Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 11:38:26    
(Sabunta) An shirya sosai wajen harba kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati kirar Shenzhou-7, in ji cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan

cri

Yayin da darektan cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan, wanda kuma shi ne babban mai bada umurni a filin harba tauraron dan Adam, Cui Jijun ke zantawa da manema labaru daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua yau 24 ga wata, ya bayyana cewar, cibiyarsa ta shirya sosai daga dukkan fannoni domin harba kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati kirar Shenzhou-7 zuwa sararin samaniya.

Cui Jijun ya ce, sassa daban-daban na kumbon suna aiki yadda ya kamata, kuma an riga an kammala aikin karawa kumbo da roka sinadarin da zai kara musu sauri.

Cui ya kuma bayyana cewar, domin bada cikakken tabbaci ga harba wannan kumbo cikin nasara da tsaron 'yan sama-jannati, cibiyar harba tauraron dan Adam ta mayar da hankali sosai kan gyarawa da sabunta na'urori daban-daban dake shafar kayayyakin 'yan sama-jannati da tsaronsu a filin harba tauraron dan Adam. A waje daya kuma, an horas da mutane masu aikin fasaha a wannan cibiya, don haka dukkan mutane masu fasaha sun sami kyakkyawar horaswa.

Bayan haka kuma, jami'an ofishin jagoranci kan ayyukan harba kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati kirar Shenzhou-7, da kwamitin zaben 'yan sama-jannati sun gabatar da 'yan sama-jannati 3 da za su sauke nauyin tafiyar samaniya game da kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati kirar Shenzhou-7, wato su ne Zhai Zhigang, Liu Boming, Jing Haipeng. (Bilkisu)