Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 17:48:44    
Tsohon dan majalisar NPC ta nuna yabo sosai da gwamnatin Sin ke sa muhimmanci sosai kan aikin jin dadin zaman rayuwar jama'a

cri
Yau wato ran 13 ga wata da safe, an kammala taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC. Yayin da nake yin hira tare da tsoffin 'yan majalisar, sun nuna yabo sosai da gwamnatin Sin ke sa muhimmanci kan aikin jin dadin zaman rayuwar jama'a.

Manjo-Janar Li Chunhe, tsohon dan majalisar NPC ya bayyana cewa,

"za a kebe kudaden Sin wato Yuan biliyan 4000 domin sa kaimi ga tattalin arziki, kuma bisa fannoni da ayyukan da za a kebe kudade a ciki, za a iya gano cewa, dukkan wadannan ayyuka suna da nasaba da muradun jama'a da kuma bunkatun jama'a, kamar gudanar da ayyukan ban ruwa da shimfida hanyoyin mota da hanyar dogo da dai sauransu, duk wadanda za su amfana da zuriyoyi sosai. Ban da wannan kuma za a gudanar da ayyukan kiwon lafiya da na inshorar tsoffi da kuma na kara yawan kudaden da manoma ke samu, duk wadannan ayyuka sun shafe muradun jama'a, bisa burin da ayyukan za su cimma, ana iya gano cewa, lalle gwamnatin kasar Sin tana lura da fararen hula sosai.".

Game da taimakon da gwamnatin kasar Sin ke samar ga manoma, Manjo-Janar Li ya nuna amincewa sosai a kansa. ya ce,

"Yanzu ba kawai an soke kudin haraji da manoma suka biya ba, har ma an bai wa manoma kudin taimako wajen ayyukan gona, wanda ya samu amincewa sosai daga manoma. Ban da wannan kuma game da tsoffin da ke fama da talauci a kauyuka, gwamnatin ta ba su kwal don dumama daki da kuma kudin taimako Yuan 2000 ko 3000 a ko wane lokacin hunturu, ta yadda zaman rayuwarsu ya samu kyautatuwa."