wata kasa ce mai yawan mutane, tsugunar da manoma a birane kawai bai dace da hakikanin halin da kasarmu take ciki ba, dan haka raya kananan garuruwa na da matukar muhimmanci ga kasarmu ta Sin."

A halin yanzu, akwai kananan garuruwa dubu 18 a nan kasar Sin. A matsayinsa na wani bangare na manyan tsare-tsare dangane da sa kaimi kan raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa a kauyuka, babu tantama bunkasa kananan garuruwa na da muhimmiyar ma'ana ta fuskar sa kaimi kan raya biranen kasar Sin. Duk da haka, kasar Sin ba ta samu daidaituwa wajen raya tattalin arzikin yankuna ba, ana samun babban gibi a tsakanin kananan garuruwan da ke a yankin yammaci da na tsakiyar kasar Sin, kuma baya-baya ne suke ciki, da wadanda suke cikin yankuna masu ci gaban tattalin arziki a gabashin kasar Sin, shi ya sa kasar Sin take fuskantar jan aiki wajen raya kananan garuruwa.(Tasallah)