Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-10 15:32:20    
Nakasassu a kasar Sin

cri

Ban da wannan, ana kuma ta kyautata samar da guraban aikin yi ga nakasassu da kuma tabbatar da zaman rayuwarsu. Ban da neman guraban aikin yi da wasu nakasassu suka yi da kansu, nakasassu suna kuma iya aiki a wasu ma'aikatu na jin dadin al'umma da aka bude musamman domin nakasassu. Sa'an nan, bisa dokokin da abin ya shafa, wasu hukumomin gwamnati da kungiyoyin al'umma su ma suna daukar wasu nakasassu bisa ka'ida. Ya zuwa karshen shekarar 2007, yawan nakasassun da suka sami aikin yi a garurruwa ya riga ya kai miliyan 4 da dubu 337, a yayin da adadin ya kai miliyan 16 da dubu 966 a kauyuka. A shekarar 2007 kadai, yawan nakasassun da suka kama aikin yi a birane da garurruwa ya kai dubu 392.

Amma daga cikin nakasassu sama da miliyan 80 na kasar Sin, nakasassu fiye da miliyan 43 ne kawai ke iya aiki, duk da haka, wadanda ba su da aikin yi ana tabbatar musu zaman rayuwa. Domin kara tabbatar da zaman rayuwarsu, sassan kula da harkokin jama'a na kasar Sin sun gudanar da harkoki da dama na jin dadin nakasassu da ba su taimako. Misali, an kafa wasu hukumomi a birane da kauyuka, domin ciyar da wadanda ba su iya aiki da kuma tsofaffi da nakasassu da kuma yara wadanda ba su da kudin zaman rayuwa.

Domin kayatar da zaman rayuwar nakasassu, ana kuma gudanar da harkokin al'adu da wasanni masu ban sha'awa a tsakanin nakasassu. Tun daga shekarar 2001 har zuwa ta 2005, gaba daya ne aka samar wa nakasassu filaye 1036, don su gudanar da harkokin al'adu, sa'an nan, an kuma samar da dakuna 244 na sauraron bayanai ga makafi da kuma filayen wasa 1026 ga nakasassu. Yanzu nakasassu na kokarin shiga harkokin al'adu da wasannin motsa jiki iri iri. A watan Oktoba na shekarar 2007, Sin ta gudanar da wasannin Olympic na musamman na duniya a karo na 12 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar. (Lubabatu)


1 2 3