Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 17:20:58    
ya kamata a habaka bukatun kasuwannin gida domin tinkarar matsalar kudi

cri

A ran 5 ga wata da yamma, 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kai ta kasar sun tattauna kan rahoton aiki na gwamnatin kasar da firayim minista Wen Jiabao ya bayar a ran nan da safe, inda dimbin 'yan majalisar suke ganin cewa, ko da yake matsalar kudi ta duniya ta kawo illa ga tattalin arzikin jihar Xinjiang, amma a waje daya kuma ta samar da wata dama wajen ci gaba da samun bunkasuwa, wato hakaba bukatun gida.

Wang Lequang, dan majalisar kuma babban darakta na jihar Xinjiang ya bayyana cewa, "Dalilin da ya sa muka tsai da kuduri kan hakaba bukatun gida a cikin wannan halin da muke ciki yanzu shi ne sabo da muna da babbar kasuwa, muna bukatar gudanar da dimbin ayyuka wadanda su muhimman ayyuka ne da ke da nasaba da bunkasuwar kasarmu cikin dogon lokaci. shi ya sa hakaba bukatun gida domin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki na dace da halin da kasarmu ke ciki yanzu. Ban da wannan kuma muna fatan za mu iya yin amafani da dimbin albarkatun duniya, amma dole ne muna da karfin da ke iya tabbatar da gudanar da tattalin arzikinmu yadda ya kamata, in ba haka ba, to za mu fi saukin samun cikas wajen bunkasuwa sakamakon sauran abubuwa."(Kande Gao)