Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:19:32    
Ya kamata a ci gaba da mai da hankali kan batun jin dadin zaman rayuwar jama'a a sabuwar shekara

cri
A ran 9 ga wata da yamma, 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na jihar Xinjiang mai cin gashin kai sun tattauna kan rahoton aiki na majalisar wakilan jama'ar Sin da shugaban majalisar Wu Bangguo ya yi a ran nan da safe, inda suka amince da rahoton sosai, kuma sun nuna yabo sosai da majalisar wakilan jama'ar Sin ta mayar da batun jin dadin zaman rayuwar jama'a a gaban kome.

Ma Dengfeng, shugaban zaunannen kwamiti mai kula da harkokin majalisar wakilan jama'a ta yankin Changji na jihar Xinjiang ya bayyana cewa, rahoton ya tsaya tsayin daka kan mayar da dan Adam a gaban kome, da kyautata batutuwan da ke da nasaba da jin dadin jama'a, hakan ya nuna cewa, hakkin jama'a yana gaban kome, kuma majalisar za ta gudanar da ayyuka a zo a gani don jama'a. Kuma ya kara da cewa,"Sabo da a cikin kundin tsarin mulkin kasar Sin, an tanadi cewa, hakkin jama'a na gaban kome, shi ya sa ya kamata dukkan ayyukan da majalisar ke gudanarwa su mai da hankali kan muradun jama'a. Bisa wannan makasudin majalisar, a shekara ta 2008 majalisar ta sa muhimmanci sosai kan ingancin abinci da kare yara da aikin koyarwa da samar da guraban aikin yi da kuma ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a da dai sauransu, kuma sun samu kyakkyawan samamako. Haka kuma a shekara ta 2009, majalisar za ta sa ido kan batutuwan da ke da nasaba da jin dadin jama'a, kamar shigad da batun kafa tsarin ba da tabbaci ga zaman al'umma a kauyuka da sa kaimi ga samun guraban aikin yi da farfado da tattalin arziki bayan girgizar kasa da kuma ingancin abinci da dai sauransu a cikin shirin majalisar."