Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 22:06:09    
Bayani kan bukin Gexu a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin

cri

To, menene asalin bukin Gexu? Ina dalilin da ya sa aka ware ranar 3 ga watan Maris na kowace shekara don ta zamanto bukin Gexu? Qin Heng ya gayawa wakilinmu wata tatsuniya, inda ya ce:"Tun fil azal, akwai saurayi da budurwa, wadanda suka kasance sanannun mawaka. Su kan rera wakoki don nunawa juna soyayya da kauna. Amma tsohon tsarin zamantakewar al'umma ya haramta musu yin aure. Daga baya saurayin da budurwar sun kashe kansu domin bayyanawa juna soyayya. Don haka ne, mutane su kan shirya bukin kade-kade a ranar 3 ga watan Maris na kowace shekara, domin tunawa da soyayya da kaunar dake tsakanin saurayin da budurwar."

Masu saurare, a ranar 3 ga watan Maris na kowace shekara, wato ranar bukin Gexu, 'yan kabilar Zhuang dake zaune a gundumar Wuming su kan shirya abinci iri-iri masu dadin-ci, ciki kuwa har da shinkafa, da kaza, da agwagwa, da kifi, domin murnar bukin tare. Da maraicen ranar, 'yan kabilar su kan taru a kan tudu, ko a dandali, ko kuma a wurin dake dab da kogi, inda su kan rerawa juna wakoki. A wasu yankuna kuma, a kan yi irin wannan bukin rerawa juna wakoki ba dare ba rana har na tsawon kwanaki 3. 'Yar kabilar Zhuang dake zaune a wurin, Huang Xiao ta ce:"Wakokin da mu kan rera suna shafar fannoni daban-daban, ciki kuwa har da ilimin taurari, da labarin kasa, da ayyukan gona, gami da soyayya da kauna, da dai sauransu."

Qin Heng ya ce, rerawa juna wakoki da 'yan kabilar Zhuang su kan yi na da dadadden tarihi, kuma a kan rera wakokin ta hanyoyi daban-daban. Qin Heng ya ce:"Wakokin da 'yan kabilar Zhuang su kan rera na da salon musamman irin na kananan kabilu, wadanda suke shafar fannoni da dama, ciki kuwa har da zaman rayuwar jama'a, da harkokin tarihi, da soyayya, da kauna da dai sauran makamantansu."

1 2 3