Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-02 19:21:05    
Shiyyar Pinggu ta birnin Beijing tana kokarin jawo manyan kamfanonin duniya da su kafa hedkwatocinsu a shiyyar

cri

Shiyyar Pinggu tana arewa maso gabashin birnin Beijing, inda take da tazarar kilomita 70 da cikin garin birnin Beijing, kuma take da nisan kilomita 90 da cikin garin na birnin Tianjin. Yanzu ana kara saurin samar da ayyukan yau da kullum da kyawawan manufofi domin kokarin jawo manyan kamfanonin duniya da su kafa hedikwatocinsu a shiyyar Pinggu ta birnin Beijing. Yanzu kamfanonin da suka kafa hedkwatocinsu a shiyyar Pinggu sun hada da kamfanoni 500 da suka fi girma a duk duniya da wasu manyan da matsakaitan kamfanoni wadanda suke aiwatar da harkokinsu a duk fadin duniya.

Sakamakon kakkafa hedkwatocin kamfanoni daban daban a wani wuri, wadannan hedkwatoci suna sa kaimi sosai ga cigaban tattalin arzikin wurin. Sabo da haka, ana kiran irin wannan alama cewa "hedikwatar tattalin arzikin". Irin wannan hedikwatar tattalin arzikin za ta iya taka muhiyyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin wurin da suke ciki. Mr. Zhao Hong, shugaban hukumar nazarin tattalin arziki ta cibiyar nazarin zaman al'ummar birnin Beijing yana ganin cewa, "Idan an kafa hedkwatoci a wuri daya, za a iya yin namijin kokarin biyan bukatun da suke nema. A waje daya kuma, idan an sanya masana'antunsu ko sassansu a sauran wurare, za a iya yin amfani da albarkatun halittu na wancan wuri. Sakamakon haka, za a iya yin amfani da albarkatun halittu kamar yadda ake fata domin raya tattalin arzikin kamfanoni da masana'antu. Irin wannan hanyar raya tattalin arziki ita ce 'hedikwatar tattalin arikin'. Hedikwata tattalin arzikin wata hanya ce wajen cigaban tattalin arzikin birane."

Yanzu a cikin manyan biranen kasar Sin, farashin gidaje da na ofisoshi ya yi tsada. Ana kuma da matsalar cunkoson fannin zirga-zirga. Sabo da haka, idan an kafa hedkwatocin kamfanoni a cikin gari na wani babban birni, kamfanoni za su kashe karin kudade. Amma idan an kafa hedkwatocin kamfanoni a karkarar babban birni, ba ma kawai kamfanoni za su iya tsimin kadaden da za su kashe ba, hatta ma za su iya yin amfani da albarkatun wurin da kyau. Kamfanoni za su iya samun cigaban da suke fata cikin sauri. A waje daya kuma, wurin da aka kafa hedkwatocin kamfanoni ma za su iya samun karin haraji da samar da guraban aikin yi da dai sauransu.

Masana sun nuna cewa, a cikin shekaru 30 da suka gabata, kasar Sin ta samu cigaba sosai a fannin sana'o'in kere-kere, amma ya kasance da matsalar ba a samu cigaba cikin daidaito ba a tsakanin yankuna daban daban. Idan an raya hedikwatar tattalin arzikin a babban birni, kuma an kafa sansanin masana'antunsu a wuraren da za a iya samar da yankuna da 'yan kwadago masu arha, ba ma kawai za a iya raya masana'antu cikin sauri ba, hatta ma za a iya bunkasa birane matsakaita da kanana. Kuma wurare daban daban za su iya yin amfani da sharuda masu gatanci a fannin tattalin arziki, kuma za su iya kara yin hadin guiwa domin neman cigaba tare. Mr. Zhao Hong ya ce, "Sabo da kasancewar bambanci a tsakanin yankuna daban daban, za mu iya yin amfani da hanyar raya 'tattalin arzikin hedkwata' domin morewar sharudansu masu gatanci. A manyan birane, za a iya raya 'hedikwatar tattalin arzikin', kuma za a iya kafa sansanonin masana'antu a matsakaita ko kananan birane. Sakamakon haka, za a iya hada kan irin wadannan wurare biyu bisa tsarin kasuwanci, kuma za a iya raya su tare."

Ba ma kawai kamfanoni za su iya kara saurin daidaita harkokinsu da sa kaimi ga cigaban tattalin arziki a tsakanin shiyya shiyya ba, hatta ma irin wanann 'hedikwatar tattalin arzikin' za ta iya daidaita da kuma kyautata tsarin masana'antu na shiyya-shiyya. Musamman idan an kwatanta shi da sansanin masana'antun kere-kere, 'hedikwatar tattalin arzikin' za ta fi tabbatar da ingancin muhalli da yin tsimin makamashi.

Shiyyar Pinggu tana da sharuda masu inganci da ba safai ake ganinsu a sauran wurare ba. Ya kasance tamkar shiyyar tabbatar da yanayi mai daukar sauti ta birnin Beijing, wato babban birnin kasar Sin, shiyyar Pinggu shiyya wadda take arewa maso gabashin birnin Beijing shiyya ce da ke tabbatar da ingancin muhallin Beijing, ita kuma shiyya ce mai abin koyi wadda take matsayin kasar wajen tabbatar da yanayi mai daukar sauti. Wannan shiyya tana da kyan gani, kuma ana iya jin dadin yanayinta. Yawan bishiyoyin da aka dasa a shiyyar ya kai kashi 63 cikin kashi dari. Mr. Qiu Shuiping, shugaban gwamnatin shiyyar ya ce, "Shiyyar Pinggu tana da tsaunuka masu kyaun gani da ruwa mai dadin sha da kuma kyakkyawan yanayi mai daukar sauti. Za su iya biyan bukatun da manyan kamfanoni suke nema domin kafa hedkwatocinsu a wata shiyyar da ke da yanayi mai daukar sauti."

Bugu da kari kuma, idan an tuka mota daga shiyyar Pinggu zuwa cikin garin birnin Beijing, ana bukatar mitoci 35 kawai, kuma ana bukatar mintoci 20 kawai daga shiyyar zuwa filin saukar jiragen sama na Beijing, kuma ana bukatar kimanin sa'a 1 daga shiyyar zuwa birnin Tianjin. Bugu da kari kuma, akwai hukumar kwastan da unguwar 'yancin harajin kwastan da tashar jirgin kasa a shiyyar Pinggu. Sabo da haka, za a iya yin tsimin kudaden sufurin kayayyaki. Sannan, ana da tsarin yanar gizo ta zamani da zai iya biya bukatun da hedkwatocin kamfanoni suke nema. Haka kuma, yanzu gwamnatin shiyyar Pinggu tana kokarin raya unguwar hedkwatocin kamfanoni inda ke da yanayi mai daukar sauti. Alal misali, ana da shirin samar da ayyuka, inda za a iya yin tarurruka. Kuma za a iya samar da sabon makamashi mai tsabta ga hedkwatocin kamfanoni. Mr. Qiu Shuiping, shugaban shiyyar Pinggu ya ce, "Za a iya samun kyawawan ofisoshi da nagartattun 'yan kwadago kamar yadda ake samu a cikin garin da zirga-zirgar mai sauki a shiyyar Pinggu. Bugu da kari kuma, za a iya shan iska mai tsabta kuma mai kyan gani lokacin da ake aiki a hedkwatocin da ke shiyyarmu. Ma'aikatan kamfanonin duniya za su iya yin aiki a cikin yanayi mai tsabta, kuma kamfanoninsu za su iya samun cigaba a cikin yanayi mai daukar sauti."

Muhimmin aikin da kamfanin samar da wutar lantarki na Longji yake yi shi ne yana zuba jari, kuma yana tafiyar da masana'antar samar da wutar lantarki inda ake amfani da kayayyakin halittu domin samun wutar lantarki. Tun daga lokacin da aka kafa wannan kamfani a watan Janairu na shekara ta 2004, an kafa hedkwatarsa a shiyyar Pinggu. Ya zuwa yanzu, jimlar kudaden kadarorin wannan kamfani ta riga ta kai kudin RMB yuan biliyan 10 tare da ma'aikata dubu 4 da dari biyu. Mr. Jiang Dalong wanda ke tafiyar da wannan kamfani ya kan bayyana cewa, an sa hedkwatar kamfanin a shiyyar Pinggu, za a iya rage kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin kamfani, kuma ana da ingancin iska da yanayi mai daukar sauti a shiyyar. Mr. Jiang Dalong ya ce, "Ni da dukkan shugabannin kamfaninmu suna tsammani cewa, shiyyar Pinggu wuri ne mai armashi. Kuma wuri ne da ke cike da bishiyoyi a gabashin birnin Beijing. Sannan, ana da tsarin zirga-zirga mai sauki a shiyyar. Bugu da kari kuma, shugabannin gwamnatin shiyyar suna daidaita harkoki bisa hakikanin halin da ake ciki. Fararen hula ma suna da kirki kwarai. A ganinmu, shiyyar Pinggu, wani wuri ne da ake jin dadin zama da yin aiki."

Shiyyar Pinggu shiyya ce ta farko a cikin dukkan shiyyoyi kusan 20 na birnin Beijing da ta tsara shirin raya tattalin arzikin hedkwatocin kamfanoni. Yanzu, ana kara saurin raya shiyyar dan ta zama wani ni'imtaccen wurin shan iska domin jawo manyan kamfanoni na gida da na waje su kafa hedkwatocinsu a shiyyar. (Sanusi Chen)