Mista Wu ya bayyana cewa, babu tantama ba za a iya canza babbar manufar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka a fannin tattaln arziki da cinikayya ba sabili da akwai hujjoji biyu, wato hujja ta farko ita ce, kasashen biyu suna cuda-bayan-juna bisa rinjayen da kowanensu ke da shi a fannin tattalin arziki; Hujja ta biyu ita ce akwai ingantaccen tushe na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Domin tinkarar matsalar hada-hadar kudi ta kasashen duniya, kasar Sin tana aiwatar da manufofi masu sassauci game da harkokin kudi yayin da ta fito da wassu jerin shirye-shirye na habaka bukatun cikin gida da na zaburar da tattalin arziki; A nata bangaren, gwamnatin Amuka ita ma ta dauki wasu tsauraran matakai na ciccibo tattalin arziki. Mista Wu Bangguo ya kara da cewa: " Bisa halin ake ciki yanzu, wajibi ne kasashen biyu su nace ga bin ka'idar yin cinikayya cikin 'yanci a kokarin magance ra'ayoyi iri daban-daban na bada kariya ga cinikayya". ( Sani Wang) 1 2 3
|