Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-10 15:32:20    
Nakasassu a kasar Sin

cri

Tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, musamman ma bayan da aka yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje, harkokin nakasassu sun sami cigaba kwarai da gaske a nan kasar. Domin bunkasa harkokin nakasassu da kyautata zaman rayuwarsu, gwamnatin kasar Sin ta dauki manyan matakai a jere.

Sau biyu ne Sin ta gudanar da bincike a kan nakasassu na kasar Sin, kuma ta kaddamar da dokokin ba da tabbaci ga nakasassu da ka'idoji kan ilmantar da nakasassu da kuma ka'idoji kan samar da guraban aikin yi ga nakasassu da dai sauransu. Bayan haka, ta aiwatar da shirye-shirye biyar game da bunkasa harkokin nakasassu da kuma tsara manufofi da matakai da ke shafar fannoni daban daban na zaman rayuwarsu.

Tun daga shekarar 1988 har zuwa ta 2007, makafi kusan miliyan 6 sun warke bisa tiyatar da aka yi musu. Sa'an nan, bisa jiyyar da aka yi musu, nakasassu fiye da miliyan 5, ciki har da masu nakasa a kwakwalwa da kurame da masu nakasa a hannaye da kafafuwa, sun sami sauki.

Bayan haka, an kuma karfafa ilmantar da nakasassu daga fannonin kafa doka da tsara manufofi da kuma zuba kudaden jari. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2007, daga cikin nakasassu na kasar Sin, akwai dubu 940 da suka sami digiri na farko, a yayin da miliyan 4 da dubu 60 suka kammala karatu a makarantar sakandare ta mataki na biyu da kuma miliyan 12 da dubu 480 suka kammala karatu a makarantar sakandare ta mataki na farko. Bayan haka, akwai kuma miliyan 26 da dubu 420 da suka kammala karatun makarantar firamare. A shekarar da muke ciki, Sin za ta zuba kudin Sin da yawansa ya kai miliyan 600 wajen kafa makarantu 190 na musamman domin nakasassu.


1 2 3