Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 15:35:54    
Shugaban kasar Guinea ya halaka sakamakon harin da aka kai masa

cri
A ran 2 ga wata da sassafe, shugaban kasar Guinea Bissau, Joao Bernardo Vieira ya halaka a sakamakon harin da aka kai masa, wanda ya biyo bayan kisan babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar, Batista Tagme Na Waie, a ranar da ta wuce. Kisan dai ya tsunduma kasar baki daya cikin halin dar-dar.

Ana ganin Waie da Vieira a matsayin abokin gaba ga juna a fagen siyasa, kuma kafin wannan, sau da dama ma ne suka tsira da rayukansu daga yunkurin kisan gillar da aka yi musu. Harin da ya fi kusa ya faru ne a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, wato lokacin da sojoji suka kai hari ga gidan Vieira, kuma daga karshe, 'yan gadinsa suka kori masu hari. A sa'i daya, Waie shi ma ya sha hare-hare, kuma a fili ne ya yi suka cewa, shugaba Vieira ne ya ba da umurnin hare-haren a bayan idon jama'a.

Yanzu ba a tabbata yadda harin ya faru ba tukuna. Akwai labarin da ke cewa, a ran 2 ga wata da sassafe, an kai hari ga gidan shugaba Vieira, kuma a yayin da Vieira ke neman tsira daga gidansa cikin mota, an harbe shi har lahira, kuma direbansa ma ya mutu. Akwai kuma kafofin yada labarai da ke ganin cewa, kashe shugaba Vieira da aka yi ya kasance ramuwar gayya ga kisan Waie, wato hafsan hafsoshin sojojin kasar, wanda ake ganin shugaba Vieira ne ya ba da umurnin kisansa. Amma sanarwar da kakakin bangaren soja ya bayar a ran 2 ga wata, ta musanta cewa, wasu tsirarrun sojojin da ba a tabbatar da asalinsu ne suka kashe shugaba Vieira, kuma yanzu bangaren soja na bin inda suka tafi.

Da kakkausar murya ce kasashen duniya suka yi Allah wadai da kashe Vieira da Waie da aka yi. Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya yi kira ga hukumar Guinea Bissau da ta bi bahasin al'amarin, kuma ta hukunta masu laifi, ya kuma yi kira ga bangarorin kasar da su kiyaye tsarin mulki da kuma mutunta dokoki a wannan lokaci na musamman, sa'an nan su yi kokari tare da kasashen duniya don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Sai kuma shugaban kungiyar tarayyar Afirka, Jean Ping ya bayar da sanarwar cewa, kisan gilla aiki ne na matsorata, kuma majalisar zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afirka za ta kira taron gaggawa don tattauna yadda za a daidaita halin da ake ciki. A ran 2 ga wata, kungiyar ECOWAS ita ma ta bayar da sanarwa, inda ta yi Allah wadai da kisan Vieira da Waie, kuma ta nemi sashen tsaron Guinea Bissau da ya dauki matakai, don hana tabarbarewar halin da ake ciki, bayan haka, ta kuma sanar da tura tawagar sulhu zuwa kasar ta Guinea Bissau.

A ran 2 ga wata, bangaren sojan Guinea Bissau ya bayyana cewa, ba su ta da juyin mulki ba, kuma za su mutunta mulkin fararen hula da kuma dokokin kasa. Amma a ganin Dr. Kabiru Mato da ke sashen ilmin siyasa na jami'ar Abuja ta Nijeriya, bangaren soja ba zai amince da ta da juyin mulki ba, sabo da hakan zai mayar da su saniyar ware, har ma zai iya janyo musu takunkumi daga kasashen duniya, yanzu sai a zura ido ga matakin da zai dauka a nan gaba.

A yanzu haka dai, hankali ya kwanta a Guinea Bissau, amma ba a iya kyautata zato ga makomarta. Guinea Bissau ta kasance zango da masu fataucin miyagun kwayoyi na kudancin Amurka ke yada wajen jigilar miyagun kwayoyi zuwa Turai, a halin da ake ciki yanzu a kasar, mai yiwuwa ne masu fataucin miyagun kwayoyi za su kara bi ta kasar zuwa Turai. A sa'i daya kuma, akwai kafofin yada labarai da ke nuna damuwa da aukuwar babban hargitsi a tsakanin magoya bayan Waie da Vieira cikin rundunar soja. A ganin Dr.Kabiru Mato, abin da ya fi muhimmanci shi ne bangaren soja ya cika alkawarinsa, ya mutunta dokokin kasa, kuma ya kafa gwamnatin da ke wakiltar jama'a baki daya, don maido da doka da oda a kasar. A game da wannan, kamata ya yi tarayyar Afirka da ECOWAS su taka rawar sa ido.(Lubabatu)