Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-01 19:29:39    
Yara na kabilar Uygur ta jihar Xinjiang da ke nan birnin Beijing

cri
A shekaru biyu da suka wuce, yara 20 da shekarunsu na haihuwa ya kai 14 ko 15 na kabilar Uygur ta jihar Xinjiang, suna cike da kyakkyawan fatan samun ilmi a fannin al'adu da fasahohi, sun zo nan birnin Beijing, don fara karatu da zaman rayuwarsu a birnin. Nan da shekaru 2 da suka wuce, yadda zaman rayuwarsu ya ke a yanzu? Kuma wane irin sakamako ne da suka samu a Beijing? Tare da wadannan tambayoyi, wakilinmu ya tafi makarantar da wadannan yara ke karatu a ciki, wato makarantar koyon sana'o'in al'adu da fasahohi na al'umma ta birnin Beijing, don yin ziyara.

A gaban kofar wani ajin da ake kira "Ajin hadin kan al'umma", ana iya jin muryar karanta littafi, ciki har ma ana iya jin fatan samun ilmi da wadannan yara suke yi. Wannan makarantar sana'o'in al'adu da fasahohi na al'umma ta birnin Beijing, ita ce wata makarantar sana'o'i daya kawai da aka kafa a nan birnin Beijing, domin horar da kwararrun fasaha ga kananan kabilu. A shekarar 2005, makarantar ta karbi yara 20 na kabilar Uygur, wadanda suka kwarre a fannin fasaha a shiyyar da ke fama da talauci ta birnin Hetian na jihar Xinjiang, kuma za ta ba su ilmi na kyauta, ana fata za su iya kara matsayin fasaharsu ta hanyar karatu a birnin Beijing.

Malam Xue Baoxiang, shugaban makarantar koyon sana'o'in al'adu da fasahohi na al'umma ta birnin Beijing, ya gabatar da cewa, ban da koyon ilmin al'adu kamar dalibai na sauran azuzuwa, kuma wadannan yara suna bukatar koyon ilmin musamman a fannonin rera waka, da rawa.

"Sabo da 'yan kabilar Uygue sun kwarre a fannin rera waka da rawa, don haka, muna fata za a zakulo fasahohin da wadannan yara ke da su. Yanzu muna mai da hankali kan horar da fasahohinsu, ta yadda za su iya samun aikin yi a birnin Beijing."

Malam Xue Baoxiang ya gaya wa wakilinmu cewa, wadannan yara sun yi zama a jihar Xinjiang har shekaru fiye da goma, yawancin su ba su taba fita da nisa ba, har ma wasu daga cikinsu ba su taba fita daga jihar Hetian ba. Sabo da haka ne yara da yawa ba su iya dacewa da zaman rayuwarsu a birnin Beijing, a lokacin da suka iso birnin ba da dadewa ba. Wasu yara sun yi tunani da iyalansu sosai, da jin haka, makarantar ta ba su kantunan taliho na kyauta, ta yadda suna iya buga waya ga iyalansu a ko wane lokaci. Sabo da 'yan kabilar Uygur suna son cin abincin taliya da na nama, don haka, wasu ba su saba da cin shinkafa da kayan lambu da makarantar ta shirya musu ba, sai makarantar ta kan shirya musu abincin musamman a lokacin hutu.

Shugaban makarantar Xue Baoxiang ya ce, domin taimakon wadannan yara wajen kara samun ilmi, makarantar ta kan tura su, don su halartar harkoki na bayan karatu.

"A lokacin bikin kasa, mun shirya wasu aikace-aikacen cikin rukuni a sansanin soja. Dalilai su ne, a fannin daya an bude idanunsu, da kara ilmominsu, a fanni daban sun mai da zaman rayuwar su a makarantar kamar a gidajensu."

Yang Bei, wata malama ce ta wannan ajin da wadannan yara 20 ke ciki. Ta ce, duk malaman makarantar suna kula da wadannan yara kamar yaransu. Yang Bei ta gaya wa wakilinmu cewa,

"Wata rana, wata yariniyar ajinmu ta kamu da ciwon tsiro mai tsanani a uwar hanji, amma iyalinta na fama da talauci, ba su da isashen kudi don biyan kudin tiyata. A lokacin da aka samu wannan labari, sai nan da nan makarantar ta biyan kudin asibiti. Shugaban makarantar da kuma malamai sun mai da hankali sosai kan wannan, kazalika ni da wasu malamai sun kula da yariniyar har zuwa lokacin da ta fita daga asibiti."

Yanzu, wadannan yara sun yi zama a nan birnin Beijing kusa da shekaru 2, haka kuma ko wanensu sun samu sakamako daban daban. Rustam ta gaya wa wakilinmu cewa,

"Na koyi abubuwa da yawa a fannin zaman rayuwata, yanzu na riga na iya zama da kaina, kuma na iya warware wasu matsalolin da nake gamuwa da su."

Alijan, shugaban ajin nan yana ganin cewa, ya samu ci gaba sosai a fasahar rawa:

"Kafin in zo birnin Beijing, ban taba yin rawa ba, yanzu na zabi fasahar rawa a makarantar, bayan kokarin da nake yi, na riga na zama kyafkin kos din rawa, malamanmu ma suna so na sosai."

Amma, abin da ya fi jawo sha'awarsu shi ne, halartar wasanni da gasar rera waka da rawa. Rustam ta gaya wa wakilinmu cewa, a lokacin da baki 'yan kasashen waje suka kawo ziyara a makarantar, kullum suna yin wasannin rera waka da rawa. Rustam ta ce, abin da ya kasa mantawa shi ne, a cikin wata gasar game da bikin fasaha na Beijing da aka shirya a watan da ya wuce, sun ci lambawan ta rawar kabilar Uygur da suka yi.

"A ko wace rana, mun yi gwaje-gwaje bayan aji, mun gaji sosai, amma a karshe dai mun zo lambawan na birnin Beijing. Sabo da haka, mun yi farin ciki sosai, har ma mun manta da wahalolin da muke sha."

Yanzu, wadannan yara 20 suna da fatansu, da kuma burin da suke yin kokari don tabbatar da su. Yaran sun ce,

"Ina fatan koyon ilmomi da yawa a nan birnin Beijing, bayan haka kuma zan koma garinmu, don raya garinmu."

"Iana son shiga jami'a a birnin Beijing, daga baya kuma, zan koma garinmu, kuma zan ba da ilmomin da na koyi ga sauran mutane."

"Bayan da na gama karatu a wata jami'a ta birnin Beijing, ina fata zan zama wani shahararren mawaki."